← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 74

Sashe 60

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Daadida tayi cikin nazari kan tace
"ke basu adireshi kawai in ma kidmashin(kidnapping) ne su zo, ni yanzu duk buruka na sun cika banda son da nake in ji me ya samu Aisha me kuma ya faru har Usman ya dau tsawon lokaci be neme ta ba da ko yanzu ma a shirye nake da mutuwa!"

Me Rashida da ummi zasu yi In ba dariya ba, hidayat tace
"kina fa da matsala, daga son ganinki se ki kawo mutuwa da kidnapping? Yanzu dae in basu address ko?"

Tace
"eh basu, amma ki basu na babanki don gobe gidanshi zan yini in ma sun zo su same ni a chan ina jin labarin Aishatu!"

Hidayat tace
"Yanzu Daadida gidan Abba da gaske zaki yini gobe? Ya fa ce ze zo da kanshi goben har gida...!"

Tace ita kam faufau sede fa hidayat ta bada address É—inshi, tace itama bata sani ba se Daadida tace to shikenan su hakura masu son ganintan, su kuma jin shiru yasa suka cigaba da danna kira har Seda hidayat ta kira ya hamza ya bata address É—in gidansu kan ta tura musu a message bata kara bi ta kansu ba.

Rashida da driver ya zo É—auka suka tafi a tare da ummi don su sauke ta, yayinda hidayat da Daadida da kuma Raed se dare sossai suka koma Dukda shi ya fita ya sake dawowa ne don har wanka ya sake ya sauya kaya, yaran driver ya maida su tare da Tabawa da ta kawo musu abincin rana asibitin.

Duk yadda ya so ta bishi gidanshi ƙiyawa tayi, tace ya bari hankali ya kwanta tukuna har fushi yayi amma kan tayi bacci seda ta san yadda tayi ta saukar dashi.

Washegari basu tashi da wuri ba se around 11 ma suka karya sbd gajiya, baba Buba baya bukatar abinci don ance ko ruwa ne kar a ajiye inda ze gani har ya ji kwaÉ—ayi kuma asibitin full kula suna samu, wanka suka yi suka shirya hidayat ta fita tayi kyau sossai cikin Atampha me ratsin ja ta kafa É—aurin zara buhari da ya zauna mata da katon mayafi red, daga takalmi har jakanta red ne tana son colourn ko don ta san yadda yake mata wani irin kyau ne oho, wuraren azahar Raed da driver suka dauke su zuwa gidan Abba.

Ga mamakin hidayat gidan a cike yake da en uwa da abokan arziki, don kaman ƙwarya ƙwaryar liyafa Abba ya Haɗa na welcoming ɗin princess ɗinshi home, dukda rashin karfin jikin hamza da rashin ganin hajiyar shi haka Abba ya saka shi daga daman shi suna taryar baƙi tare.

Gidan ko wurin parking babu sbd rantsa rantsar Motoci dake cike da harabar gidan har zuwa waje, uncles É—inta biyu suka rungume ta suna hawaye, sossai taji daaÉ—in ganin family É—inta masu dumbin arziki ne, hakanan masu karamci ne, se a sannan take ba Abba labarin haduwar ta da kakanta, hamza yace kwarai har yana gayawa Abba da uncles É—inta irin complement da Kakansu ya bayar akan hidayat ashe Allah yayi zasu ga juna Dukda basu san alakar dake tsakani ba.

Hidayat fa taga gata, kowa Seda ya san ita ɗin fa ta dabance wurin mahaifinta, hakan yasa duk wadda ya tashi tafiya se ya ajiye mata kyauta sbd ya sanya Abbanta farin ciki, aiko duk wadda ya bata ko min kankantan abu yana ganin ainihin farin ciki daga fuskan Abba, ta tashi da cheques na kuɗi har suna bata tsoro har da kyautar mota da gida duka ta samu sbd mahaifinta da ba ƙaramin mutum ba.

Hidima sossai aka yi se la'asar likis abokai da dangi na nesa suka watse bayan an yi exchanging contacts da Hidayat saboda zumunci ya ci gaba da daurewa.

Masu aiki suna ta hidiman tsabtace gidan da rumfunan da aka yi taron na cikin tamfatsetsen garden na Abban, yayinda Hidayat, Abba, Raed da kuma hamza suka fito don shiga cikin gidan suna sake tattauna irin baƙin na yau, don har yanzu en uwa na kusa na ciki da uncles ɗinta, matansu da yaransu se maman Rashida da kuma Rashida, ga Daadida da yaranta duk suna daga parlor.

Hidayat taji daaÉ—in ganin yadda Hamza yayi matukar kokari wurin sakewa don ko a fuska be kyamaci Raed ba bare ya ji haushinshi, dukda yadda dayawa suka nuna ainihin jin daaÉ—in ganin mutum irin Raed aka yi ta hotuna dashi ya zama kaman topic a taron sede ga mamakin shi er uwarshi yake taya murnar samun miji kaman Raed har ranshi.

Da kanshi yayi introducing Raed as Mijin Hidayat ga mutane dayawa kuma as yayanta ta ɓangaren uwa, har en jarida sun taru a wurin don dayawa se a lokacin suke sanin shahararren attajirin nan Alhj Usman Tafida ya tashi bisa kafafunshi bayan jinyar da ya sha na shekaru da dama, kirkinshi da irin taimakon bayin Allah da yayi a rayuwa sadda yake da lafiya ya hana TAFIDA'S mutuwa daga kamfanunnukanshi na fata, na Motoci, na sarrafa kayan abinci, na wayoyi da manyan shares ɗinshi duk suna running har kawo yanzu da taimakon Allah.

Shigowar wasu buzaye ya saka su dakata wa, masu gadi ke kokarin hana su shiga se Hamza yayi magana, É—aya daga cikinsu ya zo da sauri yace

"Alhj waennan É—in kaman buzayen Nijar ne sun zo wai suna son ganin Mama akan ta basu adireshin da zasu ganta anan, to a gaskiya mu dae bamu san wata mama a gidan nan ba hakan yasa muka hana su shigowa"

Hidayat tace
"baƙin Daadida ne, Barsu su shigo muji me ke tafe dasu!"

Shigowa suka yi buzaye ne da irin shigarsu ta asalin buzaye, mazajen biyu kayan nasu baƙaƙe yayinda mata biyu sanye da brown da kuma farin mayafi duk fuskokinsu rufe.

Suka ce
"sannunku!"

Hidayat tace
"ku ne muka yi waya jiya ko?"

Wadda yayi magana da farko yace
"kwarai kuwa Æ´ar nan"

Tace
"mu karasa ciki ko?"

Sun juya zasu shiga kenan aka wangale gate, motar Hajiya ta kutso kai, ba'a gama daidaita parking ba ta fito tana gyara É—aurin zaninta, tun kayan shekaran jiya ne jikinta a birkice take kaman kace kyat ta zura da gudu, wucesu ta zo zata yi a fujajan se suka HaÉ—a idanu da É—aya daga cikin buzayen nan..

Chakk ta tsaya tana kallon ta, kai ta sosa ta sake sosawa tace
"Ke AISHA! Me ya kawo ki? Me ya dawo dake??? Ba kin tafi har abada ba?? AISHA! Aisha kin kashe ni! Aisha ke azzaluma ce Aisha shikenan na haukace...! Na lalace wayyoooooooo"

Ta zabga ihun da ya fito da duka mutanen gidan tana cisge É—an kwalin kanta.

Alhaji Usman da ya tsaya tuntuni yana kallon idanun buzuwar ya fara takawa zuwa gareta ba tare da ya damu da Hajiya dake kururuwa ba, hannunshi da jikinshi duk rawa suke daga yadda ta kasa kallon cikin idanunshi ya ji a jikinshi cewa Hajiya Balaraba ba haukanta bane ya motsa.... AISHA TA GANI.

Hannu yasa ya sunce É—aurin fuskan nata se ga fuskan ta tarrr ya bayyana, baya Daadida da Alhj Usman suka yi zasu zube se Hamza yayi saurin tare Daadida yayinda Raed dake kusa da Alhj Usman ya tare shi yana kallon Aisha.

Me ya razana su haka da kallon fuskanta?

Hawaye ne ke kwarara bisa kamilalliyar fuskar ta wadda bazaka kirata da dattijuwa ba saboda da matukar wuya ta haura 40, Kallo É—aya zaka mata ka san fara ce amma ta disashe zuwa kalar duhu hakanan kallo É—aya zaka mata kaga ramarta Dukda daga idanu zaka san wannan tana da garin jiki me kyau.

Waje hajiya zata yi wannan buzu ya kama ta ya fara ambaton wasu Adu'o'i se gashi ta É—an natsu tana soshe soshe sede bakinta be dena ambaton

"Aisha! Me ya dawo dake??? Aisha kin kashe ni?? Shikenan na haukace?? Aisha ta haukatani" ba, ko kuma ta kira sunan Aisha se ta kwashe da dariya.

Mutumin ne yace
"Maganganun dake tafe damu ba ze yiwu mu yi shi a tsaye ba, kowa na bukatar wurin zama"

Se a lokacin Abba ya fusgo numfashi yace
"Aisha dama kina raye?"

Daadida tace
"Dama baki mutu ba Aisha na?? Kina duniya? Ya aka yi aka sanarwa hidayat cewa kin mutu? Wani irin baƙar kaddara ce wannan da ta saka jikata tashi a matsayin marainiya gaba da baya bayan da uwarta da uban ta? Ina kika shiga tsawon lokacin nan baki neme mu ba har ni mahaifiyarki?? Aisha me yasa da Buba ya kore ki kika zaɓi ki tafi ba tare da kin kara ko da second guda ba? Duk laifina ne..... Ni ce na bada kofa..."

Kuka take sossai wadda yasa Aisha ɗauke idanunta daga kan Abba karon farko ta nufi mahaifiyarta, tana isa kawai ta faɗa jikinta ta fashe da wani tsumammen kuka! Kuka take daga ƙasar zuciyarta.

Cikin muryar kuka tace
"Maa...maaa na bar yarinya ta hannun wani bawan Allah....! Na dawo naje har gidanshi basa nan...! Mama na haihu lafiya sede ko fuskanta ban iya na gani ba! Ko sunanta ban iya sani ba mama! Wace irin uwa zata dauke ni??? Ta ina zan fara nemanta??? A ina zan ganta??? Allah na tuba ya Allah! Allah idan wani laifi na aikata da ban sani ba ya Allah ka gafarce ni ka taƙaita min wannan azabar rayuwar!!"

Daadida tace cikin kuka tana kara rungume Aisha dake shiga jikinta tana kuka jikinta na rawa tace
"Allah baya bacci, Allah ya fi mu sanin daidai da ya zaɓi raba wannan zuri'a har kawo yanzu da ya haɗe mu wuri guda, Aisha seda yarinyarki ta bayyana kan bayyanar ki! Ga ƴar ki chan na cikinki! Gata chan ta tashi cikin kewa da tsananin begenku gabaɗaya! Gata chan sunanta Hidayat.... Ki je gareta ta ji ɗumin jikinki kaman yadda kika zo kika ji nawa na tabbatar da cewa ba fatalwarki bace ko mafarki nake ba"

Da sauri Aisha ta miƙe tsaye ta fara kallon direction da Daadida ke nuna mata, hidayat ce tsaye kaman mutum mutumi idanunta da suka rine zuwa jajazir duk a waje, da sauri Aisha ta mike tsaye tana me kallon hidayat, wani irin kallon kallo suke aikawa juna kan suka fara ɗaga kafafunsu a hankali kaman masu tsoron taka ƙasa suka nufi juna..
Chapter 60 · 0% Book details