← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 74

Sashe 39

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya saki ganinta da Hidayat ya san maybe ƙawarta ce, hidayat ce ta ja hannunta suka shiga motan tana sake kallon Raed, yau gata ga famous footballer da sede a kalla a TV ko a waya.

Har suka isa gidan bata dena mamaki ba, no wonder Norah suke kama sossai ai ita babbar fan É—inshi ce.

Ko da suka isa gidan haka tayi ta kallon gidan kaman bata taɓa shiga gida irin shi ba kuma duk sbd dumbin mamakin yau gata a gidanshi har ciki ciki take yi.

Ko da suka isa É—aki hidayat ta mata masauki tace bari ta samu simple abu ta yiwa yaran se suyi magana.

Norah ta turo ta kawo mata ruwa da snack, se ga Aisha da Junior sun shiga karɓan shi tayi tana mishi wasa.

Da Norah da ta fara shiga kitchen suna ayyuka tare tayi girkin ta gama ta zuzzuba musu lokacin da ta kai É—aki rike da wani madaidaicin haÉ—aÉ—É—en tray É—auke da warmers masu kyau da daga gani zaka san ya ja kuÉ—i ta samu tana sallah

Itama ruwa ta watsa tayi sallah, suka ci abinci kan hidayat ta fuskance ta.

A hankali ta fara bata labarin rayuwarta tun daga farko har kawo yau, se ga Rashida na kuka kashirban wallahi ita ko a labari bata taɓa gamo da irin na Hidayat ba..
Seda ta nitsa kan tace
"sannu hidayat lallai kinga rayuwa! Kuma daga hamza har Raed sun taka muhimmiyar rawa a rayuwar ki sede ko kama kafan na Raed hamza be yi ba.."

Kai ta gyaÉ—a tace
"na sani, Raed shi ya sama min rayuwar da nake cikin yanzu cikin sukuni da salama shiyasa nake iya yi na wurin ganin na taimakesu da yaranshi yadda zasu samu aljanna suma ta sanadiyata"

Rashida tace
"Amma Allah ya tsinewa Yusuf!"

Dariya maganan ya ba hidayat wadda se da ta dara ganin yadda Rashida tayi maganan kaman taga Yusuf a gabanta ta bindige.

"Hidayat maganan gaskiya ina Tunanin ke da Raed kuna son juna..!"

GabaÉ—aya idanunta ta waro
"Ki rufamin asiri don Allah karki faɗa wani ya ji... Me Irin Raed ze yi dani? He is my boss for goodness sake in don damuwar da na shiga ne ba wai sbd wani abu bane ina baƙin cikin kasancewar shi cikin masu aikata laifin zina ne ba komai ba.."

Rashida dake sake da baki take kallonta tace
"ni bance ki kare kanki ba, sede fa na san Raed kuwa shi ke da abunda ze yi dake, wai kina kallon madubi kuwa? Wallahi idan ba don na kalli Aisha da Junior kuma naji labarin ki ba ba zan taɓa yarda kin haifesu ba.. U are really every man's dream kaman yadda Raed yake every woman dream kinga kenan se ku haɗu ku bada kala..."

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"ni yanzu ba wannan ba Rashida taya kike Tunanin zan yi facing nashi da maganan haramcin zina? Yarinyar nan don bata da kunya kwance fa dare dare na sameta jikinshi jiya haka ma rannan.."

Dariya Rashida tayi kan tace
"uhmm, kawai ki fuskance shi ki mishi magana ta hankali da basira..amma ni de na san kuna son juna gwara kun dena kauce kauce ke kin mishi maganan wani ya É—au fushi ke kuma ya kawo buduruwarshi kin hau koke koke!"

Duka take shirin daƙa mata ta ja baya tana dariya, ajiyar zuciya hidayat ta sauke tace
"amma ni kam hamza nake tunani! Shine ya furta mini kalamar so tun ban san kaina ba, bayan na fito ya sake tara ta da Kalmar so ba zan iya watsa mishi ƙasa a idanu ba zan yi Adu'a idan Hamza Allah yace in aura se kiga an yi Dukda yanzu auren baya gabana.. Don ban tsinci komai cikinshi da ze sani sake marmarin koma mai da garaje ba"

Ajiyar zuciya Rashida ta sauke itama tana duba hamza kam daga ganin yadda yake yiwa hidayat zaka san irin su ko kwanciya tace yayi tabi bayanshi ta wuce tsab ze kwanta.

Tattaunawa suka sake yi kan, rashida ta mike da shirin tafiya.
Har ƙasa ta raka ta kan ta koma, tana jin hayaniyar su Norah a ɗakin Farrah sede bata leƙa ba ta nufi kitchen daidai lokacin shi kuma ya fito riƙe da coffee a hannu, saura kaɗan suyi karo yayi saurin janyewa har coffeen na fantsalar mishi a hannu, runtse idanu yayi a ɗan razane tace

"Subhanallah! Sannu don Allah ban san kana zuwa ba"
Kai ya gyaÉ—a mata ze wuce tace
"am..umm don Allah ina so ne muyi magana yallaɓai"

Kallonta yayi se ya kalli parlor, ta gane ba son Magana yake ba hakan yasa ya nuna mata da idanu akan suje parlor.

Seda ta bari ya je ya zauna kan ta zo ta zauna itama cikin lafazi me taushi ta fara magana na hankali.

Ayoyi da hadisai waenda ta sani da suka yi magana akan zina da haramcinsu ta fara ja mishi tana yi idanunta na cika da hawaye tana sharewa tana iya tuna a farkon aurenta da Yusuf a sadda ta fara fahimtar irin banzar É—abi'ar shi ta zauna ta mishi wannan nasihan sede dukan da ya mata a yanzu da ta tuna Seda taji a jikinta kaman yanzu abun ke faruwa take duk wani tsika na jikinta ya tashi.

Tsam ya miƙe daga inda yake ya dawo kusa da ita yana shirin zama tayi saurin saka hannu tana kare fuskanta a razane tace
"Don Allah kayi hakuri ya yusuf...!"

Wani irin karyewa zuciyarshi tayi, after some months da ya kusa rufa shekara don yanzu wata ya saura ta cika one year da barin Nigeria, har yanzu akwai wannan taɓo ashe ƙasar zuciyarta? Tausayinta ne ya motsa a ƙasan ranshi wadda ya saka shi lumshe idanu a hankali yace

"calm down hidayat ban taɓa dukan ko kare bane bare mutum..! A jinsin ma ba namiji ba Mace.. I can't!"

Hawayen idanunta ne ya gangaro tayi saurin dawowa hayyacinta tace
"kayi haƙuri please"

Ya É—an yi murmushi yace
"kalma me sauƙi kenan a bakinki na fahimta"

Gyara fuskanshi yayi yace
"Hidayat." Da sauri ta É—ago Seda suka HaÉ—a idanu yace

"ban taɓa aikata zina ba hidayat! Zina na daga cikin abunda na kyamata a duniya bayan shan kayan maye da tattoo... Ban sani bane ko Allah ya kare ni saboda watakila mahaifiyata ta taɓa yi min Adu'ar kariya daga sharrin su, ban sani bane ko Allah na so na da rahamar shi ne yasa ya kare ni all I know duk yadda mata suke rububin kawo kansu gareni a kyauta ma ban taɓa kallon wata da fuskan sha'awa ba."

Se kunyar maganan da tayi ya kama ta, Allah sarki ta mishi mummunan fahimta sede duk wadda ze ga yadda kimorah ke shishige mishi da yadda suke kwana ɗaki daya kaman yadda take ji bakin su Norah Dukda ta kan kwaɓesu kan maganan yaje ko ina har yanzu ma sun bari, tsab zaka ce sun yi ɗin ashe shiyasa Allah ya haramta shedar zina anyhow...

"Am sorry!"

Yana kallon fuskanta dake nuna kunyar da taji se yaji ta burge shi, be taɓa ganin wata na kunya a gabanshi ba se yau ko don rayuwar turawa ba ruwansu da wani kunya ne oho..

"U don't have to! Se menene kuma be da kyau?"

Yayi maganan da iyakar gaskiyar shi.

A hankali ta É—ago ta kalleshi se suka HaÉ—a idanu sun É—au seconds suna kallon juna kan ta kalli gashin kanshi da kana gani ka san ba kananun kuÉ—i ya ja a gyara da style É—in ba, ta kuma kallon kunnenshi dake É—auke da É—an kunnen diamond ga dama ta samu sede tana tsoron kar ya ki amincewa saboda ta san yana mishi kyau ne ya saka.

"Uhyimm...!"
Ya faɗi kalamar daga ƙasan makoshi wadda seda ta ji har tsakiyar jininta.
Tattaro kuzarinta tayi ta fara magana.

"Akwai hadisin da annabi yayi magana akan maza masu shiga ta siffa irin ta mata sakamakon su wuta ne hakanan mata masu shiga ta sutura da kamanni irin ta maza su ma hakan ne"

A hankali ya sa hannu ya cire É—an kunnen kunnenshi se ya wara mata fari Kal É—in tafin hannun dauke da É—an kunnen yace
"is it about this?"

Kai ta gyaÉ—a. Yace
"as from today an gama... Then?"

Kallonshi ta sake yi cikin kokonto yadda yake yin komai ba musu ko tantama shi ya fi tafiya da ita.

"See ina so na zama pure, a irin wa'azuzzukan da nake ji about jannah and hellfire I really want to be among alhul jannah... I badly want my relationship with my almighty to be good! U are an angel sent by him to us idan kika gani don't resitate kiyi mana gyara because maybe kan mu gani a Wa'azin ya jima.."

Ajiyar zuciya ta sauke tabbas kalamanshi masu tasiri ne, hakanan tsantsar gaskiya ce a ciki kwarai da dalilin haduwar rayuwarsu, komai dama Allah yayi shi cikin qadr.

"Wannan hairstyle.. Akwai hadisin da annabi yayi magana akai inda yayi hani da aske gashi rabi da rabi, wato a kwashe wani ya fi wani tsawo sede idan zaka aske ka aske gabaÉ—aya hakanan idan zaka tara ka tara gabaÉ—aya"

Kai ya gyaÉ—a yace
"I will change this hairstyle first thing in the morning... Thank you. Se me kuma?"

Tace bayan ta maida kanta ƙasa
"taɓa mace ko namijin da ba muharramarka ba ko da ba da sunan zina bane annabi yace da ka aikata hakan gwara an buga maka kusa inci tara a tsakiyar kanka"

Idanu ya lumshe yace
"Noted! Se mene?"

Ta É—ago ta narke fuska wadda ya saka shi ganin ta koma baby Farrah ko junior tace
"saboda nice sarauniyar kakale kakale ko? To ya kare"

Dariya ta bashi wadda seda ya murmusa har sautin ta fito.

"I thought akwai wani abu ne kuma and u don't want to say because of ur silly reansons da ban sani ba"

Kai ta É—an karkata kan tace
"akwai na tuna"

Ya bata hankalin shi yace
"what's that?"

"Am sorry boss! Don Allah kayi hakuri"
Kallonta kawai yake irin kallon da ya sakata jin kaman ta narke, kaman ƙasa ya buɗe ta shige ko ta ɓace nan take su turawan nan basu san ruwan kunya ba.
Chapter 39 · 0% Book details