← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 74

Sashe 58

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi me tafe da ciwo tayi tace
"Abba gwara kayi bacci ka huta in Allah ya kaimu gobe se in baka labarin don in har na baka yanzu bazaka iya bacci ba"

Shiru yayi na mintuna kan yace
"mahaifiyarki mutumiyar kirki ce, har Abada zan cigaba da kewar macen arziki mar'atussaliha irin ta..!"

Murmushi kawai tayi a hankali yake bata labarin wacece mahaifiyarta se ta fahimci a halayyar su kaÉ—an ne kawai suka sha bambam amma kusan duka halayyar su iri É—aya ne, yadda yake murmushi me ciwo zaka san kwarai ya so mahaifiyarta kuma yayi kewar ta.

****

Kusan a tare da Daadida suka shiga ɗakin sede shi daga bakin kofa ya ja ya tsaya yana kallon Baba Buba, yadda ya zama bazaka taɓa cewa shine Buban chan ba, Buba me son tarin abin duniya, Buba marar mutunci duk ya kwanjame baki a karkace, rabin jikinshi a mokaɗe.

"Buba!"
Daadida ta kira sunanshi da tarin mamaki don bata taɓa zaton jikin ya kai haka ba.

"Buba baka samun kulawa ne? Baka cin abinci ne? Innalillahi wainna ilahi rajiun"
Ta faÉ—a hawaye na zubo mata, lokaci É—aya shima ya fara zub da hawaye me ciwo idanunshi na kan Raed dake tsaye daga bakin kofa ya kau da kai sbd hana hawayen idanunshi zuba.

Ko yayi magana ba ji za'a yi ba in ya nace kuma shi yake shan azabar ciwon.

Hannu kawai ya sa ya kama na Daadida yana zub da hawaye.

Raed da kafafunshi suka gaza É—aukan shi ya juya ze fita se Buba yayi karfin hali fusgo sunanshi..

"Muhammad!"

Chak ya tsaya se ya juyo yana kallon shi.

Baki a karkace cikin taune harshe yake maimaita
"ka yafe min don Allah! Ka yafemin!"
Yana kuka sossai.

Da sauri Raed ya zo ya riƙe hannunshi Ɗayan yana zub da hawaye yace
"Na yafe maka baba, ka dena kukan nan ka samu lafiya ka ji?"

Yace
"ni kaÉ—ai na san azabar da nake ciki Muhammad! Ni da lafiya kuma har Abada, na zalunceku na raba abunda Allah yafi so Wato zumunci na cuci kaina na cuci rayuwata...."

Tarin da ya fara me yawa ne yasa Raed danna red button se ga Dr da nurses.

Dr yace
"am sorry please wani irin Nutrition kuka É—aura shi a kai? His condition is very bad am sorry to say!"

Yace
"ban gane ba? Is it about the paralyze or something else?"

Dr yace
"I don't really know me aka bashi we are not sure but rabin hanjinshi ya ruɓa, a hoton da muka yi ya nuna mana an yi aiki an yanke sede ba'a yi replacing ba so he keep suffering yanzu dole se mun sake aiki! Please karku bashi ko ruwa ne har nan da 5 days muga yadda aikin ze kasance"

"innalillahi wainna ilahi rajiun!!"

Daadida ta faÉ—i tana dafe baki, tace
"duk yaushe aka yi haka Buba? Ina kudaden da nake aika maka na abinci da magani? Me hakan ke nufi Buba? Innalillahi wainna ilahi rajiun"

Raed É—auke idanu yayi yana maida hawayen ciki, yace
"I think we are leaving to another country"

Dr yace
"duk abu É—aya ne sir, muna da duk wani kayan aikin da zaka same shi a kasashen waje haka likitocin mu zasu yi mishi aiki fiye da na Kasar waje kwanciyar hankalinku muke bukata da nashi, in shaa Allah ze samu lafiya sede yanzu yana jin jiki"

Kai suka gyaÉ—a Raed dae was not convinced, asibitin kam ya amsa sunanshi sede hankalinshi be kwanta ba.

Babu wadda ake bari ya kwana, wuraren karfe É—aya Hidayat ta zo ta duba baba Buba itama Seda tayi kwalla, lallai kaji tsoron rayuwa. Yanzu wannan alhaki dake dawainiya da wannan bawan Allah in tace bata yafe mai Bama ai ba zuciya a kirjinta itama kaman shi a baya.

Haka suka bar asibitin cikin alhini me girma, Raed bayan ya sauke su gidanshi ya wuce duk se ta damu don kallo ɗaya zaka mishi ka san ganin Baba Buba ya taɓa shi ko min lalacewar uba ubane tabbas.

#Vote
#share
#comment

                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 38*

*FREE BOOK*

Bata iya ta runtsa ba seda ta tabbatar da yayi bacci, ta kashe lokaci sossai tana kwantar mai da hankali a wayan har ta dena jin amsar shi, mikewa tayi ta watso ruwa ta zo tayi nafila tana me rokarwa mahaifinta lafiya tana kuma Rokon Allah yaji kan mahaifiyarta.

Washegari da wuri ta tashi da kanta tayi breakfast ta HaÉ—awa Abbanta ma breakfast wadda ze ji daaÉ—in shi, bayan ta gama taje tayi wanka a lokacin su Norah ma sun yi wanka suna tambayar ta ina taje jiya har suka yi bacci bata dawo ba?

Tace musu
"Dad É—ina ne be da lafiya I have to be there through out"

Aisha tace tana so ta ganshi, tace su shirya su je duka tare.

Bayan sun fito ta shiga wurin Daadida suka gaisa kan ta Haɗa mata breakfast ɗinta nan kan dardumanta don bata iya zaman dining wai na yara ne gwiwowinta se su sage, Albarka ta sa mata kan ta miƙe ta fito, tana rufe kofan yana rufo na parlor.

Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, a tare suka sakarwa juna tattausan murmushi, kallonta yake daga sama zuwa ƙasa, sossai tayi kyau cikin Rigan lace da aka mishi ɗinkin manya, ya haɗu karshe ya kuma bi jikinta kasancewarshi milk da emerald green.. Ɗan kunnen kunnenta fashion marar girma ne emerald green se sarkan mamanta na gold dake wuyanta.

Shi kam as usual sanye yake da kananun kaya designers wando da riga black and ash, hannayenshi zube cikin aljihu, a hankali ya ciro su tare da warawa yana kallon idanunta, zare cute eyes ɗinta tayi kan ta make kafaɗa tana kallon kofan daakin Daadida, baki ya taɓe kan ya fara takowa zuwa gareta yana sakin murmushi ganin yadda ta sunne kanta kasa, shi kam ko a jikinshi ya rungumeta suka sauke ajiyar zuciya a tare.

Peck yayi mata a goshi yace
"Good morning Die hard!"

Tana motsa hannunta dake sanye cikin nashi tace
"morning paapi, hope ka tashi lafiya?"

Kai ya gyaɗa yana lumshe idanu sbd kamshinta dake aika mishi da saƙo yadda ya kamata, tace
"mu je kayi breakfast"

Ya kalli hannunta dake riƙe cikin nashi farare sol kyawawa a gyare tsab yace
"u rejected my proposal yanzu hannunki yayi somehow without a ring"

Murmushi tayi tana jan hannun nashi zuwa dining tace
"wani proposal kuma bayan na zama matar aure gabaÉ—aya, but that ring yana da kyau sossai fa!"

Yace
"I changed it with another one in mun koma zaki gani, baby gurl we are leaving together today right?"

Zata yi magana yaran da suka kalli baban nasu yanzu suka fara gaida shi, Junior har da saukowa ya zo wurinshi, É—aga shi yayi ya cilla sama suna dariya suka zauna, da kanta tayi serving nashi ta HaÉ—a mai tea ta tura mishi gabanshi, itama ta zuba nata don already yaran sun yi nisa a ci.

Yana yin loma É—aya ya lumshe idanu yace
"you cooked?"

Murmushi kawai tayi, yace
"kin san wani abu?"

Ta girgiza kai tana Kallonshi, yace
"from the first time I tasted ur cook taste ɗinshi be ƙara barina na huta ba, I always longed to eat ur cooking u r really a great Cooker! Thank God"

Yadda ya karashe har yana ɗaga hannu sama ne ya sakata sakin dariya, ƙasa ƙasa yake maganan ko yaran ba jin abunda suke faɗa suke ba.

Cigaba da cin abincinta tayi wani sashe na zuciyarta na tuna mata Yusuf, zata gama wahalar yi mishi girki da mutanenshi babu sannu bare na gode, bare kuma a zo maganan yabawa, ta zauna da monster ne kawai as a husband.

Har suka gama ci suka tashi Tabawa ta zo ta tattare babu wadda ya sake magana. Abincin asibiti aka kai motanshi se ga Daadida ta fito a tare suka tarkata duka suka yi asibitin.

ÆŠakin da Abba yake suka fara shiga, yana kishingiÉ—e hannunshi rike da chasbi yana ja, gabanshi wani farin dattijo ne zaune suna magana, shigowansu ya fadada fara'arshi yana musu sannu da zuwa.

Hidayat dake murmushi ta karasa ta ajiye basket ɗin hannunta kan ta duƙa ta gaida dattijon, ya amsa yana kallonta da murmushi ta juya ta gaida Abbanta da suka gama Gaisawa da Raed, shima ya amsa yana tambayar ta gajiyar jiya, murmushi kawai tayi

"masha Allah, duka waennan jikoki nane?"

Daadida na murmushi tace
"wannan da wannan sune yaran wajen Hidayat babban ya rasu, su biyun nan kuma yaran Raed ne mahaifiyarsu ta rasu duk suna wurin Hidaya yanzu!"

Yace
"masha Allah tabarakallah! Ga mata kam sababbi fil a Leda se wadda na zaɓa, kai kam bana yi da kai..."

Yayi maganan yana kallon Junior, se ya koma ya kama hannun Raed yana Kallonshi fuska a kwaɓe, duk dariya suka yi, Norah da Farrah suka gaida shi yayinda Aisha taje ta kama hannunshi tana Kallonshi tace

"Mommy kin ce Abban ki! Wannan kuma ai ba Abbanki bane na gidan umma...ba kin ce ya tafi kenan ba ze dawo ba? Ko in an mutu ana dawowa? Yaya Usman ma ze dawo?"
Duk ta jero tambayoyin tana kallon hidayat.

Rasa amsar bata hidayat tayi se ta kau da kai hawaye na cika mata idanu, kwarai itama tana matukar kewar Usman da Abba sede ta kan musuAdu'a Allah ya gafarta musu yasa sun huta, Abba ne yace

"Aisha da gaske ne duk wadda ya mutu baze dawo ba! Wanchan ma Abbanta ne kin san mommynki princess ce tana  da Abba's dayawa dayawa"
Ya karashe yana shafa kan yarinyar, cikin mamakin yadda hidayat ta sawa É—an ta na fari suna Usman don ya san bata san shi ba! Har gwara Aisha ma ze iya cewa zata san sunan mahaifiyarta ne.
Chapter 58 · 0% Book details