← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 74

Sashe 29

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abunda ba'a taɓa yi ba aka yi a gidan hidimar suna da yanka rago se akan Raed, ba tare da sun san wani baƙin hassada da kyashi da kuma tsanar Muhammad ɗin da Mairamu Bukar da Daadida suka kara musu ba.

Raed na wata biyu wata matsala ta fara kunno kai na ɗauki ɗaiɗai da ake yiwa dabbobinshi don kullum se ya kirge su tsab, ranan da ya kirga yaga ba rago ɗaya tashin duniya ne kawai ba'a yi a gidan ba don duk ya tarasu ya kwashewa duk wadda ya taɓa mishi dabba albarka se washegari aka sake zare akuya ɗaya.

Horon abinci ya musu yace kar yaga an hura mishi wuta a gidanshi in dae har da iccenshi da kuma kayan abincinshi za'a yi anfani, gwara ma Mairamu albarkacin shayarwa ya turo mata biredi da shayi wadda ita kuma ta raba da Daadida don har ita hukuncin shi be tsallake ba.

Bayan kwana biyu aka sake dibar kaji biyar, ranan tarasu yayi yayi rantsuwar idan ba'a fitar mishi da ɓarawo ba duk ze sake su su bar mai gida da yaran su duka.

Badi'ah ce ta fara magana tace
"to ni de ban son in yi magana ne ace na ce amma tsakani da Allah banda Mairamu da Daadida dake shiga wurin dabobbin nan cikin mu ba me shiga daga shara se shara"

Zarah tace
"Najah mu faÉ—a"

Najah ta girgiza mata kai yace cikin tsawa
"me Zaku faÉ—a É—in maza a faÉ—a in Ji"

Zarah ta fara in ina.. Tace
"dama gab asubahin yau ne na tashi da nufin zuwa bayi shine na leƙa window Naga an buɗewa wani kofa ya fita rike da wani kwando a hannunshi kuma da aka dawo ɗakin Mairamu Naga an shiga Dukda ban kalli fuskar ko waye ba"

Ta Yi shiru kan ta sake cewa
"ranar da Akuya ta ɓata kuwa da ni da Naja muna zaune daga wurin shiga turken Mairamu ta zo ta wuce mu ta shiga kuma ta jima kan ta fito ko kan fitowanta diran abu muka ji kaman ta gini da kuma kukan awaki amma mun leƙa tace mana ta ɗan yi tuntube ne garin kwashe kayan Raed daga kan gini shine akuya suka razana don ta kusa faɗa musu ko Naja?"

Najah ta gyaÉ—a kai tace
"hakane wallahi"

Badi'ah tace
"in de kuwa haka ne to itace me alamar tambaya Kato kuwa a kanta"

Wani kallo Bukar ya watsa mata yace
"me zaki yi min da dabbobi? Me kika nema kika rasa da zaki fara min ɗauki ɗai ɗai da dabbobi to kiji da kyau wallahi wallahi dabba na ɗaya ya sake ɓata zaki yi mamakin mataki da zan ɗauka"

Daga haka suka watse ko sauraran ta be yi ba, tayi kuka tayi kuka har taji ba daaÉ—i saboda kazafi komin kankantarshi akwai ciwo Daadida ce tayi ta lallashinta.

Wasa wasa aka gane satar dabobbin bukar wadda Mairamu ke shan azabar hakan saboda yadda yake gana mata wahalhalu akan hakan har sakinta yayi tayi ta kuka tana bashi hakuri don bata da inda zata je karshe yace ta zauna sede ta nemi abunda zata ci da kuɗin dabobbin shi da take sacewa kuma ɗaya ya kara ɓata se ta bar gidan.

Haka suke raba abincin Daadida don ita bata da sana'ar da take yi kaman sauran matan waye ma ze bata jari, ga damuwa da ya mata yawa ga wahalan aiki don duk ayyukan da suke rabawa ita kaÉ—ai take yinsu.

A hankali a hankali bukar ya fitar da Mairamu da Raed a ranshi saboda laifukan da take mishi da yake ganin cin fuska ne, dukanta yake ba ruwanshi in abu ya samu dabbobinshi sanadiyar ta don ita kuma ke hidimar su tsab.

Raed na shekara uku har ya iya tafiya da magana sede be isa ya fita tsakar gida ba mugunta babu irin wadda matan gidan da Æ´aÆ´ayensu basu mishi, wani lokacin ma har da wuta ko ruwan zafi.

Wani rana kaddara ya sa Mairamu shiga É—akin Bukar don gyara mai, dama aikinta ne amma fa se in ya faÉ—a kamin nan sannan kuma yana kofan É—aki yana jiran ta har ta gama to yana sauri wani cinikayya da ze yi se be rufe É—akin ba ya fice, ita kuwa ta gama duk ayyukan ta tace to akan ya dawo kuma ya sakata bari kawai ta shiga tayi shine ta shiga tayi ba tare da ta san ajali ke dibar ta ba.

Ta shiga ta gyara fes ta fito ta koma daki wurin Daadida, chan bayan la'asar Bukar ya shigo ya shiga É—akin shi kusan mintuna biyar ya fito ya fara kwala kiran Matan gidan gabaÉ—aya a razane suka fito jin muryarshi a haukace.

Yace
"ina kudade ne?"
A gigice yayi maganan.

Duk a tsorace suka ce
"wani kuÉ—i malam?"

Yace
"tambaya ta ma kuke yi? Ku fito min da kuɗina ko kuma wallahi dukkanku rayukanku ya ɓaci wallahi wallahi akan kudin nan babu abunda ba zan yi ba ku fito mun da kudade na"

Duk rantse rantse suka fara ya daka tsawa yace
"wa ya shigar min É—aki a cikinku?"

Dukkansu Mairamu suka nuna aiko kan tayi magana ya fara sauke mata maruka har Raed dake hannunta ya faÉ—i, a gigice ya kwala kara itama tana kuka take ce mishi wallahi bata É—aukar mishi kudi ba shi kuwa yana cewa se ta fitar da kudadenshi har dubu É—ari uku wallahi se ta fitar.

Duk yadda Daadida tayi kokarin hanashi dukanta kasawa tayi karshe itama tura ta yayi ta faÉ—i ta kuma kasa tashi saboda kwankwasonta da yayi mugun bugawa se ta saka kukan bakin ciki kawai.

HaÉ—a Mairamun yayi da Raed ya ja su kaman kayan wanki zuwa kofar gida ya watsa su wadda dab titi ne kuma Raed ne ya sauka bisa titin, dukda azabar da Mairamu ke ciki a gigice tayi kanshi ta É—auke shi sede ta kasa mikewa, horn me karfi take ji amma ba yadda zata iya sake tashi hakan ya sa ta cilla shi gefen titi ita kuma ta runtse idanu tana ambaton Allah.

Me motan ya kasa riƙe Birkin shi don da full spead ya zo hakan ya sa ya mata mugun bugawa a take ta some, ya ɗauke ta da Raed zuwa asibiti tare da wani ɗan unguwa, sede suna isa ma aka tabbatar da ai ta cika sossai pastorn ya firgita da mutuwar gashi musulma hakan ya sa be koma gidan bukar ba seda yayi Involving police aka dawo da gawa inda aka nemi bukar.

Aiko yace se an biya diyya, nan pastor David ya biya kusan 2mil kuma bukar ya amsa cikin jin daaɗi wannan abu ya sawa Daadida hawan jinin da seda ta fi wata biyu tana jinya, a wata biyun nan azabar da Raed ya sha wurin yaddikonanshi ba'a magana sun dena kiranshi da sunanshi sede ɗan ɓarauniya ko Duna (saboda baƙin fata ne dashi kalar na Daadida don iyayen shi duka biyu farare ne)

Ko da Daadida ta samu sauki ita da Bukar idanu ne, tana kula da Raed sossai babu kuma irin cin kashin da su Najah basa mata sana'a ta fara sossai tana biyawa Raed duk wani bukatar shi don ba ruwan uban dashi.

Raed na five yrs wani babban al'amari ya faru wadda yayi sanadiyar da har Daadida ta bar gidan wadda su Najah suka zuga Bukar akan kar ya barta ta tafi da danshi aiko ya hana tafiya da Raed, taurin zuciyarshi kuwa ya hana shi ganin laifin da ya aikata babba.

Raed ya taso ne cikin tsananin ƙaunar kwallo yana son ball ta yadda ko a cikin gida yake zaka ga yana buge bugen ƴan ledojin da yake Haɗawa ya maida su kwallo, dama Daadida ce ke koya mishi karatu a gida wadda yayi nasi zuwa sabbi da kuma ayatul kursiyu sede tunda ta tafi kuma yaddikonanshi sun hana shi zuwa wurinta da sau ɗaya yaje suka mishi sharrin da ya sa Bukar kusa kashe shi shima be kara zuwa ba.

A hankali ya mance sauran wadda ya iyan ma banda Falaq nasi da kuma qulhuwa se ayatul kursiyu da salatin annabi saboda ba'a sashi a Arabi ba bare boko su sauran yayyun shi mata da suke yi ma saboda iyayensu mata ne ke biya musu shi da bashi dashi se dae zaman gida da bauta.

Ya bautu iya bautuwa Sanna ya azabtu ya kai ya kawo a turken awaki yake kwana saboda É—akin mamanshi da É—akin Daadida su Badi'ah rabewa yaransu suka yi be isa ya shiga ba.

Wata rana baban ya kalleshi yana kwallo ya rufe shi da duka akan abun Yahudawa ze kawo mishi gida, kaca kaca ya mishi da kyar ya iya bacci, da safe da hidimar gidan ya tashi shi ke diban ruwa yayi shara, ya share É—akin dabbobi ya wanke ya kuma ciyar dasu.

Se ya gama diban ruwa ya zo ze huta se yaga sun yashe ruwan masu wanka sun yi masu zubarwa sun zubar haka ze sake komawa ya sake dibowa gashi da kadan kadan yake dibowa don bucket yafi karfinshi, kuma kullum se an yi abunda ze sa Bukar dukanshi kaman Allah ya aiko shi.

Akwai wani rana da ya zo ya ajiye ruwan dabbobi ze fara saka su sha Badi'ah tayi kiranshi ya je ta bashi kudi akan ya je ya sayo mata cingam ya fice ko da ya dawo ya samu shanu É—aya ya sha ruwan kuma se ya ganshi kwance.

Yaje ya taɓa shanun don be saba gani suna bacci haka ba sede shanu kam be motsa ba, Najah ce ta shigo ta rabka salatin da ya saka Raed mikewa a razane, Bukar ya shigo wurin da shigowanshi kenan yaji salatin wani ashariya ya zabga ganin katuwar bijiminshi kwance ba rai.

"Me ka sa a ruwan?"

A razane cikin tsananin kaÉ—uwa da tsoron uban yace
"ban saka komai ba...wallahi Baba ban sa komai ba!"

Gigitaccen mari ya É—auke shi dashi wadda ya saka ya dena ji na wucin gadi.

"Zaka fara yi min irin muguntar da uwarka tayi min ko? To wallahi uban ka zan ci"
Chapter 29 · 0% Book details