← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 74

Sashe 46

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kika ce babu abunda fa kika min? Toh ba dole kiyi ba tunda ke kika zaɓarwa kanki? Ko kin manta kece sanadiyar wannan ciwon nawa?"

Wara idanu tayi tace
"Wallahi ba de ni ba, kaima ka san sanadiyar ciwonka ba ni ba kam karka É—aura min... Ah to"
Tana kai nan ta juya fuuu ta fice, da kallo ya bita, Hajiya bazata taɓa chanzawa ba a duniyan nan, Allah ya bashi lafiya shine rokon shi don yana da babban Burin da yake son cimma a duk ranar da cikakken lafiya ta same shi, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah..

#Vote
#share
#comment

                   🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 30*

*FREE BOOK*

*Fav sis🥰❤️ wannan page ɗin naki ne I love you ok😘**

**Allah in ga Ruwan comment in ba haka ba tohm ni de Zaku jini a salansa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️**

Garin yayi lublub kaman hadari Dukda ba hadarin bane sede tarin ni'ima da garin yake dashi shine ya ɓoye ranan a irin wannan lokacin, tana ta kallon hanya Dukda ba tafiya me nisa suka yi ba suka iso wani gaɓar ruwa me cike da tarin boats Parke a bakin gaɓar daga nan kana iya kallon effile tower Tarr sbd ginin da ya riƙe shin a kan ruwan yake.

BuÉ—e mata kofan da Paul yayi shi ya yanke mata Tunanin abunda ta zo yi anan É—in, bayan ta sauko ya nuna mata wata mata baturiya yace
"she will guide u ma!"

Tace
"wait! Are you leaving?"

Yace
"yes ma! My work here is to just drop u and go back home"

Kai ta gyaɗa ya shiga motan ya fice kan ta kalli matar dake gaisheta ta amsa, jagora ta mata zuwa wani tamfatsetsen jirgin ruwa me tsananin kyau fari Kal, wani keɓantaccen wuri daga nan sama da yake kawace da tables farare ta ajiye ta tace
"enjoy the view of seine river ma"

Sossai kyaun wurin ya tafi da ita, ko don girman jirgin ne ko kuma don kyaun shi ne yasa bata ji wani alaman tashin inji ba kan ta ankara dae taga jirgin yayi nisa da bakin gaɓar, mikewa tsaye tayi ta taka a hankali ta karasa wurin karafunan jirgin ta rike tana kallo, masha Allah..

Bata taɓa ganin kayatuwar wuri haka ba, waennan karafun na Paris da ake kira effile tower an kawata shi da wuta blue da ja se walwali yake yi, se ta jita a cikin wani ni'ima na musamman wurin yayi shiru hakan ya saka mata peace of mind, zuciyarta blank ba Tunanin komai se kyau da ni'imar kogin.

Bata san iya adadin lokutan da ta dauka a haka ba wata mata daban da na farko ta zo tace
"weldone ma! Oga said it's time for prayer and dressing"

Kallon kayan jikinta tayi me ya faru zata chanza? Bata yi musu ba tabi bayan matar suka dan sauka cikin jirgin kan ta buɗe wani wuri suka shiga, wow ashe akwai wuri haka a jirgi bata taɓa sani ba se yau, parlor ne me ɗauke da ɗaki da kitchen da toilet, kuma komai akwai, tana ta aikin mamaki har ta nuna mata yadda zata yi anfani da bayin ta fice.

Da tayi alwala se ta tsaya kallon madubin bayin tana kallon kanta, lokuta da dama ta kan bace a tunani in zata ɓata lokaci a gaban madubi se ta shiga kokonton itace wannan ko wata me kama da ita, gabaɗaya ta tashi daga wanchan hidayat ramamma me idanu kaman na Mayu ta koma wata classic chic, ita kanta tana son yadda take tafiyar da rayuwar ta da kuma tsarin dressing ɗinta a natse ba hayaniyar kaya se na tsantsar kyau.

Fitowa tayi ta gabatar da sallahn la'asar ɗinta don ta samu sallaya a shimfiɗe da katuwar ƙimar jalbib a cikin ledan shi ta ɓare.

Bayan ta idar matar ta dawo rike da wasu akwatuna guda biyu tace
"permit me to dress you ma!"

Kai ta gyaÉ—a mata tana kallon ikon Allah, ita fa duk bata san me wannan É—in yake nufi ba kuma, haka dae ta daure ta yi yadda matar tace a take ta fara rangada mata light nude makeup da yayi mugu mugun blending da skin color É—inta ya bata wani astonishing color me fusgan hankali.

Red dress ta ciro mata, doguwar riga ce kaman me zuwa promp night haka dress ɗin ya amshe ta Dukda ba ta inda jikinta ya bayyana banda tsagu dake bariyin kafan ta na dama shima se idan ta buɗe kafar sossai ne ake iya kallon skin ɗinta daga cikin net ɗin rigar shima be kai rabin sharaɓarta ba.

coler neck ne kaÉ—an ne kawai a buÉ—e se ta saka mata sarkar ta da ta zo dashi da wasu designers É—an kunne da kyaun su kaÉ—ai ya ishi bayyana tsadarsu suna dauke da back stones daga tsakiya, kanta se ta saka mata cikin wani silk black É—an kwali da ya zauna sossai a kan nata se black shoes masu Tsai, harda wani black purse, duk wadda ze kalli hidayat a lokacin ze É—auka irin international celebrity É—in nan ce saboda kyaun da tayi.

Ita kanta se kallon kanta take a lokacin da aka gama shirin, matar ta feshe ta da turaruka masu sanyin kamshi.

Ta lura matar se duba time take, bata dae ce mata komai ba ta samu wuri ta zauna, se dab karfe biyar da rabi kan tace mata zasu iya fita.

Mikewa tayi da bismillah sbd takalman kafan ta, ji take kaman zasu yarda ita sbd tsinin su hakan ya sauya mata salon tafiya kaman me tafiyar tarwaÉ—a, sake idanunta tayi tana kwasar kallo sbd yadda saman ya juya mata daga yadda ta shiga ta bari, wow masha Allah, abunda ta furta kenan tana kallon jajayen furrani masu fitanannun kamshi da aka kawata jirgin dashi an yi organizing table da É—azu ta zauna babu komai kai da wasu varieties na abinci harda cupcakes masu candle iska na É—an kadawa kaman ze mutu kaman kuma baze mutu ba.

Abunda yafi ɗauke mata hankali kuma shine rana da yake ta kokarin faɗuwa yayi wani haske me kyaun gani bata taɓa sanin haka sunset yake ba, ta shagala da kallon sunset ɗin taji wani ƙara kaman na flying boat yana zuwa daga nesa, a hankali ta sauke idanunta saitin inda take jin ƙaran zuciyarta ne yayi wani kalar tsalle.

The view of him a tsaye ba riga se wata three quarter black yana riding flying boat ɗin cike da tsantsar kwarewa gashi ya fito ta ɓangaren da hasken ranar ke shirin faɗuwa se ya bada wani kalar kyau da ɗaukar hankali, lumshe idanu tayi ta sake buɗewa tabbas shine builded body ɗinshi se wani haske yake, bata san ta ɗan yi gasping ba ta kuma kasa ɗauke idanunta a kanshi har ya iso jikin jirgin da take yayi tsalle ya haye tare da Juyawa ya ja flying boat ɗin ya sa a mazauninshi na cikin babban jirgin.

Se ya juyo suka HaÉ—a idanu daga inda take tsaye, lumshe nashi yayi ya sake buÉ—ewa she looks so breathtaking to him, kaman kawatacciyar flower dake samun ban ruwa ta fitar da Fure me tsananin kyau da É—aukar hankali haka ta zama, ji yake kaman ya hadiye ta ko ze huta da bugawar da jijiyoyinshi suke da sunanta.

Cikin tafiyarshi ta xaratan maza yake tunakaro ta hakan yasa tayi kokarin fusgan idanunta daga cikin kwayar nashi se kuma ta saukar a inda ya kusa sumar da ita, don sun sauka ne bisa shafaffen cikinshi wandon shi ya É—an sauka har kana iya hango v line É—inshi cikin azama ta sake daukewa se ta rasa takamammen mazaunin da idanunta suke sha'awar kallo bayan shi É—in.

Wani ash cotton shirt da ya sa aka ajiye mishi a linke a wurin ya ɗauka ya sa kan ya karaso gabanta ya tsaya ya sakar mata shanyayyun idanunshin nan yana yaba kyaun halittar Allah a wurin, ganin ta kasa Kallonshi se kafafunshi da suke kyalli sanadiyar ruwan da ya taɓa su gasu bearfooted take ta kallo yasa yayi anfani da wata kalar murya yace

"diehard!"
Wani irin amsawa kirjinta yayi, tsikar jikinta suka bada wani yaammmmm she started to get confuse bata É—ago ba seda taji ya sake maimaita

"die hard!"
Did he mean da ita yake?

Cikin tsoro ta É—aga manyan Fararen idanunta da suka ji liner ta zube bisa kanshi seda ya so yayi loosing balance É—inshi, ya lumshe idanu ya sake budesu a kanta ze yi magana se wani cool music ya fara tashi a cikin jirgin inda ya haÉ—u da yadda suke É—in ya tafi da bugun zuciyarsu ya bada wani romantic scene.

A hankali yace
"I know u have so many questions to ask but please do me a favor of keeping mute nd just follow my lead..!"

Yadda yake maganan da sanyi da wani kulawa yasa bata san ta É—aga kai ba, yayi mata leading to kujerun wurin table É—in da aka musu ado da jan kyalle, da kanshi ya janyo mata ta zauna kan ya tsaya daga gefenta kaman bawan ta ya shiga serving É—inta a natse.

Se lumshe idanu take tana sauraren lyrics na wakan dake tashi a hankali zuciyarta ke skipping..
"It's you!
Ur eyes
Ur smile
The way you walk!
The way you talk!
The way you laugh!
I could stare at you forever
I love everything about you!
It's everything..."

Har wani rawa rawa hannunta yake yi tsabar yadda zuciyarta ya matse ya shiga cikin wani wahalalliyar yanayi da ya so mantar da ita komai da kowa a duniya se wannan moment É—in da shi shi kaÉ—ai.

"Eat die hard"
Da hannunta da yayi sanyi ƙalau tayi anfani ta ɗauki spoon ɗin ta fara cin brown rice da daga yadda yayi serving ma dole ya baka sha'awa, da coconut milkshake.
Chapter 46 · 0% Book details