Sashe 54
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ciccibar Buba isa yayi zuwa mota, Alhj da kanshi ya buÉ—e mishi baya ya sanya shi, matan suna tsatsaye hannu a ka duk a zaton su É—aure shi Alhj ze je yayi, Alhj Usman yace
"Isa ba zamu tafi da mace ko É—aya cikin matan ba?"
Isa na nufan su suka runtuma da gudu suka koma cikin gida harda rige rige na karshe na banko kofa, dariya ya saka yace
"wawayyu! Babu rabon cin arziki"
Yana kai nan ya buÉ—ewa Alhj gaban motan ya shiga, shima ya zagaye ya shiga driver seat ya tayar da bismillah suka Lula, ba tare da ko gargadar hanyar suna ji ba sbd lafiyar motar da tsadar ta.
Shi dae Alhj in ka bincika ko gani me kyau ba yayi sbd damuwa, Ina matarshi? Ina abunda ke cikinta? Suna raye? Sun mutu Allah kaÉ—ai ya sani... Ko da abunda ze mallaka ze kare a duniya ba ze huta ba har se ya samo Aisha da abunda ke cikinta....
Hawayen idanunshi ya É—auke cikin zafi da kunar zuciya.
****
"Hhhh zaka iya ne?"
Tayi maganan cikin kasa sossai da murya tana murmushi yace cikin wara idanu.
"Kina mamaki ne? Ai kece ciki ni ina na san wani kunya...! In kuma kina ganin ba zan iya ba Allah ya kaimu in sauka a Nigeria babe zaki yi bayani..!"
Dariya take yi tana rufe bakinta sbd Daadida dake zaune a parlorn.
Duk yadda ya so ta gayamishi wani magana me daaɗi ƙiyawa tayi wai Daadida na zaune kuma bazata iya tashi ta tafi ɗaki rike da waya ba, kwafa yayi yace
"kin ci bashi am promising you! Ina my boy?"
Tace chan ƙasa
"gashi chan ya hana Daadida shan iska cikin lumana"
"please put him on the phone I missed him"
Baki ta tura tace
"mu da bamu da me missing namu ai bamu mutu ba...! Junior! Junior!!"
Murmushi kawai Raed yayi yana lumshe idanu, yana jin sabon drama da suka fara don junior ko ya juyo ya kalleta ma bare ya san tana kiranshi.
"Ka ga min yaro! Toh Daddynka ne ke son Magana da kai in kuma shima bazaka juyo ba se in j....."
Shiru tayi ganin shi a gabanta yana kiran
"Daddy?" Yana zazzare idanu.
Rankwashi marar zafi ta mishi kan ta saka mishi wayan a kunne ta koma ta kwanta tana murmushi, rayuwa ne ya kawo ta wannan matsayi, ashe akwai farin ciki irin haka a cikin wannan rayuwa bata taɓa sani ba se yanzu? Idan taga inda take rayuwa da yadda take rayuwa da yanayin yadda fatan jikinta da komai nata ya zama na rich pikins se tayi murmushi tace Alhamdulillah.
"Daddy pls come back I missed you! No one is playing with me here.. And this old Granny is always mocking me"
Ya karashe yana tura baki yana kallon Daadida.
Dakuwa ta mishi tace
"ungu nan kai da turancin naka na tsiya, na san sarai magana ta kayi shiyasa kake min wannan kallon to kai da uban naka duk kun yi kaÉ—an"
Dariya hidayat ke tayi ita kaÉ—ai idan taga yadda Raed junior ya maida fuska ga Daadida na ta masifa kuma babu me jin yaren juna se ta kara saka dariya, Ta tabbatar rarrashin shi daddyn shi ke yi har ya sake fuska yana cewa
"Many balls yeayyyyy"
Taɓe baki tayi be wuce tsaraba ya tambaya ba yace balls yaro da ball wannan ai ko uban dake ɗan kwallo se ya shafa mishi lafiya.
Su Aisha ne suka shigo cikin shigan Atampha da ya musu kyau Dukda dogayen riguna ne amma kana ganin Su Norah zaka san sun takuru sossai haka dae suke lallaɓawa don Daadida tace shigan Turai ba'a gidanta ba.
Sallaman me gadinta ne ya katse musu dariyar jan Da su Norah ke yiwa Daadida tana ta masifa.
"Hajiya baƙo kika yi kuma yace lallai lallai yana son ganawa dake don Allah daga chan Gembu yake"
Tace
"Ah malam mudi shigo dashi parlorn baƙi na gani nan zuwa yanzu"
Mikewa tayi ta Sabi gyale ta rataya tace
"Ke Nuriyya ki cewa Tabawa ta kawo abun taɓa wa parlorn baƙi na"
Baki Norah ta tura don ta tsani wani Nuriyya da Daadida ke kiranta ta wuce kitchen, chan ta dawo bayan Daadida ta fita tacewa Hidayat dake danna wayanta suna chatting da Rashida akan sauran É—inkunan da ta bayar.
"Mom, Tabawa fa Daadida ta aike ta kuma ta sake aika na wurinta again"
Hidayat tace
"maybe ta manta ne, bari na Haɗa na kai, ba abun na aike ki ba kila baƙin kunya ne ki baiwa er tsohuwa kunya"
Ta miƙe ta shige kitchen Norah ta bita tana cewa zata iya Allah ai taga yadda suke yi a Nijeriya, hidayat bata ce komai ba ta Haɗa ruwa da snacks a tray ta dauka ta fito ta ajiye bisa dining kan ta shige ɗaki ta ɗauko hijab ɗinta ta fito.
Tunda ta doshi parlorn gabanta ke wani irin faÉ—uwa haka dae ta daure ta karasa sede jin tashin sautin kukan Daadida ya sanya ta saka kai cikin parlorn a rikice, daga bakin kofa ta ajiye ruwan ta karasa hankalinta na kan Daadida dake kuka sossai ta rungumeta tana cewa
"Subhanallah! Daadida menene? Me ya same ki haka? Yanzu fa lafiyanki ƙalau wani ne ya rasu?"
Ba tare da ta jira amsar Daadida ba ta ɗago don ganin wadda yake parlorn, saura kaɗan ta kife ƙasa saboda Rikicewa da bugawar zuciya shima a take ya mike tsaye yana kallonta hannunshi na rawa ya nuna ta.
Daadida dake kuka se ta nemi kuka ta rasa ta tsaya tana Kallonsu yadda duk suke kallon juna da wani yanayi me wuyar fassaruwa.
"Alhj Usman! Ka Santa ne? Hidayat!"
Ta kirata tana jijjiga ta da sauri ta dawo daidai sede jikinta na wani rawa da ta rasa dalili, shi kam be ce komai ba se matsowa da yake yi gangan ta idanunshi a fuskanta yace
"Mama ba ga AISHA ba!"
Daadida tace
"wannan ai sunanta Hidayat Usman, rabona da Aisha tun korar kare da Buba yayi mata! A lokacin bani da yadda zan yi dashi....wallahi wallahi a kullum se nayi kuka cikin dana sanin Barin Aisha ta tafi da tsohon ciki cikin halin rashin cikakken hankali gashi bata kara waiwayonmu ba, nayi nema har na gaji!"
Ta karashe cikin kuka.
"Mama a jikina nake jin ina da alaqa da wannan yarinyar! Mama ina iyayenta?"
Ya faÉ—a hawaye masu zafi na gangaro mishi, duk da natsuwar shi da cikar kamalarshi sossai rauni da damuwarshi suka bayyana.
"Bani dasu!"
Hidayat ta bashi amsa itama tana zubar da hawaye.
"Mahaifiyata ce kaÉ—ai itama ta ra....su bayan ta hai...feni"
Kuka ne ya ci karfinta.
Aisha da ta shigo da gudu riƙe da waya tace
"Mom Dad ya kira he wants to talk to you..!"
Turus tayi kan tayi kan hidayat tace
"Mommy! Why are you crying?"
Riƙeta hidayat tayi tana share hawayenta, a take hankalin Raed dake kan wayan ya tashi yana ta magana sede tuni Aisha ta ajiye wayan bisa stool dake gefen kujeran.
"Mama karfin jini ya wuce wasa, ina jin karfin jinin dake tsakanina da yarinyar nan ko ma ita wacece.... In baki da iyaye ina danginki?"
Se a lokacin Daadida ta sharce majina tace
"wallahi ni karan kaina tun daga kallon farko nake jin ta a raina tamkar yadda nake Jin Raed na É—auka ko don ta taimakawa rayuwar Raed ne, na É—auka don ta zama silar cikar babban Burin raina ne...amma yanzu da kayi magana na fara jin sabon al'amari tattare da ita tabbas tana É—iban yanayi da AISHA"
Mikewa hidayat tayi ta dube su tace
"Wacece Aisha? Ku fahimtar dani Don Allah?"
Kamata Daadida tayi ta zaunar ta dubi Aisha dake kuka tace
"yi shiru ba wani abu bane ya samu uwar taku iyayen son uwa! Ki je kuyi wasa kinji? Zata zo yanzu"
Kallon hidayat tayi se ta gyaÉ—a mata kai nan ta juya ta fice ta ma manta da wayan dake kunne Raed kuma na kan layi hankalinshi a tashe, Hidayat fa ke zub da hawaye da aurenshi a kanta bayan alkawarin da yayi bayan kukan farin ciki har abada ta gama kukan wani damuwa, ji yake kaman yayi tsuntsu ya baro Riyadh kaman shima ze yi kukan yake sauraron su zuciyarshi na zafi yana jin haushin wadda ya sakata wannan kuka.
"Aisha ƴata ce hidayat ita take bin buba su biyu kaɗai Allah ya mallakamin a duniya, ina matukar ƙaunar Aisha saboda saɓanin Buba Aisha yarinya ce me tsantsar haƙuri, shiga rai da iya lafazi, tana da sanyin hali wadda a kullum nake mata Adu'ar kar ayi anfani dashi wurin cutatar da ita, ta taso ne da matsin wanta buba idan har ba Mahaifinsu na nan ba ko motsin kirki bata isa tayi ba don ko ni ba bari Buba yayi ba.
Aisha sun haÉ—u da Usman ne a lokacin ya je kauyen mu akan hannun Jarin da ya zuba mafi rinjaye a wani kamfanin lipton, tun daga sannan Usman be yi kasa a gwiwa ba ya samu mahaifinsu saboda sanin addininshi da natsuwa irin tashi be sameta da maganan ba seda ya samu Mahaifinsu, shi ya bashi lokaci kuma Seda Mahaifinsu yaje har Kano yayi bincike akan asalin Alhj Usman sbd matashi ne a lokacin me ji da kuÉ—i, kin san kuma yadda kuÉ—i yake abun tsoro, sede Alhamdulillah ashe Sanannen É—an kasuwa ne da yayi shura a lokacin ma, kuma samun shi da duk wani nagarta da ake so ne yasa ya bashi izinin neman auren Aisha.
An yi sa'a sun fahimci juna tana matukar sonshi se kuma buba yace shi be amince ba, an kai ruwa rana har yana cewa in ta aureshi shi babu ruwanshi da ita har duniya ta nade, Mahaifinsu yace tunda ba shi ya haifeta ba in ya ga dama hanyar Da Aisha ta bi kar ya kara bi, kaman wasa ko gaisuwarta baya amsawa bare na Usman yayiwa Usman cin kashi iri iri sede Usman dan uwan Aisha ne a hakuri Dukda yana da karfin ikon hukunta buba amma be taɓa ɗaga kai ya kalleshi ba.