← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 74

Sashe 53

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dab miqat suka tsaya suka yi duk abunda ya dace suka yi nafila raka'a bibbiyu tare da É—aura niyyar yin Umura, ko da suka isa masauki be bari ta kalli gaze na ka'aba ba don hotel É—insu daga window É—in É—akunan kana kallon ka'aba tarrrr.

Seda suka ajiye loggage É—insu kan suka fito zuwa masallaci, tana sa kafafunta a harabar masallacin ta lumshe idanunta tana jin wani ni'ima da sanyi, a hankali ya karaso kusa da ita ya sanya hannunshi cikin nata yace cikin raÉ—a

"lower ur gaze"
Bin umarnin shi tayi bata É—ago ba seda suka iso mataf area inda anan ake dawafi, hannunta ya sake shigarwa cikin nashi yana massaging a hankali yace
"are you ready?"

Kai ta gyaÉ—a mishi yace
"ok lift ur gaze to set sight on the beutific vision of the holy ka'aba!"
Yayi maganan dab kunnenta..

A hankali ta fara ɗagowa har ta ɗago gabaɗaya idanunta suka sauka bisa ɗakin Allah, kuka take yi da sauri ta ɗaga hannunta with the utmost concentration and sincerity as nan ɗin waje ne da Adu'a ke karbuwa seda ta fara yiwa annabi salati sbd duk Adu'ar da zaka yi ze tsaya ne tsakanin sama da ƙasa idan har baka cike ta da salatin annabi ba hadisi ne ingantacce.

Rashida da Daadida tare da yaran duk sun wuce sun kyale su su biyun su, a tare suka yi performing Umura É—insu matsayin mata da miji, wadda dumbin musulmai da mala'iku suka sheda, tunda ya zo a hadisi cewa ko wani rana mala'iku dubu saba'in suke sauka a Saudi don aiwatar da Umura, suna rike da hannun juna suka yi dawafi suka yi raka'a biyu a kusa da maqama Ibrahim, suka yi sa'i a safa da marwa abu na karshe suka rage gashin su ita inch É—aya da karamar scizors, umurarsu ta cika.

Gida suka koma suka huta gajiya inda se dare suka zo suka yi magrib da isha anan masallacin, tayi Adu'a sossai ta roki Allah ya bayyana mata zuri'arta karo na farko a rayuwarta, ta roki Allah ya ji kan Abba, ta roki Allah ya bata zaman lafiya da zuri'a dayyaba a gidan aurenta, ta roki Allah ya kare mata mijinta ya raba shi da sharrin mutum da aljan ya sada shi da halal ya nesanta shi da haram, ta roki ubangiji ya raya musu yaransu, da yakinin Allah ze amsa tunda shi É—in maji rokon bayin sa ne..

Kwana biyu suka kara a Makkah sallar farillah ko ɗaya bata taɓa yarda tayi a ɗaki ba, kaman kar su bar Makkah sbd gari ne da zaka ji baka son nesa da ita, barin ma ɗakin Allah har tsakiyar ruhinta take jin aminta da natsuwa a duk sadda zata ɗaura hannunta bisa ɗakin na Allah, jeddah suka dawo da pjet ɗinshi suka yi Nigeria inda suka barshi a baya don ze karasa Riyadh ya gama signing contract ɗinshi.

Se gata a Aminu Kano international Airport bayan shekara da watanni da barin ta Nijeria, ta tafi cikin zullumi da kokonto, ta tafi cikin rashin cikakken wayewa da shakku, ta tafi a matsayin Æ´ar aiki se gashi ta dawo a matsayin cikakkiyar matar aure, ta dawo zuciyarta cike da farin ciki da soyayya, ta dawo da ilimi, natsuwa, da kuma nagarta. numfashi me karfi ta ja ta sauke kan ta gyara zaman sun glasses É—inta, Rashida bata bisu ba sbd an zo daukarta daga gidansu inda driver É—in Daadida ya dibesu zuwa gidanta.

Ɗaki na musamman Daadida ta sauke ta ita kaɗai, tayi kiran waya cikin awa biyu se ga wata mata ta zo da akwati jibgege, itama ta sauka a ɗakin na Hidayat daga ganinta kaga cikakkiyar shuwa Arab  amma half kanuri ce, a ranar aka fara yi mata gyara ingantacciya.

Sam bata hau online ba tunda suka isa madina se yau, ga mamakin ta É—aurin aurensu har yanzu yana wani irin trending a kafafun sadarwa duk inda ta shiga hoton Raed ne sanye da jallabiya fara sol da hirami ya mata dauri irin na Larabawa fuskanshi cike da tsantsar annashuwa yana Gaisawa da mutane, dukda security suna kare shi sbd gudun wani matsala, amma kusan duk wadda yake wurin kuma yake da Burin ko da Kallonshi ne seda yayiwa musabaha.

Adu'o'i kam har Seda ta zub da hawaye, al'ummar musulmi sun masu fatan alkhairi, lallai Raed na da masoya a duniya inda ta ci albarkacin shi, Sam basu yi hoto a Makkah ba amma ga mamakin ta se ga wani hoton su ta gani a media, hannayensu cikin na juna yana sanye da Fararen ihram ita kuma sanye da baƙar Abaya magana yake mata ita kuma tana Kallonshi tana murmushi hakwaranta a waje, ba karamin kyau hoton yayi ba, shiga tayi tayi saving, da sauri ta kashe datar ta janyo ciccibi da ta dahu da itacuwa masu kyau da wani sirri ta fara ci sbd jin motsin mata me gyaran jikin.

****

A hankali baƙar GLS tayi parking a kofar gidan, Seda aka dau mintuna kan driver ya sauko ya zagayo da gudu ya buɗe seat ɗin baya, a hankali ya sako kafafunshi waje rike da sanda wadda tafi yanayi da na sarauta, takawa yake a hankali zuwa kofar gidan.

Drivern ya karaso yace
"ko za'a yi mana iso tukuna?"

Kai ya girgiza cikin kamilalliyar muryarshi yace
"ka yi sallama matan su gyara"

Wucewa isa yayi cikin minti biyu ya dawo yace su karasa.

A hankali suka nufi cikin gidan, aka yi musu jagora zuwa ɗakin... Da mamaki ya sanya kanshi cikin ɗakin, se suka yi tozali da mutumin da ko a mafarki be taɓa kawo ze sake ganinshi ba bare a zahiri, Idanu suka zubawa juna suna kallon kallo......

#Vote
#share
#comment

                 🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 35*

*FREE BOOK*

***Alhamdulillah! Ina matukar godiya da irin kulawar ku a gareni waenda suka kirani, waenda suka min SMS, waenda suka min saƙo ta what'sapp da ma masu min fatan samun lafiya a cikin groups Na gode sossai ALLAH ubangiji ya saka muku da gidan Aljanna, Allah ya bar zumunci.. Waenda basu sani ba kuma har sukan tambaya Bani da lafiya ne har yanzu kuma ina kan samun sauƙi ne, akallah na sha 12 bags of drip. Ciwo yake zuwa farar ɗaya saukin se a hankali... Ku cigaba da sani cikin Adu'o'inku Allah ya bamu duka lafiya me anfani🥰🙏***

**Wannan shafin sadaukarwa ce gareku daukacin masoyana❤️❤️**

%%%%

Wani irin kakkarwa jikinshi ya ɗauka kaman ana buga mishi gangi a firgice a kuma razane yana kokarin miƙewa sede saɓanin hakan kifewa yayi yana me cigaba da son yin magana jikinshi babu inda baya rawa..

Da sauri mutumin ya durkusa gabanshi yace
"calm down Yaya buba, nine dae Usman ba wani ba... Me ya sameka kake cikin wannan mawuyacin halin kai kaÉ—ai? Ina Mama? Ina Aisha da abunda ke cikinta?"

Ai kakkafewa idanun buba suka fara lallai lallai yana son yin magana sede ya kasa se hawaye sharrrr suke zubowa, da kyar ya iya fito da Kalmar
"Ina Aisha?"

Usman yace
"ban gane ba yaya buba?"

Badi'ah dake makale jikin kofa tace
"Hmmm ai Alhaji bana manta irin cin kashin da buba yayiwa Aisha da abunda ke cikinta korar kare shekaru da dama, korar da yayi sanadiyar tsananin fushin mahaifiyarshi gareshi wadda ba tantama sanadiyar shiganshi wannan hali kenan muma gashi muna fama babu cin yau bare na gobe"

Dabas haka Alhaji Usman ya zube gumi na tsatsafo mishi ko ta ina, idanunshi suka rine a take suka juye zuwa wani abu daban jikinshi har rawa rawa yake....

"Ya Buba! Innalillahi wainna ilahi rajiun..! Innalillahi wainna ilahi rajiun!! Ka kori Aisha da abunda ke cikinta??? Aishar tawa?? Aisha fa??" Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan.

Isa ne ya zo ya riƙe shi yace
"Alhaji kayi haƙuri a bi komai a sannu kaga kaima ba isashiyar lafiya ne da kai ba gashi babu wadda ya san kayi wannan doguwar tafiyar kar wani abu ya zo ya sameka..."

Hanky fari Kal dake tashin kamshi ya ciro ya share fuskanshi kan ya miƙe da taimakon Isa, ya kalli Badi'ah yace
"Ina mama? Karki ce min ta rasu don Allah"

Tace
"tana nan tana jin daaÉ—in rayuwar duniya ina mutuwa yanzu"
Isa yace a zuciyarshi 'ji jahilci'

"Address É—in ta zaki bani"
Usman ya faÉ—a cikin wani irin mawuyacin hali.

Tace
"nima ban san wani Adara ba shi buba kaÉ—ai ya san wurin"
Tana kai nan ta juya ta wuce ta san yau Alhaji Usman se ya daure buba har igiya tayi saura..

Kallon kwantaccen buba dake ta kuka Alhj Usman yayi, cikin tausayawa Dukda ƙasan zuciyarshi akwai daci da raɗaɗin abunda Buban ya mishi wadda har Abada baze gogu ba idan ba Hasken idaniyarshi ya gani ba sede yace

"Yaya Buba zaka iya bamu kwatancen gidan Mama?"

Da hannun dake É—an aiki ya iya pointing wani Rigan shi, isa ya karasa ya ciro ya duba aljihun akwai paper É—auke da address É—in.

Yace
"gashi yallaɓai, bamu da nisa ma ashe"

Karɓa yayi ya duba kan ya sa a aljihu yace
"Isa ba zan iya barin shi haka ba, zaka iya É—aukar shi ka sa shi a mota?"

Isa na dariya yace
"ai yadda ya zama kuÉ—in guzurin nan ko Kano se in je dashi a É—auke..."

Girgiza kai Alhaji yayi yace
"careful Isa"

"sorry sir!"
Isa ya saramai, dukda yadda yake jinshi cikin tashin hankali da damuwa hakan be hana shi murmushi ba, Isa drivernshi ne na tun hankali na kwance tun be yi makaranta ba har yayi diploma a karkashin shi sbd shi mutum ne da duk na kasan shi ke jin daadinshi, baya taɓa bambance talaka da mai kuɗi a tsarin rayuwarshi kowa nashi ne.
Chapter 53 · 0% Book details