← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 74

Sashe 62

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka muka sake komawa wurinshi ya bani wasu magungunan, zamana da yaya babu matsala amma Alhj yau lafiya gobe babu, na sha wahala sossai nayi ta rashin lafiya don sau kusan biyar ina yin ɓari, bani da sirrin da yaya bata sani ba tsakanina da miji na, kwarai naji tsoron Allah na ji tsoron munafukin mutum me fuska biyu, don na bata yarda ta ci amana ta, tana da baiwar lafuzza wadda ko baka so idan ta kanainayeka se ta ji cikinka da salon munafurcinta.

Mun je kasashe kusan biyar ganin likita akan yawan ɓarina sede ba chanji, wani cikin da nayi Seda ya shiga wata na bakwai nayi nakuda me matukar wuya na kusan sati, na fita hayyacina gabaɗaya saboda wahala a lokacin muna a Saudia, da taimakon Allah wani malami kuma likita ya taimaka mana inda na haifi kadangare, iya tsoro mun tsorata nan ya kwantar mana da hankali ya tabbatar mana aikin asiri ne akwai Mahaifinshi ze taimaka mana.

Mutumin nan ya taimake mu tsawon wata shidda nayi jinya kan na dawo garau, tun yaya na mita har ta gaji ta kyale mu a Tunaninta zama kawai muke ko jinya nake ta hanani zaman lafiya, bamu baro Saudi ba seda na samu cikin hidayat na wata uku.

Ko da muka dawo wurin Adama naje muka kara komawa wurin mahaifinta nan yayi ta min nasiha yace kuma in kiyaye kishiya ta shima kuma ze cigaba da bani taimako, anan na fara jin tsoron Yaya don tabbas na yarda fuska biyu gareta.

Da ta fahimci hakan se ta fara nuna min ainihin halin ta a fili, munafurci da kirsa babu wadda ban gani ba wurin yaya, wani lokacin Alhj ya yarda wani lokacin kuma Allah ya taimake ni, duk burina akan cikina ne, nayi alkawarin bashi kariya da raina da numfashina, babu abunda zata bani inci tayi yin duniya ta gaji ta kyaleni, cikina na wata takwas wani rana ina kwance bayan nayi walaha se bacci ya É—an sureni.

Mummunan Mafarki nayi macizai na fito min daga jikin gini zasu marasa kyaun gani, bakunansu na zubar da bakin jini kuma suna kiran sunana cikin muryar amsa kuwwa, a firgice na farka se muka HaÉ—a idanu da yaya da sauri tace

"Aisha!"

Nace
"Na'am yaushe kika shigo?"

Wannan magana shine na karshe da nayi da wani a gidan Alhj, a take naji na tsani environment É—in da gidan na tsani garin Kano gabaÉ—ayanta, kaman tunzura ni ake ana turani akan in bar garin, da hijab a jikina jakana kawai na É—auka na rataya na fice ba tare da na sake ko waiwaye ba.

Tasha na iso ina ji na ba lafiya ba, kaman me maƙuwa haka nake ganin kaina bana gane duk wani magana da ake a gefena ko a kusa dani, da taimakon Allah na ambaci Taraba a tashar nan suka gane inda nake son zuwa kenan aka ce min rana yayi motocin jalingo sun tafi sede Gombe, haka na biya na Gombe.

Kusan tafiyar awa takwas ta kawo mu Gombe Dukda tarin gajiya, yunwa da ƙishir ruwa da nake ji haka na sake neman tasha ba tare da na damu ba na biya kuɗi aka sake dauka ta zuwa Taraba(jalingo) nan ma wata tashar na nema na samu motar da za shi gembu, kafafuna sun kumbura sumtum in banda sunan garinmu ban yiwa kowa magana ba tun fitowa ta don kaman bebiya na zama duniyar tayi min shiru babu abunda nake so illa in yi nisa da Kano.

Kwana nayi a hanya don ban isa gidanmu ba se wurin karfe goman washegari, jiri nake gani sbd yunwa ga tsohon ciki da kyar na iya na kawo kaina gida, amma se yaya Buba ya ƙi amsata bakin ciki da ciwon da nake ciki ya hanani iya furta ko wacce kalma don ko nace zan furta ɗin ma bani da tabbacin magana me anfani ne ze fito daga bakina don kwakwalwata ya riga ya juye gabaɗaya bana jin nice karan kaina.

Yana wullo ni na samu na kare cikina, na mike ban tsaya ba don nan É—in ma ji nayi na tsani kowa, na mike na naushi hanya nayi tafiyar kafa na kusan awa uku zuwa huÉ—u don bana gani da kyau kafafuna basu iya daukana, ashe na bar gari ma gabaÉ—aya na fara shiga tsaunuka, anan na faÉ—i.

Na farka na tsinci kaina a wani gida cikin wasu mutane, da kyar na iya buÉ—e idanuna cike da son fahimtar nan É—in ina ne, se na fahimci kaman gida ne na masu zaman kansu ko na haya, don wasu na zaune suna karta, wasu na shaye shaye, wasu na
Cacar baki, wasu na wanki suna jin wakokin da daga ka ji zaka san ba na mutanen arziki bane, babu abunda babu a tsakar gidan en daudu, mata da maza.

"Kin ganta nan riba biyu, ga na É—an ciki ga na jikinta.. A nawa zaki saye ta?"

Matar da tayi kama da tsohuwar kilaki tace
"amma ai kaman bata da cikakken lafiya gaskiya Ba zan baka ya wuce dubu É—ari uku ba"

Yace
"kai Asabe! Kin san Allah duk gembu ba zan sama miki irin macen da kike so me kyau da diri kaman wannan ba, ina me rantse miki tana haihuwa shikenan zaki fara Moran ta yadda ya dace"

Ina kwance kaman mutum mutumi ana ciniki na, daga karshe dubu dari biyar ta bashi, ta sa aka kama ni aka kaini wani É—aki ina rungume da jakana da be bar jikina ba.

Abinci aka kawo min saboda irin yunwar da nake ji jikina na rawa ainun na hau ci hannu baka hannu ƙwarya na gama na sha ruwa se bacci, ba zan tashi ba se idan lokacin sallah yayi wannan kam Allah be mantar dani ba zan tashi na gabatar na sake komawa bacci, bana tashi se yunwa.

Idan suka hana ni baccin kuma to haka zan kwana in yini ina maganganu wadda suke alakantawa da hauka, don zan yi kuka, in yi dariya duka ni kaÉ—ai.

Seda nayi sati uku wannan gida ba tare da na san a ma wani gari bane, wata rana tsakar dare wuta ya tashi a gidan.....

#Vote
#share
#comment

                 🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 41*

*FREE BOOK*

*Sorry! Jiya bamu da wuta wayana ya mutu kan wuta ya dawo kuma na wuce Garinmu a bacci! Yauwa I want to talk about ghost readers, kun ganku? Babu na gode, babu comments se an kwana biyu ba'a ganka ba se kaga ana cewa "wacce kam shiru!" "Yau babu kowa yaga zabuwa" ko kuma masu cewa "continue" Abeg ku duba wahalar da mutum yake sha wurin wasa kwakwalwa, data, hannu da idanu wurin faranta muku ku faranta mishi kuma... Typing is not a joke I repeat ba wasa bane wlh! Allah yasa mu dace***

Wuta sossai ya tashi a gidan ba tare da na sani ba saboda baccina ba na lafiya ba, wata ce ta zo ta tada ni karfi da yaji ta Jani muka hau gudu muka fita daga gidan kaman yadda sauran jama'ar gidan kowa yayi ta kanshi yayinda wasu daga ciki suka ƙone kurmus ciki harda magajiya, dab asuba kowa ya kama gabanshi haka nima na nausa nayi ta tafiya ban damu da dubun dare ba banda jakana da nake rungume dashi ba dare ba rana ko takalmi babu kafafuna.

Karnuka sede su min haushi su gaji su wuce amma ko ta kansu bana bi bare in tuna wani abu wai shi tsoro, jikin wani gida na samu na zube a wurin saboda gajiya da nayi ga bacci ina ji, pillow nayi da jakana na hau bacci a wurin Dukda uban sauro dake yawo a unguwar.

"Baiwar Allah! Baiwar Allah!!"
Wata murya ke ta ambaton hakan har Seda na fara buÉ—e idanuna ina lumshewa, ganin garin yayi shaaaa Dukda be zama haske tangararam ba hakan yasa nake iya kallon kamilalliyar fuskanshi yace.

"Me kike yi anan haka da tsohon ciki? Na fita zan je masallaci na ganki har kuma na dawo baki tashi ba! Baki tsoron sauro ya illatar dake da abunda ke cikinki?"
Ban amsa ba se Kallonshi kawai da nake, chan na iya buÉ—e baki kaman an fusgo maganan nace
"ru....wa"

Yace
"tashi! Tashi mu shiga gida se in baki kisha"

Da kyar na iya mikewa sbd nauyin jiki da ciwon kafafu, haka muka shiga gidan nashi tun fitowa ta shine mutum na farko da ya tausayamin har ya taimake ni ba tare da ya san ko ni wacece ko daga ina nake ba!

Mutum ne me matsakaicin karfi don baza'a kirashi me kuÉ—i ba, gida ne daidai na rufin asiri, sallama yayi cikin babban sashen.

Wata mata ta fito tana kallonmu É—aya bayan daya, yace
"Umman khausar ga bakuwa nan don Allah kaita extra room É—in nan ki bata ruwa in akwai wani abu a gidan ki bata kan a gama abin kari!"

Kallon tara saura kwata take mana daga ni har shi seda ta gama kare mana kallo kan tace
"amma Abban Yusuf ka ma raina min wayau, haka kawai ka shigo min da mace da tsohon ciki rimi rimi ka wani ce in bata extra É—aki da abinci? Ina ka samo ta da sassafen nan?"

Yace
"tsaya tukuna Amina gidanki ne nan kam ko gidana? Taya zan ce ga abunda za kiyi kice ba haka ba matar nan tana tsaye tana jin jiki?"

Dariya tayi ta tafa hannu tace
"Aaaa lallai ni dayake ba ciki ne jikina ba a kwance nake ina jin daaÉ—i, taya zaka fara fifita wata kaina? Kab zuri'arku ban san me kama da aljannu ba bare in ce daga dangi take.."

Juyawa yayi ya kalleni yace
"zo mu je baiwar Allah"
Chapter 62 · 0% Book details