← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 74

Sashe 4

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Habiba da Zulai da itama ta É—aga labule tana jin Abunda suke faÉ—a suka kwashe da dariya.

Fita Hidayat kawai tayi ba tare da tace musu komai ba, bata san me ta tare musu ba ita rayuwar da take ciki ma kaÉ—ai ya ishe ta, yadda suke mata ko tsakaninsu da suka HaÉ—a miji basa yi se da ita.

Asabe ta kallesu tace
"wlh bakwa kyautawa abunda kuke yi, baiwar Allahn nan tana fama da lalura ga wahalar rayuwa Dukda haka bata fasa baku girmanku na maƙota kuma ƴan uwa a musulunci ba, amma kun kafa mata karan zuƙa..."

Katse ta Zulai tayi wacce ita ce uwargidan su tace
"mu ji duka kan mu san kina yi Asabe"

Habiba tace
"Ah to!"

Daga haka bata sake magana ba ta cigaba da abunda take yi, waye be san irin rayuwar da hidayat ke yi a gidanta ba! Waye be san irin kaddararen miji da Allah ya HaÉ—ata dashi ba! Ko basu tausaya mata don komai ba sa tausaya mata sbd cikin dake jikinta da kuma kankantan shekarunta cikin Kab matan da suke layin.

Hidayat kam na fita bata tsaya sake shawara ba ta taka zuwa bakin titi ta tsare machine suka yi ciniki ta hau se hadeija road, anan ta saro gawayinta se sauri take sbd magrib da ya karato gashi yaranta na gida su kaɗai, rokan me machine ɗin tayi ya kawo ta har kofan Gida Albarkar abun cikinta ya amince, anan ya dire mata buhun gawayin hannunta rike da leda wadda cikinshi ledoji yellow masu zanen baƙi ne ciki na kulla gawayin.

Almajirai ta nema suka shigar mata ciki ta basu hamsin, da gudu Aisha ta zo ta karɓi ledan tana mata sannu da zuwa.

Usman da ya samu karfin jiki ya kawo mata ruwa, murmushi tayi ta karɓa tana godiya duk halin da take ciki idan har zata zauna ko da na seconds da yaran nan nata se taji zuciyarta yayi haske, kaunar da suke mata ya samo asali ne daga tsananin tausayinta da suke ji, duk kankantar shekarunsu sun san duk abubuwan dake wakana a rayuwarsu, ita kuma burinta shine rayuwar su ta inganta, bata son ganin sun yi kukan wani abu bata taɓa Barinsu da damuwa ko da kuwa ita cikin ranta dankare yake da damuwar.

Hakin dake yawan damunta tai tayi Dukda ruwan da ta sha sede be dena ba, da kyar ta samu ya lafa ta kalli Aisha tace
"shatu! Ki shiga Gidajen maƙotan mun nan ki faffaɗa musu muna saida gawayi kin ji? Kar fa kiyi nisa iyakacin layin nan kinga magrib ya gabato"

Kai Aisha ta gyaÉ—a kan ta fice da gudu.

Seda aka fara kiraye kirayen sallah kan ta dawo tana bata labarin waenda suka yaɓa mata magana da waenda suka amshe ta suka ce se sun zo saya da waenda ko kallon arziki ba'a mata ba da waenda masu gadi suka koro ta daga kofar gidan.

Tana ta murmushi kawai tana matse kafafunta da suka kumbura, Seda suka saki kan ta mike tayi alwala suka gabatar da sallarsu a tare, anan suka zauna suka yi azkar don duk rintsi bata barin su su kwanta ba tare da sun yi azkar ba haka bayan sallar asuba, karatu suka ɗan yi na Qur'ani kan ta basu abincin da ta rage musu, yaran na da tsananin wayau hakan yasa basu ce mata komai ba sede fa duk wadda yayi loma ɗaya ze sa mata ɗaya idanunta cike da hawaye take karɓa har suka gama suka sha ruwa suka zo suka kwanta sbd basa fita ko ina daga magrib yayi, in sun yi isha kuma haka zasu kwanta suna hira tsakaninsu har bacci ya sace su hakan yasa yaran nata ke da tsananin kulafucinta wani irin shaƙuwa da kusanci ke tsakanin su.

***

Alhamdulillah Hidayat ta fara sana'ar gawayi kuma daidai gwargwado tana samun ciniki sbd kafin sati buhun ya ƙare ta samu napep ta je ta sayo buhu biyu ta cigaba da sana'ar ta sbd ita tun daga washegarin ranar da ta fara sana'ar gawayi bata sake saka Yusuf a ido ba tun kuma 1k da ya wurga mata.

Usman ya warke garas yanzu ya koma makarantarshi boko da Islamiyya, ita kanta ba yaran ba hankalinsu a kwance yake na rashin saka Yusuf É—in a idanu sbd a sake suke komai ba tsoro da kaffa kaffa.

Da ɗan cinikin ta ta fara tara wasu abubuwan da suke dole wurin haihuwa sbd tana da tabbacin ko yau ko gobe zata iya tashi da naƙuda don har ta ma wuce Edd ɗinta.

Yau haka kawai ta tashi da son ganin Abba, hakan yasa ta ajiye duk wani fargabarta da tsoron ta ta shirya cikin kodaddun kayan ta da hijab ɗinta da yayi fari fat sbd koɗewa ta fita ta hau achaɓa, cikin sanyin murya ta faɗa mishi unguwar da ze kaita cikin mintuna kasa da talatin suka isa ta sallameshi gabanta na faɗuwa ta shiga gate ɗin gidan.

Allah ya taimake ta bata gamu da kowa a wakeken tsakar gidan ba har ta isa sashen Abba, da sallama ta shiga uwar É—akin se suka HaÉ—a idanu da dattijon a take ta saki murmushi shima fuskanshi a take ta washe baya iya magana amma a cikin idanunshi ta karancin murnar ganinta da yayi, babu abunda ya raba shi da Yusuf se tsufa da ze nuna mishi.

Da sauri ta karasa gabanshi ta duƙa tace
"sannu Abbana!"

Kallon cikinta yake yi, hakan yasa ta miƙe tana fahimtar so yake ya hanata duƙawar sbd cikinta tana murmushi tace
"ya jiki Abba? Allah ubangiji ya baka lafiya yasa kaffara ne wannan ciwon"

Idanu ya lumshe, yana me kallonta tace
"Abba su Aisha na gaisheka duk suna lafiya sun je islamiyya ne yasa ban taho dasu ba"

Sake lumshe ido yayi ya buÉ—e tace
"Abba ka sha maganin ranar ka kuwa? Abba ya kake zaune kai kaÉ—ai?"

Bata jira Cewarshi ba ta gyara ƙimar ɗinta ta taimaka mishi ya zauna da taimakon Allah ta mayar dashi kan kujerar shi na turawa wato wheel chair sbd ganin rashin tsabtar ɗakin da take, ta turo shi varender inda yake shan iska, komawa tayi ciki ta fara da wanke bayi, ta gyara bedroom ɗin zuwa parlorn Kal Kal ta saka room fresheners dake ɗakin ta ɗan kara Ac sbd zafin da garin ya ɗauka yanayi ne da damina ke dab da sauka hakan yasa a kullum zafin ke kara yawaita.

Bayan ta gama ta miƙe da kyar sbd bayanta da ya kage ta koma ta turo shi suka dawo, kunun da ta samu a flask ta tsiyaya ta bashi da spoon dukda rabi ke shiga rabi na zuba haka ta bashi ta goge inda ya ɓaci a jikinshi, nan ta zauna kasan kafan shi ta miƙe kafa tana ta bashi labarai tana murmushi.

Hidayat is a strong girl/woman he has ever seen a rayuwarshi, lumshe ido yake yana me mata Adu'a a zuciyarshi Allah ya gani ya bata Yusuf ne da tunanin ze riƙeta amana ya kula da maraicinta be san ganganci yayi ba seda lokaci ya kure, ba yadda ze yi ne yake ganinta cikin wannan kangi na rayuwa, a kullum ya kan roki Allah lafiya ne sbd ya samu ya kwatar mata hakkinta.

Yarinya ce da ta tashi cikin wahala ta Rayu cikin wahala tayi aure cikin wahala, she deserves a better life, natsuwa, hankali, ilimi da kyau Duka tana dashi why life choose to be so rude to her? She's so jovial faram faram ce da matukar wuya ka fahimci damuwarta.

Duba yanzu kaman ba shi ya haifi iyalin da suke gasa mata aya a tafin hannu ba, duk ranar da ta zo wurinshi ya kan tsinci kanshi cikin farin ciki sbd yadda zata zage ta bashi kulawa tayi making time ɗin lively da hirarrakinta ta tsabtace mishi muhalli wadda matar da yake aure kuma uwar Yayanshi bata mishi ba, duk cikin yaranshi babu me tsayawa yi mishi wannan hidima se me aiki, be taɓa sanin wani lokacin kuɗi kan zama masifa da bala'i ba seda wannan kaddarar ta same shi, da shi ɗin talaka ne, da lokacin neman kuɗinshi be shiga lokacin iyalinshi ba da ya dasa shakuwa da tausayi a zuƙatarsu, ya kan ga laifukanshi a kaso mafi yawa cikin abubuwan da suka faru da rayuwarshi kuma yana ɗaukan darasi in ya mutu falillahil hamd idan kuma yana da rabon lafiya ze yi iya kokarinshi wurin ganin ya gyara.

"ABBA..!"
Hidayat ta kirashi tana waving hannunta fuskanta cike da shagwaɓa wadda ya fidda asalin ainihin kananun shekarunta tace
"ko Hirar bata maka daaÉ—i ne naga idanunka sun sauya kala?"

Idanun ya zuba mata se ya lumshe su alamun a'a, tace
"in cigaba?"

Ya sake lumshe mata idanu, idanunta ne suka sauka kan agogo ta wara ido yaran suna gab da dawowa bazata so su dawo su tarar bata nan ba, mikewa tayi tace
"Abba zan tafi zaka kwanta?"

Ya lumshe mata idanu sau biyu alamun a'a sbd ya gaji da kwanciyar, hannunshi yake ta motsawa wadda yatsu biyu ke iya É—aguwa hakan yasa ta fahimci magana yake son mata, kallon inda yake kallo da kokarin pointing tayi taga bedside drawer É—inshi ne ta kalleshi tace
"A'a Abba ina da kuÉ—in machine"

Haɗe fuska yayi yaki kallonta hakan yasa ta fahimci fushi yayi, se ta taka zuwa wurin ta buɗe tare da sa hannunta akan kuɗin zata zare 1k kenan aka turo kofan, karab idanunsu suka haɗe wadda ya haddasa mata mummunar faɗuwar gaba da sauri ta miƙe sbd Kab duniya babu wacce take kallonta taji hanjin cikinta ya kaɗa irin umma, ta gana mata azabar da ko sunan umma taji an kira se gabanta ya faɗi.

"La'ila ha'illallahu Muhammadur rasu lillahi salla lahu alaihi wa sallama... Sata? Hidaya abunda kika koma Kenan? Ɓarauniya..!"

#like
#share
#comment

                   🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 4*

*FREE BOOK*
Chapter 4 · 0% Book details