← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 74

Sashe 38

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daadida ta share hawayen fuskanta tace
"bana so in mutu in bar su haka Hidayat, kullum ƙara tsufa nake rayuwar bukar ta riga ta gama taɓarɓarewa saboda abunda ni na san hakki ne...! Ciki harda laifi mafi girma shine na saɓawa iyaye, A hakan ma kullum ina rokar mishi gafara sede Allah babu ruwanshi abunda kayi shi za'a maka... Jiya ya bar nan cikin tashin hankali saboda wani mummunar faɗa da Badi'ah da Zara suka yi wadda yayi sanadiyar jefa ƴaƴan su rijiya, ya ce kullum gidanshi kaman gidan kaji ko na ƴan dambe, ko allura ya ajiye za'a nema a rasa saboda sata gashi har yau bayan Raed be da wani ɗa namiji... Yara mata ne cikinsu babu abunda babu, har da ƴar daba wacce yace tayi ikirarin yanka wuyanshi ya sake ɗaga mata murya gidanshi kuma dole ta shiga... Hidayat abunda ya ɗaure min kai har yanzu be yarda hakki ne ke binshi ba ya kasa neman yafiyata ya nemi albarka... Ya kasa neman ɗan shi ya nemi ɗauki wani irin azabtar da kai ne wannan?"

Hawaye hidayat ta share tace
"Ki cigaba da Adu'a da sadaka Daadida in shaa Allah komai ze yi sauƙi... Watakila Allah ne ya ɓatar dashi ya kuma mantar dashi Tunanin da ya kamata yayi wurin gyaran kuskuren shi saboda ya girbi abunda ya shuka, muyi fata Allah ya tsayar dashi iya haka"

Dukda hidayat bata taɓa ganin Daadida ba sede akwai wani shakuwa da ya shiga tsakaninsu ta waya, saboda matsaloli Raed Dukda har yanzu ba shiga harkar ta yake kaman da farko ba, iyakar su karatu wadda yana gamawa ze fice,  ya fi maida hankalinshi kan sana'arshi yana kuma azabtar da kanshi da motsa jiki a ko wani lokaci.

Sallama suka yi da Daadida tana sauke wayan hamza na kira.
ÆŠagawa tayi yace
"Hidayat da wa kike waya tun É—azu layinki busy?"

"Da grandmother É—in boss É—ina muna tattauna wani batu ne da ya shafe shi..!"
Ta faÉ—a kanta tsaye da iyakar gaskiyar ta.

A zafafe yace
"kina so ki kashe ni ne hidayat? Wallahi hangen kwanana nake kusa...! Rayuwata na shirin taɓarɓarewa na kiraki ko zan samu sanyi ta wurinki shine kike gayamin maganan wani boss?"

Dafe goshinta tayi tace
"ya ilahi! Ya Hamza wani furuci nayi da ze harzukaka haka? Tambaya ta kayi na kuma baka amsa.. Me ke faruwa ne?"

Runtse idanunshi yayi yace
"Hidayat hajiya ta ƙi tsayawa ta saurareni zainab ta rigani a wurinta, a sanina yadda hajiya ke so na a matsayin tilon ɗan ta komai nake so yi min take amma yanzu tana shirin juyamin baya"

"ya hamza ka san me ya fara burgeni da kai?" Ba tare da ta jira amsar shi ba ta cigaba.
"Kaifin basirarka da natsuwarka amma yanzu duk kana nema ka rasa, ni ba gudu zan yi ba ina nan ka bi komai a sannu har mu samu albarkarta kaji don Allah?"

"Hidayat companies É—in Abba na na rawa wadda sanadiyar abubuwan dake faruwa dasu na bar aikin soja na dawo don in kula dasu amma na kasa focusing don Allah in zo a É—aura mana aure daga baya se mu nemi yafiyar hajiyar ko zan samu in mai da hankalina kan abu guda.."

Kasake hidayat tayi, Wai me ke faruwa ne?.ta tambayi kanta.. Wani irin possession ne wannan?

(Nima nace ku tayani gani)

**Don Allah wa ya san wani magani na ciwon kunne? Wallahi nayi yawon Asibiti na gaji**

#like
#share
#comment

                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 25*

*FREE BOOK*

*Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na gode matuka da adu'o'inku duk babu wadda ban gani ba... Allah ubangiji ya bar zumunci, baki yayi kaɗan ya furta irin godiya ta da kulawar ku... Wannan page ɗin naku ne masoyan Kowa yaga zabuwa🥰😍*

"Sam ba zan iya baka gudummawa wurin saɓawa mahaifiyarka ba ya hamza, mu cigaba da Adu'a kaji? Sannan kayi hakuri komai ze zo ya wuce kaman ba'a yi ba"
Ta faÉ—a a tausashe sbd yadda hamza ya fara bata tausayi da gaske yake sonta yake sossai.

Ajiyar zuciya ya sauke ba wai don hankalinshi ya kwanta ba suka yi sallama, ta jima zaune a wurin cikin tunani kan ta miƙe ta fito wurin yaran, yau har suka yi magrib da isha be dawo ba saɓanin yadda ya saba yi a gida tare da yaran.

Suna zaune a dining suna cin abincin dare ita kuma tana tsaye a kansu tana HaÉ—awa Junior custard ya shigo, sannu da zuwa suka mishi da kai ya amsa kawai ya wuce room É—inshi.

Ba'a yi awa da shigar shi ba se ga Kimorah ta shigo sanye da wasu irin kaya da daga ka gani ka san wannan a addininsun ma an wuce gona da iri, kallo É—aya ta yiwa dining É—in tace
"Norah, baby Farrah hey!"

Kan ta wuce É—akin Raed É—in, lumshe idanu Hidayat tayi tana me kau da kai..

Norah ma fuskanta be nuna ta ji daaÉ—in zuwan na buduruwar mahaifin nasu ba, se cin abincin ya zama wani iri haka suka gama suka tarkata suka wuce É—akin hidayat É—in, duk yadda yaran suka so su sanya ta cikin hiran su bata iya shiga ba haka suka kyale ta..

"Ma....ma u..wa"
Junior ya fadi cikin harshen yara waenda basu iya magana ba, Norah na assignment ne Aisha kam har tayi bacci yayinda Farrah take riƙe dashi hakan yasa hidayat ɗin miƙewa tace

"bari in kawo maka junior"
Ficewa tayi Sam bata kula dasu ba seda ta zo tsakiyar parlorn, zaune yake a karkace system ɗaure a kafanshi yana kallon Umar series yayinda kwance daga jikinshi Kimorah ce tana ta mishi magana cikin kanƙan da murya.

Da sauri hidayat ta kau da kai ganin sun HaÉ—a idanu a hankali ta musu sannu kan ta wuce kitchen, buÉ—e fridge tayi ta É—auki ruwa me sanyi ta sha sossai tana jin ba daidai ba gabaÉ—aya a yanayinta, ta jima tsaye nan ba abunda take kan ta É—auki ruwa marar sanyi ta fito, bata kalli inda suke ba ta wuce É—aki..

"Why are u looking at her?"
Maganan Kimorah yasa ya É—auke kai daga kallon bayanta ya mayar system ba tare da yace komai ba.

"Meyasa se in ta maka magana kana share ni ne? Tun fa kan na tafi na dena gane maka É—an kulani da kake wadda shi kaÉ—ai ma yake sawa inji na fi kowacce mace É—in ma yanzu baka yi, yanzu ko kwanciya nayi jikinka ka dinga ture ni kenan idan ba na nace ba sede in hakura, please in wani abu nayi maka ka faÉ—amun"
Tayi magana da harshen turanci cikin Raurau da idanu.

Yace cikin gajiya da komai da ma kallon..
"Please kimorah let me be! Ki shiga spare room É—in chan ki kwana ko kije one of the rooms down stairs am not in the mood"

Zata yi magana ya É—aga mata hannu tare da mikewa ya shige dakinshi, haka ya karasa duk abunda ze yi ya kwanta cike da wasu tunannuka..

Washegari tayi ayyukan ta fiye ma da yadda ta saba tashi don kan ace bakwai ta gama komai da komai tayi wanka, bata jira tafiyar yaran ba ta fice don Allah ya gani kwanan ta da wannan buduruwar tashi inuwa ɗaya ba karamin baƙanta ranta yayi ba, haka ta isa makarantar ma ajin bata wani fahimta sossai ba.

Bayan ta gaji da kallon malamin kawai ta fito ta samu wani keɓantaccen wuri ta zauna, lokaci lokaci se ta share hawaye, rabon da tayi kuka tun daga ranar da aka bata labarinshi shima na tausayinshi ne amma kukan dake fita daga zuciyarta tun tana gidan Yusuf se gashi yau tana yi haiƙan.

KafaÉ—anta taji an dafa, da sauri ta É—ago tana share hawayen idanunta se suka HaÉ—a idanu da Rashida..

"Hidayat! Lafiya kike kuka?"

Kai ta gyaÉ—a tace
"lafiya ƙalau Rashida, ba kuma kuka Nake ba"

"karƙi maida karuwa ƴar iska mana hidayat, ai ko makancewa nayi na shafa idanunkin nan na san kin sha kuka, ko de baki ɗauke ni yadda kika ɗauki ummi bane?"

A hankali tace
"Wallahi ba haka Bane, maganan ban san ta inda zan fara bane!"

"Fara ta ko ma ina ne zan baki listening ear"

Zata yi magana taji an ce
"Maama!"

Da sauri ta juya se taga, Norah da Farrah da Aisha tsaye amma Aishan ce tayi kiran.. Da sauri suka zo suka yi hugging nata..

ÆŠago Aisha Rashida tayi tace
"Hidayat wannan ƙanwarki ce ko? Kinga yadda kuka yi kama?"

Dariya ne ya kama hidayat tace
"wani irin ƙanwa baki ji tace mama ba?"

Harara ta zabga mata tare da cewa Aisha da tace mata ina yini.
"Lafiya, gayamin gaskiya waye mamanki?"

Hannu ta É—aga ta nuna hidayat tace
"itace mamanmu da ni da Ya Usman da kuma Junior, ko mama?"

Wara idanu Rashida tayi tace
"har ku uku?"
Kanta se ya kulle hidayat at her age har ta haifi yara uku? Sannan in ta haihu me yasa yanzu suke nema da hamza? Ya abun yake ne kam..
Maganan Norah ne ta katse ta.

"Miss hidayat! Daad is waiting in the car and he hates that."

Wara idanu tayi tace
"Meyasa baki faÉ—a min tuntuni ba? Mu Je"

Gaba suka yi se Rashida ta rike hannunta tace
"amma kin san ba zan bari ki tafi cikin damuwa ba ko? Ina so muyi magana tunda babu ummi ina so please kiyi shearing problems É—inki dani wallahi aminiya na dauke ki"

Ajiyar zuciya ta Sauke tace
"yanzu kinga ana jira na ko zaki biyoni muje gidan se muyi magana?"

Kai Rashida ta gyaÉ—a suka fito a tare, ya É—an sauke glass É—in gefenshi fuskanshi a kame as usual.

Lekawa Rashida tayi ta gaishe shi se suka HaÉ—a idanu, gabaÉ—aya idanunta ta fiddo waje..

"OMG! Moh Raed??"
Wani ƙara ta saki tana sake Lekawa da kyau wallahi kuwa shine..
Chapter 38 · 0% Book details