← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 74

Sashe 27

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Seda likita ya sake dawowa ya sa mishi drip sbd jikin dae ba daaÉ—i, ba jikin kaÉ—ai ba har zuciyarshi likitan ya tsorata ganin ciwon da suka samu suka raba shi dashi karfi da yaji ne ke shirin sake dawowa, idan kuwa hakan ta kasance har career É—inshi se yayi affecting..

Yana fita ya kira Father ya sanar dashi, a rikice yace ze bi available flight yau ya zo Paris É—in.

Norah da Farrah jikinsu duk yayi sanyi kaman sune ba lafiyan har Aisha da kyar ta lallaɓa su suka tafi school, ita ta girka mishi abu marar nauyi da kanta ta kai mishi..

Cikin karfin hali ya mike yayi brush da ta É—auko mishi har nan ta ajiye mishi abincin, kaÉ—an yaci yace ya koshi, maganin shi ta ballo ta bashi ya sha da coffee É—in da ta hada mishi.

Tattare wurin tayi ta fice, da kallo ya bi ta har ta rufo kofan ya koma ya kwanta.

Da rana ma haka ta sake kawo mishi cikin muryarshi yace
"baki je school ba?"

Kanta kasa tace
"eh, idan na tafi babu me kulawa da kai"

Motsi me karfi yaji zuciyarshi tayi da Seda ya runtse idanu, a hankali ya buÉ—e yace
"thanks"

Kai ta gyaÉ—a, tace
"ko zaka yi wanka sir?"

Kai ya gyaɗa mata kawai, ta shiga toilet ta hada mishi ruwa me dumi ita dae taga turarukan wanka kala kala a bayin sede bata san wanne yake anfani dashi ba hakan yasa bata saka ba ta fito, ya miƙe yana dafe gini ya wuce nan ma jarumta kawai yake da karfin hali amma shi kaɗai ya san me yake ji..

Yana shiga ta hau gyara É—akin, fes ta gyare cikin lokaci kankani, bata bari ya fito ya sameta ba ta fice daga É—akin..

Abincin Æ´an makaranta ta hau yi bata gama ba taji motsin shigowa, kuma bata ji hayaniyar yaran ba..

Da sauri ta ajiye abun hannunta ta leƙa se suka Haɗa idanu da kakkarfar mutumin sanye da wando da riga me yanayi da dogon riga baƙi da fari, se wani abu kaman mayafi da ya ɗaura saman rigar igiyar har wurin gwiwar shi, katuwar sarkar cross sanye a wuyan shi se Bible rungume a hannunshi na dama Ɗayan hannun kuma brief case.

Fitowa tayi a ladabce don bata san wanene ba tace
"u r welcome sir"

Kallonta yayi sama da kasa wannan ce kenan da Raed ke faɗa itace sabon nannyn yaran, aiko se ta bar gidan daga gani ma itace sanadiyar ciwon shi da ya tashi tunda a farkon barowansu Nigeria a duk sadda ya ga baƙin fata se ya shiga panic attack, ya zo da wata baturiya daga Amsterdam na Kasar Netherland da dama yawancin zaman shi a chan ne don hakan sallamar wannan dole.

Ba tare da ya amsa ta ba ya wuce zuwa room É—in Raed, Seda yayi knocking kan ya buÉ—e yana shiga idanunshi suka faÉ—a bisa kanshi, da sauri ya karasa yana cewa
"Son!"

Tare da riƙe hannayenshi yana zama bakin gadon, 3 quarter ne a jikinshi da ya zazzage daga sama ya fitar da boxers ɗinshi fari Kal jikinshi ba riga yana jingine da gado yana duba phone ɗin shi ɗakin banda sassanyar kamshinshi me cike da wani ni'ima da sanyaya zuciya na musamman babu abunda yake ga sanyin Ac.

Murmushi ya saki yace
"father finally ciwona ya sa ka zo, Princesses will be happy today"

Yace
"drop that son! Me ya faru? What brings this illness back? Na tabbatar wannan baƙar fatar ce da ka ɗauko"

Kai ya girgiza yana tuna damuwarta da ciwon nashi wadda a rayuwarshi baze ce ya taba ganin makamancin tausayinshi a fuskan wani ba bayan nata, ya karanci ba karamin jimami take ba shi kuwa be san tsoronta na in ya mutu a tsukukin nan yana cikin babban hatsari bane, taimakonta da yayi kuma wadda bazata taɓa mancewa ba yasa ta ci alwashi me girma a kanshi..

"She is not father, I just had a dream abt my past!"

Yace
"then seeing her is the essence, na yi hiring nanny from Amsterdam a well reserved person ita zata cigaba da kula min da jikokina u should fire this one, and that's final.."

Da sauri ya É—ago ya kalleshi..

***

Ita kuwa ganin ya wuce kai tsaye yasa ta saka a ranta maybe dan uwansu ne, komawa kitchen É—in tayi ta karasa duk wasu ayyukanta kan ta fito ta koma É—aki.

Kasa bacci tayi a jiya da Tunanin wani irin rayuwa Raed yayi. Shi kuwa menene tarihin rayuwarshi haka? Wanene shi?

Kasa hakura tayi ta lalubi inda ta rubuta landline number É—in Daadida ta saka kira..

Ringing na karshe aka É—aga
"Assalamu Alaikum jikata..!"

ÆŠan murmushi hidayat tayi tace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah ina yini daadida?"

Daadida tace
"mu a wurin mu har yanzu kwana ne, Awa É—aya da Æ´an mintuna ya rage mu shiga yinin"

Murmushi hidayat ta sake tsohuwar akwai barkwanci tace
"to ina kwana"

Tace
"lafiya ƙalau Alhamdulillah ya kuke duka? Ya wannan sarkin miskilancin? Wai fushi yake dani, in kira in kira ya ƙi dauka ja'iri kuma wallahi ba zan fasa gayamai gaskiya ba ko mutuwa ze yi"

Hidayat ta É—an yi murmushi tace
"yana kwance bashi da lafiya"

Daadida tayi salati ta sallame tace
"Allah sarki, Allah ubangiji ya bashi lafiya ya sa kaffara ne"

Hidayat ta amsa da
"Ameen"

Se ta É—an yi shiru cikin shirya kalaman da zata yi akan tsari tace
"Daadida kin roke ni a kan tallafar rayuwar uban gidana kuma na ɗau alkawari, sede duk inda na duba babu wata mafita har se in na san wanene Muhammad Raed, yaya rayuwar shi take wani giɓi ne ya samu yake buƙatar plaster se na san ta inda kuskuren ya faro kan in yi tunanin hanyar bi wurin gyara"

Daadida ta sauke numfashi me nauyi tace
"Hidayat shi ba giɓi bane a rayuwarshi, tubali ne bashi dashi kinga toshewa da plaster ba ze taɓa yiwuwa ba in har ana so yayi karƙo se an rushe an sake sabon dakakkiyar tubali, ina nan ina muku Adu'a, ina sadaka ina saukar Alqur'ani da yardar Allah mafarkin da na jima ina yi a kanki nake saka ran tabbatarsa don haka zan faɗa miki wanene Muhammad Raed...."

#Vote
#share
#comment

                 🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 19*

*FREE BOOK*

*Wannan shafi naku ne ɗaukacin masoyana da kuka tayani murnan kamalla bautar kasa ta lafiya, especially Gureenjo Novels group bazaku kirgu ba da na kirgo ku one by one sede in har kina karanta wannan just know that am really grateful and I sincerely appreciate...na gode sossai matsayinku a raina bazata kirgu ba kuma na ji daaɗi kwarai.. Allah ubangiji ya bar ƙauna😍🥰*

18/03/1986

Zaune take dabas a ƙasa saboda bazata iya jumrewa tsugunon ba hawaye ne wani ke bin wani a fuskanta tana sa hannu ta share lokaci zuwa lokaci, yayinda wani farin bafulatani tsayayyen namiji tsaye a kanta yana zabga masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba ko damuwa da a gaban mahaifiyar shi yake be yi ba.

"Ke kin san Allah wallahi na gaji, na gaji da wannan jarabbaben jinya naki, ke kullu yaumin ciki, a yayin cikin in sha wahala in kashe kuÉ—i ki ishe mutane da laulayi kika tashi haihuwa ki haifo mace, nan ma suyi ta jinya suna karya tattalin arziki na har su zo su mutu to wallahi Allah ba ze yiwu ba wannan cikin zubda shi za'ayi a juye mahaifar"

Dattijuwar dake zaune daga kan kujerar tsuguno ta zabga tagumi tana aikin kallon shi tace
"Bukar kayi hakuri ka bari tunda tana son kayanta ta haihu baka san ko shine me tsayuwa ba.."

Katse ta yayi da sauri
"A'a mama dama tun farko kece kike É—aure mata gindi shiyasa take jin daadi kuma take abunda ta ga dama"

Shiru matar tayi saboda ita karan kanta shakkar yaron na cikinta take yi, har ya juya ze fita ta kalli Mairamu dake kuka kaman ranta ze fita ta É—aga ta kalle shi tace
"Bukar!"

Da mamaki ya waiwayo saboda ya sani idan yayi magana ya zauna kenan ba me juya ta har uwar da ta haifeshi amma yanzu tana kokarin fara shiga sabgar gidanshi da iyalinshi kenan suma su ma su samu Daman raina shi kenan, fuskanshi a tamke ya amsa.

Tace
"Don Allah kayi haƙuri akan wannan kaɗai mun yarda idan be tsaya ba tun kan ta samu wani cikin se a juya mahaifar"

Shiru yayi na mintuna kan yace
"Tunda kin matsa ai shikenan sede fa ni ba ruwana ba kobo na da ze yi ciwo a akan cikin nan kuma hidimar aurena yadda take yi haka zata yi.."

Kallonshi kawai Daadida ke yi har ya fice, duk sauran da suke tsatsaye har ita  wacce aka kira da Maryam dake durkushe nannauyar ajiyar zuciya suka sauke, ɗaya rike da karfe varender ɗinta tace

"ke ma in banda jaraba tunda an ƙi samun namijin mama a hakura Haba!"

Na biyun tace
"Toh ina bakin ciki ze bari ke kuwa ba'a samu magajiya ko magaji ba"

Na ukun tace
"ni ba don ma haihuwar da take yi suna komawa ba da se ince wannan anya ba juya ba! To ko ni da nake Amarya yaushe na zo gidan nan har ina da biyu.."

Daadida tace
"ya isheni haka, babu ruwanku wannan tsakanin Maryam da mijinta ne.."

Baki suka taɓe kan kowacce ta juya ta shiga ɗakinta dake dauke da parlor da ciki ɗaya

Miƙewa Daadida tayi ta zo ta kama Mairamu ta mikar da ita da taimakonta suka koma ɗaki don haka laulayinta suke ba karamin wahala take sha ba..
Chapter 27 · 0% Book details