← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 74

Sashe 15

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun kusa one hour a haka ita bata zauna ba haka shima kaman be san da halittar mutum dake je ka ka dawo ba a wurin, É—akin da aka shiga dashi ne ya buÉ—u likitan ya fito yana share gumi yace
"am sorry we cannot save him Jini yayi forcing kanshi to his brain wadda yayi ajalinshi, Allah ya gafarta masa ya baku ha..."

"Us..us..man É—inaaa? A'aaaa A'aaaa ba shi ba dae! Ba shine bane! Dan Allah baze mutu yanzu ba..! Wayyoooo I can't, I cannot loose him! Yarona...."
Wani irin kukan da bata taɓa yi ba na tashin hankali take, he's just a little child yanzu ya fara rayuwa!

Sulalewa tayi kasa a sume, a take itama aka yi emergency da ita.

Moh Raed da ya runtse idanu tun jin rasuwar ya buÉ—e tare da bin gadon da aka wuce da ita da kallo, he's so heartbroken yana tuna sadda Usman yake ce mishi fuska cike da farin ciki cikin Salon maganan yara..
"Allah ya biya ka da gidan Aljanna yasa a mizani haka mama tace a cewa duk mutumin kirkin da yayi maka alkhairi.!"

Sake runtse idanu yayi yana tuna murmushin yaron, he can't imagine himself losing one of his child Norah or Farah.

Shi yayi komai har aka fiddo gawar Usman zuwa motan Ambulance, hidayat da wata nurse ta taimakawa ta fito ko tsayuwa bata iya yi ya kalla gabaÉ—aya ta firgice, kaman robot haka take tafiya.

Wayanshi da ya dauki ringing akallah na kusan shidda kenan ya kallah kan ya É—aga a lokaci É—aya ya lumshe kyawawan idanunshi yana sauraran faÉ—an da ake na mintuna kan ya saukar da wayan ba tare da ya ce komai ba, a Ambulance din hidayat ta zauna ya je motanshi ya dawo a kan cinyar ta ya ajiye envelope hakan ya sakata É—ago idanu.

Sarkewa idanunsu yayi cikin na juna a hankali ta sauke nata cikin muryar nan tashi me nauyi da be fita sossai yace
"May his gentle soul rest in Peace, he will be in a good place in shaa Allah"

Yana kai nan ya juya ya wuce, shi karan kanshi da sau ɗaya ya taɓa ganin Usman he felt the death bare mahaifiyarshi but, she's really too young for this.

Seda Ambulance É—in ta fice a asibitin for some minutes kan ya iya tada motar shi ya fice da mugun gudu...

*am in full tears😭😭😭🤧 kuyi hakuri gobe ba tabbacin Zaku samu sbd ina da abubuwan yi dayawa amma in na samu chance in shaa Allah Zaku jini*

#like
#share
#comment

                    🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 11*

*FREE BOOK*

**Ameeratuh kin hana ni baccin safe🤧 ga shinan kan ki zo min a mafarki🚶‍♀️🚶‍♀️**

"Hidayat haba mana kar imaninki yayi ƙaranci ki dinga furta kalmomin da zaki je kiyi saɓo, Usman kwanan shi ya riga ya ƙare shine dalilin mutuwar shi Sam baki yi Sila ba sbd be yi gaggawa ba mu ma kuma ba jinkiri mu kayi ba, yau kwana bakwai kenan bakya ci bakya sha, sbd kuka dubi idanunki yadda suka koma ki kalla ki ga Aisha yadda take a firgice tun rasuwar nan shi karan kanshi junior  bakya bashi kulawar da ta dace idan ke kika Gaza su kuma fa?"

Idanunta da suke a sussuntume tun rasuwar ta É—aga ta kalli ummi tace cikin wani irin murya
"haka ne! Na gode ummi yanzu ina ga lokaci yayi da zan yi abunda ya dace, ba zan yi faÉ—a da YUSUF yanzu ba amma ba shi yake nufin ya sha a banza ba, yanzu ne na fara koyo daga karatun da duniya take koyar dani, zan yi bita in hardace a duk sadda na tashi amsa jarabawar baze yiwa kowa daaÉ—i ba saboda da 100/100 zan fita, yanzu zan iya yin duk abunda ya dace saboda yarana biyun nan da kuma fansar jinin Usman... YUSUF! hmmm"

Dukda ummi bata fahimci maganan ta ba, ita dae tunda tayi magana yau da sauki, abinci wadda ummi na shigowa gidan hidayat ta mika mata envelope da Moh Raed ya ajiye mata Dukda bata san waye shi ba ya taimaka mata har aka gama gaisuwar usman ba'a rasa abinci da ruwa ba.

A gabanta ta ajiye Seda ta kalli abincin na seconds kan mutumin ya faÉ—o mata a rai, Allah kaÉ—ai ya san daga ina yake ya tsaya ya taimakesu ba tare da neman komai a wurinsu ba, ko ma dae menene she's so much indebted to him.

A ranan ummi ta koma gidansu ganin Hidayat ta dena koke koken ta natsu, kan Ummi ta tafi babu abunda bata mata ba har abinci ta sake girka wani ta sa a food flask ta ajiye mata, yamma Lis tana yiwa Junior wanka Aisha da yanzu babu yawan maganan tan nan na zaune gefe tayi tagumi kaman wata babba.

Kaman an jefo shi haka ya faÉ—o gidan tun daga dukan da yayi musu ita da Usman bata sake ganinshi ba se a yau Usman na kwana na bakwai zuwa takwas a rami, yadda ya shigo yasa Aisha firgita ta tashi da gudu taje ta faÉ—a jikin hidayat tana kankameta kaman zata shide take cewa

"Abba! Abba kayi hakuri don Allah karka dakemu... Ya Usman ya mutu nima karka kasheni karka rabani da mamana!"

Hawaye ne ya sulmiyowa hidayat ta É—ago rinannun idanunta ta zube a fuskanshi, haÉ—e rai yayi kaman wani mala'ikan É—aukan rai yace
"ke ya ma sunanki? Wallahi kika kuskura na rike ki se na lahira ya fi ki jin daaÉ—i"

Hidayat bata sake Kallonshi ba ta É—ago ta tana share mata hawayen dake zuba tace
"karki sake kuka Aishana ai yanzu kuma me dukanki se ruwan sama shi É—in ma se in na bari, ki dena kukan nan bana so"

Har ya wuce ya dawo yace
"me kike cewa?"

Mikewa tayi tare da ajiyewa Aisha junior a cinyar ta ta kalleshi cikin idanu tace
"nace me taɓa ta kai har ma ni a yanzu kam se ruwan sama!"

"kina nufin ban isa taɓaku be kenan?"
Da mamaki yake maganan ganin ko É—ar babu a fuskanta se wani irin shakkar ta ya rufe shi da a da ne ze iya kai mata hannu zuwa yanzu.

"Yadda kunnuwanka suka ji"

"Ah lallai kan mage ya waye, karki manta a gidana kike kuma har yanzu ni mijinki ne, ita kuma wannan Æ´ata ce don haka ina da ikon yin yadda na ga dama a lokacin da na ga dama.."

Wani irin dariyar rainin hankali hidayat ta saki kan ta juya manyan idanunta tana kallon gidan tace

"Gida fa kace? Ai ni ban ga gida ba banda kasungumin daji me cike da namun dabba masu hatsari da ban tsoro, jikin hidayat kuwa daga kwana bakwai baya ka datse duk wani alakarka da ita, datsewa ta har Abada kuwa... Ashe se yau ka san Aisha Æ´ar ka ce? To kaji da kyau Aisha da Muhammad Raed Æ´aÆ´an hidayat shine sunansu, basu san wanene yusuf ba kuma ba za su san shi ba. har Abada sunansu ya tashi daga Aisha Yusuf zuwa Aisha hidayat Abubakar, ni nice uban su kuma ni ce uwar su don haka ka kiyaye alakanta kanka dasu"

Gabaɗaya idanunshi a waje suke yana mamakin wannan sabuwar hidayat da be taɓa gani ba, kwarjininta da yadda take kallon shi cikin idanu babu tsoro se ma hango wani wutar bala'i dake tashi a cikin idanunta yasa yaji wani sanyi sanyi na kokarin lulluɓe shi.

Cikin karfin hali yace
"kin san a yau na sake ki zan iya auren mata huÉ—u rus? Kuma a yau na sake ki baki da wurin zuwa so dole ki dawo nan É—in ki tsuguna a gabana ki roki gafara a lokacin kuma ina ga lokaci ya riga ya kure miki..."

Hannunta ta harÉ—e tace
"babu macen da zata iya zama Da Mugun Miji irin ka Yusuf idan ba hidayat ba har Abada ba'a yi macen da zata iya shigowa wannan kurkukun kaddarar ba, kuma ka ji da kyau idan har na saka kafafuna na fita daga gidan nan wallahi wallahi ko mutuwa zan yi a waje na gama taka harabar gidan nan kenan  gwara in mutu da in sake alakanta kaina da kai... Azzalumi, Fasiki, makashi..."

Tayi maganan hawaye na gangaro mata sede fa ba shi ya nuna gazawarta ba, hawayen na wutar bala'in dake cin ƙasar zuciyarta ne..

"Ni kike kira da waennan sunayen? Kije na sake ki saki BIYU"

Wani dariya tayi tare da haÉ—e hannunta ya bada sautin clap tace
"tafi nono fari, ko baka sakeni ba dama bani da ra'ayin ci gaba da zama da kai.."

Har ya fara tafiya tace
"Baka ji ba!"

Waiwayowa yayi tana murmushi tace
"Karka yi tunanin Idan hidayat ta tafi ta tafi kenan fa, Hidayat zata dawo idan har ta Rayu zata dawo ta zama WUTAR DAJIN da babu zato babu tsammani se de kawai a ganta ta mamaye dajin, se ta tabbatar ta yagalgala rayuwarka ta yadda baka yi zato ba, nayi alkawari ni hidayat daga yau a gareka kadangariyar bakin tulu ce a bar ni na ɓata ruwa a tabani kuwa a fashe tulun... Daga rana irin ta yau jinin Usman ba ze barka ba har se ka je inda ka tura shi....
Kuskurenka ɗaya Yusuf! Shine na taɓa wutsiyar damisar dake bacci cikin yunwar kwana da kwanaki.. Ka ga ko me kwatarka se Allah.."

Gabanshi ta karaso ta HaÉ—a yatsunta biyu suka bada wani sautin É—as har sau uku kan tace
"put this at the back of your thick lunatic skull!! Zan dawo.. Hidayat zata dawo"
Chapter 15 · 0% Book details