Sashe 1
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KOWA YA GA ZABUWA...
  (DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.      Â
     (Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
           *PAGE 1*
*FREE BOOK*
Duƙe take a gaban murhun tana hura shi da iskar bakinta, daga idanunta har zuwa hancin ta da suka yi jajazir kasancewar ta fara tas zubar ruwa suke na hayaƙin da ya turnuke sararin wurin sbd kasancewar iccen ɗanya, hannunta da yayi baƙi sandiyar hura wutan ta sanya ta kamo ɗan kwalin kanta irin me yauki na da ɗin nan ta sa ta share hawayen idanunta kan ta mike a hankali tana gyara zanin da yake tsab tsab saboda tsananin tsabtarta sede a koɗe yake yayi fari fat..
Katon cikin dake jikinta na fallasa kanshi, a hankali take tafiya zuwa bakin rariyar su ta duka ta ɗauki buta tare da fyace hancin ta sossai, Seda ta wanke hannunta dake baƙi sbd hura itace kan ta wanke hancinta zuwa fuskanta ta sa sabulu guntu da ta tsinta wurin wanke wanken ta wanke hannayenta da kyau kan ta sake wanke fuskanta..
Wata yarinya dake gefen ta da suke matukar kama da bata wuce shekara 6 bane ta ce
"Mama wutan ya ki kamawa ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana kara kikkimta mawankin tace
"Aisha ya zan yi, ya ki kamawa tsabar fifita kin ga yadda hannuna ya zama"
Yarinyar ta matso tana É—aukan maficin ta cigaba da fifitawa tace
"mama ko in koma in sami baba me faskare ya tsanmmana rairayi da sauran faskare mu zo mu sa, yunwa nake ji kinga yaya manu ma dake rashin lafiya tun safe be ci komai ba"
Lumshe idanunta tayi da suke kyawawa har mamakin ganinta a irin wannan yanayi na rayuwa Ya rufe ni,(sede ba'a mamaki da ikon me duka) a hankali cikin muryarta dake fallasa rashin son Magana da hayaniyar ta ta ce
"Aisha baze gaji damu bane? Kullum muna kan yawo wurin shi neman faskare bayan ba saya muke ba?"
Dakuna fuska yarinyar tayi hawaye na zubo mata.
Matsowa matar tayi ta zauna a kujeran tsuguno dake wurin tare da karɓan maficin ta ce
"kar kiyi kuka bari na cigaba da fifitawa samu ruwan ya tafasa in dama kunun ki sha, kiyi hakuri"
Dukda ita karan kanta ba wani karfi ne da ita ba tsabar yunwa tun jiya da rana da ta sha kunun da ya zame musu jiki na garin masara da tsamiya bata kara saka wani abun a bakinta ba bayan ruwa har yanzu da ake neman karfe sha É—aya na rana ban da Juyawa babu abinda yaron cikinta ke yi cigaba da fifita wutan tayi da kyar ta samu ruwan ya tafasa dama tun tuni Aishan ta dama musu garin masaran da ruwan tsamiya sbd rashin abun sarrafa shi kawai ta juye a ciki tana Juyawa har ya nuna.
Saukewa tayi Aisha ta je ɗan karamin kitchen ɗinsu dake zagaye da zink da yayi baƙi kirin ta ɗauko wasu kofuna marasa hannun arziki ta kawo guda uku, ba tare da sugar ba sbd basu dashi basu da dalili ta zuzzuba, ta Mikawa Aisha nata ta rufe nata a gefe tare da ɗaukan Ɗayan ta karasa kan yaloluwar taburma dake shimfiɗe cikin varender ɗin sun da rabi a fashe rabi da siminti, farin yaron da kammaninsu yake sak kaman Aisha da shima ba ze wuce 10yrs ba ta ɗago ta taimaka mishi ya zauna, jikinshi banda tururin zafi babu abinda yake fitarwa.
Cikin yanayin muryanta ta ce
"Usmanu tashi ka sa wani abu a cikinka ka ji? Sannu.. Daure babana"
Da kyar ya iya yin kurɓi biyu se amai, ya fara kelawa ruwa banza sanadiyar rashin komai a cikin nashi daga karshe ma banda kakari babu abunda yake yi, hawaye masu zafi ne suka kwararo mata, banda fatan Allah ya jefo mata Yusuf babu abunda take yi a ranta, zata tambaye shi zata roke shi ya taimaka kar yaron su ya rasa ranshi kwance a gida ko da ze zage ta har zagin ya Mannu a jikin ta ne bata damu ba.
Allah ya amsa mata Adu'ar ta kuwa sbd banko kofar kyauren da aka yi tare da kamshi irin na turarukan da Yusuf É—in ke anfani dasu da ya bule gidan ne ya shaida mata da shi É—inne ya shigo, kwantar da Usman tayi tare da zubawa Aisha da ta taso da gudu ta dawo bayanta ta makale idanu, shi karan kanshi Usman É—in dake kwance rawan jikin shi ya karu, zuwan Abbansu ba alkhairi bane gare su har ma ga mahaifiyarsu wani irin tsoro suke mishi da na tabbatar ko mala'ikan É—aukan rai ne suka ji motsin shi se haka.
Tsab fuskar shi ya bayyana fari sol tsiririn bafulatani Sam bashi da ƙiba sede yana da kyau iya kyau kaman shi ya halicci kan shi, takowa yake yana kwaɓe fuska kaman wadda ke bin cikin kashi Dukda tsakar gidan banda shatin tsintsiya na shara ko tsinke babu, komai a kimtse yake a gyare cike da tsabta irin ta matar gidan, har ya karaso varender da suke ya ɗago ya watsa musu wata muguwar harara cike da neman magana.
Babu wadda ya iya É—aga ido ya kalle shi a cikin su se yaran ne baki na rawa suka ce
"san...sannu da zuwa Abba"
Tsaki me karfi ya ja yace
"kuma sannun in da daaÉ—i... Ke Hidayat ke kin fi karfin marabtata ko in na dawo cikin gidan nan? Zaki gayamin zaman uban da kike in ba nawa ba da har zan shigo cikin gidan nan ki kasa É—aga ido ki mini sannu da dawowa, To wallahi ubanki zan ci in baki kiyaye ni ba, wannan iskancin bazan É—auka ba wallahi..."
Sababi ya ci gaba da yi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, kaman wacce ta aikata wani babban laifi, kanta na ƙasa bata ɗago ba, ba se rashin bashi haƙurin ya kara ɓular da shi ba ya shiga zagin ta zagin cin mutunci ba ita kaɗai ba har da iyayenta da zuri'arta gabaɗaya, bayan ya gama wanke ta son ranshi ya karasa wani kyakyawar kofa dake daga gefe gini ne na zamani da fentin shi Milk da pink ba kaman wadda suke zaune a gabanshi ba me single room da varender banda plaster ko arzikin penti be samu ba..
Key ya sa ya buÉ—e tsararriyar kofar ya tusa kanshi cikin parlorn, tare da kunna wuta nan haske tar ya bayyana haÉ—uwar parlorn me É—auke da milk and gold royal set na kujeru da dining tsararre a gefe kayan kallo da home theaters se fridge da labulaye ruwan gold me adon milk har Ac akwai a parlorn, cikin É—aya daga cikin kujerun ya je ya zauna yana fiddo Wayanshi kirar iPhone 12 ya fara operating cikin kwarewa kan ya sa a kunnen shi ya fara magana daidai lokacin da ta turo kofan a hankali tare da sassanyiyar sallama nan daga bakin kofan parlorn ta duke don nan É—inne kawai take da izinin takawa a muhallin nashi idan ba shara da goge goge bane ya shigo da ita.
Wayanshi ya cigaba da yi cikin narkakkiyar murya yana zuba kalamai kaman ba shine ya gama tijaresu ba yanzu a tsakar gida, Seda ya shafe a kalla kusan awa kan ya kashe wayan nan ma be kula ta ba ya É—auki remote ya kara muryar TV abin shi.
Kafafunta da suka fara tsami sbd tsuguno ne yasa a hankali ta ce
"Hamma Yusuf wurinka na zo, Dan Allah ka aramin mintuna biyu cikin lokacin ka magana nake so mu yi"
Seda ya bushi iska kan ya ce yana kuma haÉ—e gabas da yamma
"se yanzu kike da bakin magana da ni alhali kin min laifi ina faÉ—a a gaban waennan tsinannun yaran naki masu busashun ido irin ki baki iya bani hakuri ba?"
Lumshe idanunta da zuwa yanzu ta tabbatar baza'a samu hawaye ciki ba sbd kila sun kare tayi, 'Yarana zasu yi albarka in shaa Allah' ta faÉ—a a ranta a fili kuwa ta furta a hankali.
"Dan darajar Allah kayi hakuri, na san nayi kuskure kayi hakuri"
Ta riga ta saba ko da bata da laifi dolen ta ne ta bashi hakuri a duk sadda ze zage ta ko ya ci mutuncinta.
Share ta yayi, ta tattaro duk wani dauriyanta ta haÉ—iye miyau da da kyar take iya haÉ—e su a bakinta sbd azabar yunwa da ciwo da take fama dashi tana daurewa ta ce
"hamma..! Usman bashi da lafiya yau kwana biyu kenan kullum gaba gaba jikin yake yi, dan Allah ka taimaka ko chemist ne a kaishi yana jin jiki... Sannan bamu da ko kwayar hatsi a gidan nan garin masara kalilan da ta saura da shi na mana kunu da rana"
Wani mugun kallo ya watsa mata, tare da jan tsuki ya ce
"ai dama ta inda kuka fi kauri kenan kuɗi da abinci ba, ba kince kin ji kin gani daga an taɓaki se ciki a ce ki zubar bazaki zubar ba ba? Toh wallahi ba ruwana da ciwon yaron ki hakanan ba ruwana da cin su ko shan su, ke ɗin da kika zama dole na auna miki masarar da na san a cimar cikin ki ze miki wata guda churrr yanzu tsakiyar wata ki wani zo da baki kaman shadda ki ce min abinci ya kare? Toh wallahi bazan iya ba bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa, kin tashi kin ɓace min da gani ne ko se na take ki hanjin cikinki da wannan abunda kika kuntson sun yo waje? Gantalalliya uwar fi'ili"