← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 74

Sashe 5

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawar murya tace
"A'a umma don Allah kiyi haƙuri wlh Abba ne ya matsa na ɗauki kuɗin machine shine zan zari dubu ɗaya.."

Wasu Zafafan maruka hagu da dama ta É—auke ta dashi wadda Seda ta saka ta kaiwa kasa tana ji kaman amsa kuwwan maganan umma tana cewa
"Munafuka! Algunguma sharri zaki yiwa Alhajin? Ina ya ga bakin magana da har ze matsa ki ɗauki kuɗi? Idan ba salon sata ba me yasa da kika shigo baki shiga cikin Gida ba kika sulale nan? Eyee wato da mudi me gadi bai ce min kina nan ba sede mu zo mu samu an wawushe Alhaji? No wonder kullum kwanan duniya ake samun kuɗi ya ɓata.."

Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, ta sa hannu ta goge har lokacin bata ji daidai sbd umma ba bahaushiya bace irin kabilan kudun nan ce da suka ginu da tuwo da wahala hakan yasa hannunta na daga cikin hannun da in ta sauke maka se ka rasa natsuwa da ji na tsawon lokaci, cikin rawar murya tace
"Wallahi ban taɓa ɗaukan abin wani ba umma kuma ke sheda ce, da ina sata da tun kan nayi aure da kin sani Allah ya gani b..."

Gwaɓe mata baki tayi wadda Seda ya fashe umma tayi.

"Rashin kunya kuma zaki min? Eh lallai dole.. Karki ga kaman kin haihu biyu ko kina da tsohon ciki wlh baki sauya a idanu na ba, be dame ni ba yanzu in lakaÉ—a miki na jaki in ga uban da ya tsaya miki a garin Kano, banza Æ´ar Zina...."

FaÉ—uwar mutum da suka ji yasa duk suka juya, Jijjiga Abba ya fara wadda har yana sulmiyowa daga cikin kujeran ba tare da sun kula ba seda ya faÉ—i.

Da gudu suka yi kanshi suna kiran sunanshi, umma na shikenan ta kashe min shi ta huta.

Kaman daga sama se ga Yusuf da kaninshi mus'ab da gudu suka É—auki Abba suka fito zuwa mota.

Hidayat bata tsaya ba ta shiga motan tare da kafe shi da idanu tana zub da kwallar takaici da baƙin ciki, babu wadda ya kula sbd tashin hankali suka ja suka yi asibiti umma ta biyo su da motan ta, suna parking a harabar kumfa ya fara fita daga bakin Abba hankali tashe Hidayat ke share mishi da hijab ɗinta.

BuÉ—e idanu yayi ya kafe ta da shi, wani natsuwa da karfin gwiwa ta samu a take ta fara karanta Kalmar shahada abu da ikon Allah mutumin da ya shekara É—ai É—ai har shekaru bakwai da watanni a yanayi na jinya da rashin magana da tsananin ciwo ya buÉ—e baki kalmomin na fita a rarrabe ya fara cewa

"Kiyi haƙuri da rayuwa, ki yafe min hidaya!"
Sune suka fito kaman an fusgo su daga bakinshi, kalaman da suka yi sanadiyar karasa ruÉ—ata tsabar hawayen dake kwaranya har bata iya gani da kyau tana girgiza kai tace
"baka min komai ba Abba..! Baka min komai ba..!!"

Murmushi yayi se ya fara karanta Kalmar shahada daga karshe numfashinshi ya tsaya Chakk.

Daidai lokacin da Yusuf ya fisgota waje ba tare da yayi la'akari da cikin jikinta ba, isowarsu kenan da gadon marasa lafiya don a É—auki Abba sede likitan na lekawa yace

"Innalillahi wainna ilahi rajiun! Sede haƙuri Allah ya riga ya amshi abun shi"

Ihu umma ta kwala, yayinda hidaya da ta riga da ta san da mutuwar sede bata yardar ma zuciyarta ba seda taji daga bakin likitan, chaak duniyar ta tsaya mata Sam bata san me suke yi ba.

Idanunta sun yi ja ga hawaye masu zafi suna gangarowa, ji tayi kirjinta ya mata nauyi ga wani zafi da yake aikin yi mata kaman ze kama da wuta ko ya riga ya kama, Ko sunanta zaka tambaya a lokacin tana da tabbacin bata san daga wata kalma ta fara ba tsabar tashin hankali, shikenan ita kuma alqiyamarta ta tsaya, bangon ta, jigon ta ya rushe ya zube! Shikenan fah bata da kowa da ya saura mata a duniya shikenan!
Wani irin jiri ya ɗibe ta ta duƙe bisa gwiwowinta ta fashe da wani irin kuka da dukkan zuciyarta kaman wacce aka lodawa gabaɗaya damuwan duniya a kirji.

17 YEARS EARLIER

Yarinya ce Æ´ar kimanin shekaru biyar tsaye jikin rariya Dukda Duhu da sanyi irin na asuba da ya mamaye garin ita tsaye take tunbur babu ko É—an kamfai a jikinta, banda rawar sanyi babu abinda take yi hawaye kuma wani na bin wani a idanunta sbd jikinta dake raÉ—aÉ—in duka da taci da asubahin Allahn.

"Tsaye kika yi baki watsa ruwan nan kin zo kin fitar da kayan nan kin wanke ba?"

Da sauri ta É—auki bocket É—in ruwan ta kwarawa jikinta bayan ta É—auke numfashi saboda azaban sanyin shi musamman umma ke ajiye shi ya kwana buÉ—e yadda ze yi sanyin da se ya kusa daskarar da gudun jininta.

Bayan ta gama ta taka a hankali zuwa cikin É—akin ta É—auki rigar ta da ya koÉ—e wadda kuncen Surayya ne ta saka, dukda ba wai ta girma bane ga rashin girman jiki da ya mayar da ita Æ´ar pirut ta É—auko ledan pitsarin da zanin ta koma chan baya ta wanke ta shanya a saman soak away sbd tsawon ta da baya kaiwa igiya.

Har ta dawo ɗakin dukkansu yaran gidan na kwance suna bacci, tsabar kwarewar umma a mugunta Dukda akwai masu shara sede ita ɗin de ita zata yi a Cewar ta bata kai matsayin ƴan gida ba kuma dole ta dinga tunawa da ita ɗin Ɗiyar Riƙo ce, haka ta daddage tayi ta shara in be fita ba ta koma ta sake sbd a haka ta saba, se a lokacin yaran gidan suka tashi, manyan suna wanka da kansu yayinda yaran se de ayi musu har Surayya kuwa dake sa'ar ta, bayan sun gama aka shiryawa kowa breakfast ɗinshi wadda dankalin turawa ne da shayi me madara.

Raƙubewa tayi jikin dining ɗin tana jiran su gama ta bi plates wadda suka rage ta ci, hakan kuwa aka yi bayan sun koma parlor kowa na saka safa ta tashi ta bibbi plates ɗin ta cicci wadda suka rage ta tattare ta kai kitchen, ta dawo da sauri ta je ta saka uniform ɗinta sbd sun fara ficewa in kuwa ta ɓata musu lokaci ba karamin duka zata ci ba.

Bayan ta saka bata tsaya sa safa ba ta riƙoshi a hannu da jakanta ta fito da sauri, a gaban Abba ta same su da shima ya fito ze tafi wurin aiki, tun daga nesa ta sakar mishi murmushi shima yana murmushi har ta ƙaraso hannunshi ta riƙe tace
"Abba ina kwana?"

Yace
"lafiya ƙalau hidayat, an shirya kenan?"

Kai kawai ta gyaÉ—a sbd bata da yawan magana, hannu ya sa a aljihu ya ciro hundred hundred Naira ya ba kowaccen su, godiya suka yi kan suka yi mota a lokacin Yusuf na Level one a university.

Khausar da suke cewa Aunty kausi tana js2 se Mus'ab dake primary 6, se Salamatu dake pri 5, fahariyya tana Primary 4, se ita da Surayya dake primary 2, babu wacce ta mata kallon arziki a cikinsu sbd bata takale su ba inda ta saba duƙawa a ƙasan motar wurin ajiye kafafu ta duƙa don bata da darajar zama a seat har suka isa makarantar, kaman yadda ta saba seda ta kwashe jakkukkunansu ta kaiwa kowacce class ɗinta kan ta ɗauki nata dana surayya ta kai musu class, a seat ɗinta ta ajiye mata kan ta wuce nata ta zauna kusa da ummi.

Kaman ka'ida ana tashi ta bi ta tattare jakukkunan ta kai musu mota kan ta tsuguna a mazauninta suka kama hanyar gida, ko da suka isa gida ma a nan parlor suka dinga cillar da abubuwansu tana tattarewa tana kaiwa inda suke tara kayan na wanki, a É—akin nasu chan lungu aka shimfiÉ—e mata taburma da zanin gadon da bata san shekarun shi ba alhali kowacce a cikinsu da gadonta na katako a wakeken É—akin.

Anan ta cire uniform ta sauya na islamiyya ta fito, lokacin sun yi nisa da lunch inda ta saba zama ta zauna, minti minti wannan ze aike ta wanchan zata aike ta har suka gama, ta tashi ta bi plates É—insu ta ci abinci kan ta tattare ta kai kitchen, ganin babu wacce ke da niyyar zuwa Islamiyya cikinsu yasa ta fice.

Wuraren karfe biyar ta taso daidai kofan gate suka haÉ—u da Abba wadda driver ya dawo dashi daga office, bayan ya shiga be shige sashen shi ba se ya jirata har ta karaso ta gaida shi cike da kulawa ya amsa yace

"hidayat ina Æ´an uwanki? Me yasa baku taho tare ba duka kuke tafiya daban daban?"

Cike da yaranta tace
"Abba ai basu je ba, ni kaÉ—ai na je"

Ya jefa mata tambayar
"ko me yasa?" Da sauri.

Tace
"nima ban sani ba Abba"

Hannunta ya kama suka wuce sashen umma, a parlor ya same su baje, masu kallo na yi masu danna waya na yi be yi wata wata ba ya zare cable É—in TV Seda ya ba kowacce biyar biyar kan ya ja musu kunne akan ko da wasa ya sake samun su ran islamiyya basu je ba sun zauna suna shashanci yana kai nan ya fice.

Tunda aka fara dukar taji kaman fitsari na shirin kubce mata don ta san yau yankata ne umma ba zata yi ba, yadda take ƙaunar yaranta ko kuda bata so ya taɓa su, tunda Abba ya fice ta zube bisa guiwowinta cikin shesheka take cewa

"Wallahi ba ni na faÉ—a mishi ba, umma wlh ban faÉ—a ba.."

Mikewa umma tayi ta nufota, yarfe hannu kawai take tana wayyo Allah, ko da umma ta iso É—ankwalinta ta cire ta cusa mata a baki tare da fusge hijab É—in kanta ta É—aure bakin yadda ihunta baze fita ba ta fara jibga kaman me faÉ—a da sa'ar ta.

Zata iya cewa ta suma a lokacin sbd azaba ga ba halin ihu bare roƙo, Seda umma taga tana shirin kashe rai kan ta sauka ta wuce ba tare da tace uffan ba ta karkaɗa kan yaranta zuwa ɗakinta, dab kofa ta waigo ga hidayat dake yashe ko motsin kirki bata yi ba tace
Chapter 5 · 0% Book details