← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 74

Sashe 41

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Motsi Abban yayi wadda ya saka hamza waro dukkan idanunshi waje..
Kaman wadda aka Umarta a hankali yayi ta kokarin buɗe idanunshi wadda ya saka hamza Suman tsaye, wani irin sassanyar farin ciki ne ya lulluɓe shi yana mamaye dukkan ilahirin jikinshi.

Da gudu ya fito yana kiran hajiya.
"Wai menene? Ni kam na shiga uku na lalace hidayat ta haukata min É—a. Me hakan?"

"Hajiya Abba ya buÉ—e idanu, Alhamdulillah Abba ya farka hajiya.."

Harara ta maka mishi tace
"mutumin da ƙasar waje ma cewa suka yi mu sa hannu a karasa shi saboda babu ranar waraka shine zaka ce ya buɗe ido?"

Hannunta kawai ya janyo don ba ze iya magana ba, suna shiga kuwa Abba da ya rufe idanun saboda haske da ya mishi yawa ya sake fara kokarin buÉ—ewa ai murna a wurin su ba'a magana nan take suka fita dashi aka yi asibiti don ba zasu iya jiran doctor ba.

****

Zaune yake shiru a ɗaki yana jin wani irin tone tone da matan nashi ke yi suna baje iskan hammata, a razane ya miƙe tsaye da yaji sadda zarah ke cewa
"azzaluma me HaÉ—a husuma tsakanin uba da É—a... Wato abunda kika yiwa Raed har yayi sanadiyar barin shi gidan nan nima shi kike kokarin yiwa ta wa Æ´ar to ahir É—in ki me gida da mota dae se ta aura.. Ki ji da Æ´an daba da karuwan yaran ki"

Wani irin shewa Badi'ah tayi tace
"ai gwara ni abunda nayi me sauƙi ne, ke fa? Tsabar tsanar da kika yiwa uwar Raed ina anan kika shiga kika sace kuɗin malam ya zo ya lakada mata duka wadda sanadin shi ta gamu da ajalin ta...? Gwara ni sau dubu muna da mashinshina Dukda ƴar daban ce, karuwancin na ki  su samu mana"

Da wani irin gudun da be san akwai sauran karfin yinshi ba saboda cin rogo carbohydrate yayi yawa ya fito a hautsine yace
"maimaita abubuwan da kuke cewa ban ji da kyau ba...!"

Wiki wiki suka fara da idanu don tsabar masifa sun manta yana nan..

Da gudu yaje ya rufe kofar gidanshi ya dawo da arda da gora.

"Ko ku min filla filla ko in kashe ku in ya so nima se a kasheni...!"

****

"Rashida ba karamin mamaki yallaɓai ya bani ba...ban taɓa cin karo da namiji irin shi ba tabbas da a cikin musulunci tsantsa ya tashi da musulmai sun yi alfahari da samunshi"

Rashida tace
"kin zo se koÉ—a shi kike tuntuni ni baki gayamin ya kuka yi ba"

Dariya hidayat tayi tace
"Rashida Allah ya tseratar da bawan shi, ya min rantsuwar be taɓa aikata zina ba, abun mamaki shi da ƴan mata suke rububi a kanshi, ga kuɗi ga suna sede ya kiyaye jefawa zuri'ar shi bala'in zina saɓanin Yusuf da ko kafan takalmin Raed be kamo ba amma ya mai da zina ado a rayuwarshi"

Rashida tace
"hmm, ai shi Allah in ya so kare bawa ko tsirara mata zasu yi yawo gabanshi Allah ze kare shi, kuma kinga yayiwa kanshi babban kiyamul laili da baya shan komai"

"ban taɓa Tunanin Yallaɓai ze biyu ta sauki ba, yanzu damuwana tsakanin shi da Mahaifinshi"

"ke kin san wallahi ina Tunanin son ki da yake ne babban maƙamin da ya sa yake biyuwa ta sauƙi"

Harara Hidayat ta zabga mata tace
"ba so ba kin manta...!"

Dariya Rashida ta kwashe dashi tace "gashi daga magana kin fara blushing"

"Rashida tsakani da Allah tsoro nake ji"

"Tsoron me?"
Ta tambaye ta tana gyara zama.

"Rashida aure! Ina yin karfin halin maganan aure ne amma in na tuna da zancen auren wlh gabana faÉ—uwa yake, tsoro se ya shige ni. Ko kin san har yau bana samun cikakken baccin da ya kamata bawa ya samu?"

"Na sani Hidayat! Shiyasa nake so ki godewa Allah ki kuma godewa Raed, kina Tunanin ba don shi ba rayuwa zata miki saukin blending haka ne? Ko Kin san da a Nigeria kike da yanzu baki da maraba da mahaukaciya? Abunda yasa nace haka, a nan baki ganin violence hakan ya taimaka wurin baki cikakken natsuwa, da zaki ga ana faɗa se abunda baki yi tunani ba ya same ki, hakanan zama da yaran nan shima kwarai ya taimaka miki ai a likitance taɓon da Yusuf ya miki warkewarshi ba yanzu ba.."

Kai ta gyaÉ—a tace
"hakane, shiyasa bana iya kallon film Sam don yana sani tsorata.. Sau ɗaya na taɓa kallon Animation ɗin su Farrah, goigoi ne amma dayake ana duka da faɗa ciki seda na kwana ban runtsa ba haka jiya da buduruwarshi ta so tada husuma wlh baki ji yadda gabana yayi ta faɗuwa ba"

Rashida ta riƙe hannunta tace
"a hankali in shaa Allah komai ze daidaita, Raed ba irin Yusuf bane zaki rabauta da samunshi"

Zata yi magana wayanta ya fara ringing ta duba taga hamza tace
"Allah se na gayawa ya hamza karfi da yaji kike son danganta ni da abunda kin san ya fi karfina"

Tana kai nan ta É—auki wayan, suka gaisa ya faÉ—a mata farkawar dad É—inshi, sossai ta taya shi murna ta ba Rashida ma ta mishi murna, suka É—an kara magana kadan kan suka yi sallama.

Yau ko da ta iso gida bata samu yaran ba, ko da ta tambayi miss Mary tace sun fita da babansu.

A natse tayi sallah ta hau girkin rana.

Seda ta gama ta fara jerawa suka shigo suna hayaniya ga ledoji a hannunsu.

Farrah ta zo da gudu ta kama hannun ta tace
"Miss hidayat! We are going for a trip yeeeeey"

Hidayat na ajiye tray É—in hannunta tace
"easy Farrah, school É—in fa?"

Norah tace
"we are on mid-term break, Dad na da wasa a Belgium and he want us to attend"

Aisha ta miko mata ledojin hannunta tace.
"Dad made this shopping for you saboda kina makaranta and we don't know what u like"

Ɗago idanu tayi se suka Haɗa idanu yana riƙe da Junior, murmushi ya sakar mata itama ta mayar mishi ba tare da ta san tayi hakan ba, ta karɓi Ledar Hannun Aisha tace
"thank you Daddy!"

Dariya ta bashi sede be yi ba ya É—an murmusa.

Yace
"the trip is with u.. Hope bazaki samu matsala da karatunki ba"

Kallonshi tayi tace
"I don't think I can make it bcs ina da assessment this week"

Kwaɓe fuska duka su uku suka yi a tare suka ce
"oh no!"

Dariya sossai hidayat tayi tace
"ba wani abu ai u will enjoy the trip I trust Daddy"

Gira É—aya ya dage yana zama a dining É—in irin yeah É—in nan, dukda be ji daaÉ—in rashin samun zuwan tan ba, ganin kuma yaran da gaske sun damu yasa ya chanza shawara yace
"hey gurls! Calm down and eat ur food.. "Mommy" is going in shaa Allah"

Ras haka gabanta ya doka a sadda ya ambaci mommy ɗin, sossai jikinta ya karɓi sakon nashi don da wani kalar murya yayi anfani, ya wani lakaba mata mommy ita sa yaranta ma mama suke cewa su Norah kuma miss hidayat, Yaran ina suka sani se murnan zata je suke yi.

A hankali ta kalleshi, ya dage mata gira É—aya alamun what?

"Amma ma...."

"Shiii....!!" Ya ja I É—in yana É—ora dogon yatsanshi bisa saman tausasan lips É—inshi da yake tauna abinci a hankali, lumshe idanunta tayi kawai tana kauda kai...

#Vote
#share
#comment

                  🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 27*

*FREE BOOK*

*Afuwan jiya kun jini shiru was very busy ne*

Lip É—in shi ya É—an cija yana kau da kai daga kallonta, yaran ta zubawa abincin se ta zuba nata zata wuce É—aki ya ce
"Miss hidayat! Why can't u eat here?"

Farrah tace
"yes please you always don't like eating in the dining with us"

Lumshe idanu tayi tana jin yadda bugun zuciyarta ke harbawa, dawowa tayi ta ajiye plate É—in tare da É—an jan kujera ta zauna, daga su har yaran babu wadda ya sake magana se junior don ta hana su magana yayinda suke cin abinci, Sam a takure take don lokaci lokaci tana iya jin kaifin idanunshi a jikinta alamun yana kallon ta, hakan yasa take cin abincin kaman baby jikinta na mutuwa a hankali kaman yadda nashi ma yake amsawa.

A duk sadda ze ga lips É—inta yadda take tauna abincin kaman wani jan aji ko yanga wadda ya san duk ba haka bane rashin sabo ne kawai da ci a haka É—in tunda bata yi É—in, se yaji tsikar jikinshi na neman tashi... Tsammm haka yake shagala da kallon nata, hannun abincin ta kuwa har mantar dashi inda yake yake yi, sun riga sun saba da cimar kasashe barin ma French dishes Amma yanzu da ya kan zauna yaci abin da ta girka se yake jin ba ze iya cigaba da cimar Paul ba.

Ita kuwa askin da yayi ne yake ɗaukar hankalinta, a hankali take satar kallon kan nashi da lowcoat ya maidata se ya kara mishi wani irin kwarjini da haske, yanzu ne take Kallonshi as cikakken musulmi don in zaka ɗau lokaci kana Kallonshi kana iya hango taɓon sallah da ya fara yin baƙi daga goshin shi.

A duk sadda idanunsu zasu haÉ—u se su wani basar kaman ba Satan kallon juna suke ba, haka dae aka gama cin abincin ta tattare wurin suka koma parlor anan suka cigaba da tarihin annabawa inda take basu na Annabi Musa da firauna, sossai nan kam ya sakar mata idanu yana kallo wadda wani lokacin har kakarewa take saboda yadda gabaÉ—aya ta rasa natsuwar ta take neman Rikicewa..

Fahimtar hakan ya saka shi sakin murmushi me sauti, tarihin da ba'a karasa ba kenan ta gudu don ya hanata sukuni da kaifaffun idanunshi.
Chapter 41 · 0% Book details