Sashe 37
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Eh hajiya, amma don Allah ki fahimce ni ba wai don cutar da zainab nake son shigo da Hidayat rayuwata ba, son ta ya samo asali ne daga tausayinta in bazaki manta ba a shekaru da dama su Abba ƙarami sun je nema min aurenta har sau uku a wurin marikinta.." Ya faɗa yana kallon Hajiyar cikin son tunatar da ita hidayat.
"Eh kwarai na gane, wacce ka ce tana zaune ne wurin marikinta kuma bata jin daaÉ—in rayuwar gidan, daga karshe kuma aka aura mata É—an gidan ko?"
Ta faÉ—a tana mishi wani kallo.
Yace
"eh hajiya!"
Cikin tsananin masifa ta fara magana
"ban gane eh ba? Kana nufin ita zaka sake tura mahaifanka a tozarta su kaman yadda aka yi a baya? Marar tushe da asalin? Wacce dama tun a wanchan lokacin karfin ikon me mazari ne(kakanshi na wurin uba) yasa na zuba muku ido, Ko kana so ka ce zainab bata wadace ka as mace ba da har bata shekara ba kake maganan yayibo wani aure?"
"Hajiya uban goyon ta ya rasu, bata da kowa se Allah don Allah karki hanani aurenta"
Ya faɗa cikin roƙo.
"Dakata ma tukuna! Yanzu a Paris É—in wurin wa take zaune?"
"Hajiya tana aiki ne na kula da yara waenda suka rasa mahaifiyarsu shine baban ya É—auke ta aiki kuma tana karatu" ya faÉ—a da iyakar gaskiyar shi.
Wata doguwar salati hajiya ta ja ta sallame nan fa ta fara balbale shi da masifa akan wallahi ba'a zuri'ar ta ba, Æ´ar bariki dake zaman kanta Inaaa..
Duk yadda ya so ya fahimtar da ita ta kasa fahimta, Hajiya irin manyan matan nan ne en duniya waenda duniya kuma tayiwa daaɗi, bata da mutunci ko na sule biyar bata san wani abu wai shi kawaici ko kunya ba, bata da kirki in ka taɓa ta kaman yadda girman kai da izzarta ba ze bari ta rabi kowa ba barin ma idan talaka ne, shi kuwa yana jin ba ze iya rayuwa babu hidayat ba.
Daga karshe korarshi tayi, ɗakin Abban shi ya nufa ya same shi kwance jiya e yau, rufe yake da blanket fari, hancinshi abun oxygen ne ba uhm ba um um kuma yayi shekaru da dama a haka, idan jikin yayi tsanani se an saka mishi oxygen da abun abinci ta baki amma idan da sauƙi ya kan yi numfashi.
Hannunshi hamza ya riƙe ya ɗaura fuskanshi a kai se hawaye, yana son hidayat son da be sani ba seda hajiya ta fara nuna mishi turjiya akan aurenta, kaman fa baze iya rayuwa ba tare da Hidayat ba, kwarai in hajiya ta raba shi da ita kwananshi kirgaggu ne a duniya.
****
Tafiya yake kaman sabon kamun hauka wurjanjan, riga daban wando daban na yaÉ—i kodadde wadda ake kira wanke kuÉ—in ka, kayan da da in ya gani jikin Usman yake kyarar shi saboda kyamkyami se gashi yau na Usman ma yafi nashi kyaun tsabta da sabunta.
Daga kafaɗun a yayyage yayi baƙi gabaɗaya ya koɗe kaman ba Yusuf ɗan kwalisa ba, buhun karshe na dako da yake yanzu ya kai ya karɓi Naira ɗari ɗaya da aka bashi yana juyata..
Me ɗari zata mishi? Ba Wa shi kaɗai ba harda familyn shi da suke gida suke jiran ya kawo? Ba ga matarshi da yake ji kaman ya mata sujada ba, ba ga mahaifiyar shi da ƙannenshi ba.
Hanyar gidan ya kamo a rikicenshi in ya ga yaro tsaran Usman se ya ruga da gudu ya kama shi
"Usman! Usman!! Baka mutu ba ko? Yauwa zo muje gida ba zan kara dukan mamanka ba don Allah ka barni in sarara"
Wani lokacin idan abun ya Motso se an yi da gaske ake kwace yaro a hannunshi se yace Sam Usman ne ze kaiwa Hidayat shi saboda ya dena zuwar mishi a mafarki da zahiri.
Gida ne na laka cikin wata kwaraɓaɓɓiyar unguwa da kwata shine abu mafi rinjaye da yayiwa anguwan ƙawanya, kudaje kuma suka zama ma'abotan huldarsu, kutsa kai yayi ba tare da ya damu da yayi sallama ba.
Zaune yaga Kausar wacce itama ta zama wata jagwal, tana HaÉ—a abubuwan da take anfani dashi wurin toya doyanta na yamma..
Harara ya zabga mata ba wata wata itama ta rama.
"Ni kike Harara?"
"An harare ka ɗin, in ban harare ka ba wa kake so na harara? Wallahi in na ganka wani baƙin ciki da takaici nake ji kaman in kashe kaina, in banda wawanci irin naka da daƙiƙanci taya da degreen ka za'a damfare ka kudadenmu? Gashi ka mana sanadiyar baƙin talaucin da babu ranar fita daga cikinta.."
Yace yana harzukowa
"eh ai gwara ni da degree na ke fa? A sadda ake neman kiyi karatun ƙi kiyayi kika ce aure gashi yanzu uwar miji ta sakoki ba Chas ba ass se tallar doya"
"ahayyeee ai gwara ni ban zama malohuwa sokuwa ba, mace nake kuma ina amsa sunana wasu mazan da suka koma mata fa? Kai da kayi degreen da me ya anfana maka? Gaka nan marabinka da mahaukaci bin bola...!"
Ta kare tana buga kafa kasa cike da masifa, tsabar rama da talauci kana iya ganin ƙura na tashi in tayi wani jijjigan
"ni fa kun ishe ni Haba!"
Surayya dake fitowa daga fallen ɗakin dake gidan bayan wani me ciki da parlor ta faɗa tana saɓan mayafinta a kan igiya.. Tayi gaba
"yawon shashancin da aka saba, tsabar lalacewa ma wai a wurin masu shayi da layin ga ruwa ake ƙarewa"
Cewar Kausar again.
Surayya da har ta fita ta dawo tace
"ai gwara ni ina da abunda zan bayar É—in in wata ta isa tayi mana..."
Harzukowa Kausar tayi sede tuni Surayya ta fice, Zasu cigaba daga inda suka tsaya da Yusuf umma ta fito sanye da wasu riga da zani da suka ji jiki ta kare kaman ba umma ba, zata yi magana wata sangamemiyar mata ta fito daga daki me ciki da parlorn tace
"kai ya isheka hakanan! Ina cefenen da na ce karka dawo gidan nan babu shi?"
Sosa kai yayi cikin wani irin ladabi yace
"Wallahi wallahi ba aiki yau dako nayi kuma shima É—ari É—aya kawai na samo"
"kawo ka wuce ka koma...marar zuciya sususu"
Zuwa yayi ya miƙa mata ya juya ya fice.
Kallon tsakar gidan tayi tana kallon umma tace
"ya aka yi kwata kwata wurin ba'a kimtse ba?"
Umma tayi saurin cewa
"eh..eh dama yanzu ne za'a kimtsa..."
Fara tattare gidan tayi tana kallo Kausar ta gama HaÉ—a doyarta ta fita ko yanka É—aya bata bar mata ba gashi tun safe babu abunda ya shiga cikinta.
Tunanin rayuwa ta faÉ—a..
Ashe haka hidayat ke ji a sadda suke azabtar da rayuwarta? Wani irin sakayyah ce wannan me muni? Tun bayan da ƙasa ya rufe idanun Abba ibtila'i yake sauko musu abu na karshe da tayi nadama shine korar kare da tayiwa hidayat da ɗanyen jariri.
Yadda hidayat ta sa kafa ta tsallake kaman ta tafi ne da duk wani sauran rayuwar da suke lallaɓawan, garin wawancin yusuf ya zube dukiyar su duka hannun rikakkun ƴan 419
Sun sayar da Motoci har biyu wurin bin polisawa ko za'a samu clue dukiyar su ta dawo sede a banza.
Bayan tafiyan hidayat Yusuf ya haɗu da wata mata, tunda ta ganshi taji shi take so kuskuren shi daya shine zina da ya fara da ita wadda shine makasudin rayuwar da suke ciki yanzu, saboda ana rade raden cewa muddin ka kusanceta to zata mallake ka ne da abunda ke kewaye da kai har se in ita ta tafi da kanta amma baka isa guje mata ba.
A yadda yake a hauka hauka saboda kasa sukuni da mafarke mafarken Usman cikin mugun yanayi ta saka shi aurenta, ita ke tura shi ya sato abubuwa masu muhimmanci da su umma suna sayarwa kan umma ta farka wayam, kayan sawa ma be bari ba, karatun Surayya ya tsaya Chak hafiz ya ɓata ɓat kaman walkiya.
Har ta kai ta kawo gidan Abban ya fi karfinsu saboda suna zaune ne kaman a kango tunda gashi a cikin babban gida sede ba abinci, dalilin sayarwan kenan suka dawo suka saya wannan me saukin kuÉ—i a cikin irin wannan anguwa da da ko wucewa babu É—ayansu da ze iya yi.
Kausar ta gamu da sharrin uwar miji sanadiyar kaninshi da tayiwa ƙage akan ya neme ta wadda kashe ɗan uwanshi ne kawai mijintan be yi ba, daga nan uwar mijin ta sa mata karan zuƙa wata biyar tana gana mata kalolin matsaloli har asirin ta ya tonu kawai tana jin haushin cin arzikin ɗan uwanshi da yake yi ne, nan suka mata jina jina tayi tilis kan suka korota daga ita se kayan jikinta.
Daga karshe taje ta kwashe kayan ta sede a hankali suma aka sayar da komai chanjin ne har yanzu take Juyawa shima da tsiya tsiya.
Fahariyya kuwa mijinta aure yayi ya auro wacce ta maida ta bola, tana zaune ne kawai saboda tsoron irin rayuwar da ake a gidansu amma kwarai tana azabtuwa yadda ya kamata!
Matar Yusuf ba ginin da za'a taka a hau bace hakan yasa komai na gidan su suke yi, sau daya Kausar ta gwada Haɗa ƙashi da ita Seda aka mata ɗauri, har yusuf ɗin in ta ganshi yana kallon wata haka zata saka shi a gaba ta zane tsab! Har Seda ya fara dana sanin zina a rayuwar shi.
Gabaɗaya rayuwarsu ta taɓarɓare wadda a shekarun baya ko a mafarki basu taɓa Tunanin kasancewa cikin irin wannan rayuwa ba.
(Ni ko nace ai wadda ya ƙi Sharan masallaci dole ze yi na kasuwa!)
PARIS
Zaune take riƙe da waya a kunne
"Daadida! Don Allah ki kwantar da hankalinki a bi komai a sannu, a gaskiya taɓon da Baba bukar yayiwa rayuwar yallaɓai me matukar girma ne wadda bana Tunanin ze gogu sede watakila idan addininshi yayi zurfi zuciyar musulunci tasa ya iya gyara alakarshi da Mahaifinshi, karki manta ba iyaye bane kaɗai ke da hakki a kan yara, ƴaƴa ma suna da hakki a kan iyaye.. Mu yi ta Adu'a Allah ya dubi lamarin se kiga komai ya zo ya wuce"