Sashe 67
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama a nata bangaren godiya me tarin yawa take Mikawa Mahaliccinta da ya bata Raed a matsayin miji, tana mikewa beddings ta fara chanzawa sbd yadda wanchan ya chukwuikuye baze gyaru ya kwanta ba, a washing machine ta sanya ta dawo ta ɗan kikkimtsa ɗakin, dama tayi wanka kan tayi alwala se ta sanya doguwar riga bubu da hijab tayi sallah, hijab ɗin ta mayar ta fito sbd sanin cewa namiji ne cook ɗinsa, ga mamakin ta babu kowa a ƙasan.
Kitchen ta shiga yana nan neat ba kowa, sauri sauri ta fara HaÉ—a masa breakfast liver sauce ne da dafaffen Irish tana cikin kwashewa a warmers taji an sanya hannu an rungumeta ta baya, dukkansu suka sauke numfashi a tare....
#Vote
#share
#comment
        🖤Gureenjoh🖤
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763
AND ON AREWA BOOKS @gureenjo
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*PAGE 44*
*FREE BOOK*
"Good morning..!"
Yayi whispering yana zare mata hijab É—in na jikinta, murmushi ta saki me taushi tace
"Good morning, hope an tashi lafiya?"
Ƙara shigar da ita jikinshi yayi yace
"in akwai abunda yafi lafiya ma yau na tashi dashi baby gurl, sannu da aiki"
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"sannu! Ammm se Naga kaman akwai namiji dake shigowa nan ko? Shiyasa na saka hijab"
Yace
"Nah! Daga nan har Paris babu namijin dake da hurumin shiga min parlor bare kitchen baby gurl, that was before"
Bata sake cewa komai ba ta ajiye kular da ta gama kwashe dafaffen Irish ɗin, se ta tsaya cikin kunyar ce mishi ya saketa ta gama Haɗa breakfast ɗin, Sam duka wannan bambarakwai take jin su wai namiji da suna Hajara, leƙa fuskanta yake yi daga wuyan ta yace
"wait! Baby gurl are you avoiding my eyes?"
Ya karashe da sautin smile, bata ce komai ba
Yace
"please don't! Kin fa riga kin zama rakumi ni kuma akalarki duk inda zaki je yanzu a tare dani zaki, so feel free around me we are already one and I love you ok?"
Duk yadda ta so sunnewa haka ta hakura kaman yadda ya faÉ—a kuwa duk inda tayi tare suke yi, breakfast É—in ma kusan plate É—aya suka yi da tea cup guda, bayan sun gama suka sake kwanciya bacci ba su suka farka ba se wuraren azahar.
Kitchen ta sake shiga bayan tayi wanka tayi sallah tayi pasta half wadda yaji vegetables, bata sa a kula ba sbd shima ya sauko yana tare da ita so a plate suka juye shi ya wuce dashi cikin parlor yayinda ita ta ɗibi drinks da cup, a tsakar parlorn suka zauna suka ci abincin cikin nishadi, bata taɓa Tunanin haka aure yake ba.
Bayan sun gama yace su je su shirya su tafi asibiti, cikin doguwar rigar Abaya ta fito maroon wadda yayi mugun amsar ta, ta rufe kanta da gyalen, wayanta kawai ta É—auka ta fito a parlor ta same shi suka fita a tare hannunshi cikin nata.
Ko a motan ma hiran su suke yi na masoya fuskokinsu cike da nishadi wadda ze tabbatar maka hankalinsu a mugun kwance yake, a haka suka shiga asibitin riƙe da hannun juna, kunya ne ya rufe ta a sadda suka tarar da iyayenta a ɗakin da duka yaran tare da Daadida.
Daadida ta kasa shiru tace
"Aaa lallai se yanzu ake ganinku?"
Basu amsa ba se murmushi, ya gaida Abba, sannan Maami duk cikin jin daaÉ—in ganin da suka musu suka amsa, suma daga ka gansu ka san ma'aurata ne masu cikakken natsuwa da kwanciyar hankali, ita dae hidayat na ta fama da Junior dake tambayar ta ina taje ta barshi.
Baba Buba kallon su kawai yake yana hawaye tare da murmushin karfin hali, rayuwa fa kenan, lallai mahakurci mawadaci dubi yadda duk suke cike da walwala shi kuma gashi kwance yana girban abinda ya shuka.
Duk waje suka fita inda suka shimfiÉ—a carpet aka zazzauna ana hirarraki kaman dae yadda kuka san asibiti, anan ne ma Daadida ta kawo maganan ko za'a É—auko matanshi duk babu me kira cikinsu yaji halin da yake ciki, a lokacin da yake bukatar su a sannan suka yi watsi dashi, su da baya so a sadda yake da mamora sune ke taimakon shi a yanzu.
Abba yace a kyale su da sun damu ai da sun zo, shi dae Raed ya fita wani taro da aka gayyace shi, planning tafiya Saudia da baba Buba kawai yake, ko ba komai in ya É—an samu karfi su shiga yayi aikin hajj don ya ragewa kanshi zunubi.
Tunda hamza ya bar gidan ɗauke da hajiyarshi kai tsaye gidan mahaifinta ya nufa, a hanya ya kikkira yayyunta da en uwa na kusa akan su haɗu a gida akwai matsala, bayan an zazzauna a ɗakin taro aka buɗe da Adu'a hamza be ɓoye musu komai ba cikin duk abubuwan da suka faru sbd labarinta izina ne ga en baya masu irin halin ta, ina mijin? Ina dukiyar? Ina lafiyan? Duk ta salwantar da hannunta ba na wani ba.
Daga karshe ya rufe da
"ba na baku labarin bane saboda in tona mata asiri, na faÉ—a muku ne saboda ya zama dole ku sani kar ku ga kaman Abbana butulci yayi nata a sadda shi ya samu lafiya, zan gyara mata É—akin inna (mahaifiyarta) zan samu me kula da ita su zauna tare, ku yi mata fatan samun lafiya da fatan shiriya saboda babu wadda ya fi karfin wannan jarrabawar"
Kwarai sun jinjinawa karfin zuciyar hamza, yayi kokari sossai wurin ganin ya hana kanshi tsanar mahaifiyar shi, dukda ya san ta riga ta ɓata mai rayuwa da na zuri'a, kaman yadda ya roka Dukda yadda hajiya balaraba take da nuna isa da son a san ita fa wata ce, haka dae a gaban hamza suka yi mata Adu'ar shiriya da samun lafiya sede babu wadda ya kara da ko Naira biyar bayan nan.
ÆŠakin mahaifiyarta da single room ne sbd gidan ba masu karfi bane sede rufin asiri ya shigar da ita, be san a yau É—in wa ze kwana da ita ba haka ya zauna ya zabga tagumi yana kallonta, daga karshe kuka sossai yayi a haka suka kwana É—akin ko ta fara bacci zata tashi a firgice tayi ta ihu cikin dare.
Haka ze tashi shima ko yayi mata karatun Qur'ani ko yayi mata Adu'a, da asuba kaninta dake gidan ko gaisuwar hamzan be amsa ba sbd kaman yadda basu yi bacci ba haka shima da iyalan shi dake gidan.
Se rufe ta a É—aki yayi da safe ya fita, a sannan suka yi waya da Maami da wayan Abba take tambayarshi ko ze shigo ya karya?
Yace ba ze samu shigowa ba ze yi a wurin zainab.
Hakan kuwa aka yi gidansu yaje ba laifi zainab ta tausaya mishi tunda taji labarin wurin mahaifinta, ita ta bashi breakfast kuma ganinsu ya sa ya É—an samu karfin gwiwa, ta mishi alkawarin neman me aikin da zata iya kula da hajiyar.
Daga nan wanka yaje yayi ya É—an runtsa, kan azahar ya tashi ya sayi abinci a restaurant ya koma gidan se ya samu ma zainab taje da girki ta taimakawa hajiyan tayi wanka ta bata abincin tana ci, sossai yaji daaÉ—i a ranshi wani damuwan ya sake raguwa, a nan suka zauna har me aikin da ta kira ta zo, taimakon Allah hajiyan bata duka sede ihu da firgici se surutai marasa kan gado.
**
"Isa ka gane kwatancen kuwa?"
Yace
"ai Alhj sede idan ba cikin birnin Kano yake ba, na gane tsab yanzu zamu isa"
Kai kawai Abba ya gyaÉ—a kan ya maida hankalinshi kan maganan da suke da Maami a bayan motan, Farrah ce zaune daga gaba.
Daga motan isa se na Daadida ita da Norah ne da Aisha se driver É—inta, daga karshe kuma Raed ne da kanshi yake driving zaune daga gefenshi hidayat ce, daga baya junior.
Kallonta yayi yadda tayi shiru ta kurawa hanya idanu, hannunta dake kan cinyarta ya sa hannu ya riƙe tare da matsewa, ta kalleshi ta ɗan yi murmushi yace
"please die hard ki daina sawa kanki damuwa akan waennan mutane da basu cancanci damuwarki ba, promise me bazaki yi kuka don tuna wani abu da suka miki a baya ba, yanzu rayuwarki is a better life abunda ko a mafarkinsu basu taɓa hange ba"
Idanunta da suka sauya ta mayar ƙasa tace
"paapi sun yi min illa a rayuwa, sun yi min sanadin mutane biyu masu muhimmanci a rayuwata! Komai aka yi musu ko menene hukuncin su bana ji zan ji sassauci a raina idan har na tuna, sede Alhamdulillah idan na kalli irin rayuwar da Allah ya sauya min se in jinjinawa karfin hukuncin ubangiji dake fitar da rayayye cikin matacce ya kuma fitar da matacce cikin rayayye.."
Kiran wayanta ya hana shi magana ta É—aga tana tambayar ta iso daidai wurin? Ummi ta amsa da eh, basu kara tafiyar mintuna uku ba suka hangeta suka tsaya suka É—auke ta.
A mutunce suka gaisa da Raed, kan suka gaisa da Hidayat.. Aiko ummi tace
"Hidayat saura mu je ki zubar da hawaye a idanun waennan kaskantattun mutanen har su ga damarki ni da ke ne..!"
Murmushi kawai Raed yayi yana kallon hidayat da ta juya take harararta, Daga yanayin kalar unguwar da suka fara shigowa ummi da Hidayat suka buÉ—e baki suna kallon ikon Allah, wai anan umma da su Yusuf ke rayuwa?
Tunaninsu be gama kuncewa ba seda suka yi parking aka ce mota ba ze yi gaba ba sede a shiga a fiddo su.
Raed fuskanshi kawai ka gani se ka yi dariya, be taɓa shiga irin wurin a duniyan nan ba, kudaje da kwatami sune flowers da furannin unguwan.