Sashe 17
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawai se ta fashe da kuka me karfi saboda tsoratar da tayi hakan yasa Aisha ma fara sabon kuka.
Wani tsakin ya kuma ja kaman ya wuce yayi tafiyar shi sede tunda ya gane Aisha daga cikin mota yaji ba ze iya tafiya ya kyale su ba hakan ne ma ya saka shi fitowa taimakonsu but look at what her mother is doing...! Be san wasu irin mutane ne a Nijeriya ba har yanzu mamakin waennan da suka zo satar Aisha kiri kiri yake, haka ƙasar mu ta lalace?
Kallon Area ɗin yayi Gidaje ne manya manya na masu hannu da shunin garin Kano, ko wani gida ka kalla zaka san ba ƙaramin kudade aka kashe wurin ƙerawa ba, sede rabi da kwata Gidajen empty ne duk ana Abuja ko Lagos ko ma kasashen waje, wurin yayi shiru dayawa da za'a iya kashe mutum a binne ba tare da kowa ya sani ba ko da kuwa da rana ne bare dare.
Hulan ya sauƙe, gyararren ponk ɗinshi rinanne ya bayyana, hannu ya sa ya shafa kan tare da zare facemask ɗin yana zuƙar iska tar kyakyawar fuskanshi ta bayyana, diamond ear ring ɗinshi na shining..
Aisha dake Kallonshi kaman yadda hidayat ke Kallonshi ta fusge ta ruga da gudu taje ta faÉ—a jikinshi tana cewa
"Daddy!"
wara hannu yayi ya chaɓe ta se ta fashe da kuka.
"Shhh! Shhh Shhh it's OK you are safe honey.."
Se a lokacin hidayat dake Kallonsu ta dukar da kai tana É—igar da hawaye..
Shine Daddy? Shine wannan mutumin da ya taimaka mata a sharafan mutuwa, shine wannan wadda ta sanadiyar shi take numfashi har kawo yanzu, shine ya taimaki Usman a sadda ya ɓata garin nema mata taimako, shine wadda ya taimaka mata zuwa kai Usman Asibiti ya biya bill ya kuma biya Ambulance da ya maida su har gida, shine ya ciyar da mutane daga aljihunshi har mutane suka ci suka sha zuwa ƙarewar makokin Usman, sannan shine ya taimaka musu a yanzu da ake kokarin cutar dasu... Lallai Tarihin hidayat baze cika ba idan ba'a kira sunan wannan bawan Allahn ba, shi ɗin kaman mala'ika ne a wurinta da Allah ke turo mata a duk sadda take buƙatar taimako ita yanzu baiwa take a gareshi saboda ya mata abunda babu wadda ya mata a duniya...
Hannun Aisha ya saki yana shirin wucewa tunda mahaifiyarta bata bukatarshi da sauri Aisha ta sake rike hannunshi tana kuka tace
"Daddy karka tafi ka barmu, bamu da inda zamu je, Abba wai ya saki mama mun je gida umma ta koremu ni tsoro nake ji.. Karka tafi Daddy..!"
Ɗago ido yayi ya kalli hidayat dake Kallonsu se tayi saurin duƙar da kai ba tare da ta bari sun Haɗa idanu ba, hannun Aisha ya riƙe ya zagaye ta ya je ya buɗe gaban motanshi ya ɗaga Aisha ya ajiyeta ya rufe kofan tare da xagayewa yaje ya shiga mazaunin driver, gwiwa a sage hidayat ta buɗe baya ta shiga sanyi da fitinannen kamshin motar na dukanta, kunce junior da har ya gaji da kukan yayi shiru tayi tare da saka shi a kirjinta, jakukunan kayansu duk sun zubar garin gudu gashi bazata iya ce mishi su je su duba ba ta ya ma zata fara?..
Se a lokacin ta lura da unguwan da suka kawo kansu, wasu irin mahaukatan Gidaje da bata taɓa gani ba take gani har suka isa wani golden Gate me kyau sossai daga motar ta ga ya ɗauki wani abu ya danna se gate ɗin ta zuge da kanta..
Kutsa kan motar yayi ya Parker a tsakankanin wasu mahaukatan range Rovers, fitowa yayi ya zagayo ya buɗewa Aisha tare da riƙe hannunta suka dan yi gaba, se hidayat ma ta sauko cikin mamakin irin kalar shi shi kuma kaman kurma?
Cikin takunshi na xaratan maza yake tafiya hakan yasa hidayat kara sauri har suka isa kofan shiga gidan, kofan karan kanshi abun kallo ne, daga kasa taga ya danna kofar ta kawo wuta ya saka wasu numbers waenda suka bayyana a flat screen na lock É—in se kofar tayi magana tare da buÉ—uwa, karasa turawa yayi ya shige hidayat ta bisu a baya.
Wani kalar haduwar da parlorn ke dashi ya sakata dakatawa gabanta na dukan tara tara, da wa Allah ya HaÉ—ata? Anan parlorn ya saki Aisha yace
"seat"
Yana nuna mata kujera da idanu, kafaÉ—a ta make tana sake rike hannunshi gani take kaman ze gudu ya bar su, hidayat ta matso tace
"Aisha me haka?"
Hannu kawai ya É—an É—aga mata ya sake rike hannun Aishan suka yi wani kofa...
Mintuna biyar suka fito suka haye sama da kallo ta bisu har suka ɓace ta sake dawo da idanunta ta golden color staircase ɗin har ƙasa tana cewa Abba na da kuɗi ashe shi kam ba kuɗi yake dashi ba..
Maganan da aka yi ne ya dawo da ita hankalinta Dukda dai hankalinta rabi na kan Aisha da ya haura da, bata san waye shi ba Dukda tayi trusting É—inshi sede fa a tsorace take dashi Allah ya gani.
"Madam Oga said I should show u a room"
Juyawa tayi ta kalli me maganan namiji ne, binshi a baya tayi zuwa wani ɗaki a nan ƙasa ɗakin babu abunda babu har TV kuma tsare yake a tsabtace.
A ƙasa kan center rug ta zauna se ga mutumin ya sake dawowa da kayan cook ya ajiye mata tray da varieties of Food wadda ba Nigerian dishes ba yace mata
"this is only what we have if u can't eat then I should cook u something different ma"
Kallon tray É—in tayi abinci har kala biyar Dukda ba yawa yawa sede yace bazata iya ci ba? Wacece ita? Uhmm girgiza kai tayi tace
"is ok I will have this"
"thank you ma."
Yace kan ya juya ya fice.
Cin abincin tayi sossai saboda yunwa da dama take ji kaman mene, tana gamawa ta sake zama ta shayar da Junior cikin tausayin rayuwarsu.
Tana nan zaune har wuraren ɗaya taji knock a hankali, miƙewa tayi taje ta buɗe se idanunsu suka sarƙe wuri guda, sassanyar kamshinshi ya daketa, sanye yake da silk riga da wando na bacci cream color sede ba karamin kyau yayi ba, bata san me zata ce ba se ta nemi duburcewa Aisha dake ɗauke a kafaɗanshi ya nuna mata da hannu yace a ƙasaitance
"can I put her on bed?"
Miƙa hannu tayi zata karɓe ta ya mata kallon uku saura kwata ya wuce ta ya nufi gadon ya shimfiɗe ta, ya zo ya wuce ba tare da ya ce mata komai ba.. Se da ya fita ya ja kofan kan ta sauke numfashin da take rike dashi mene? Gani yake bazata iya ɗaukan Aisha ba ko me? Amma lallai mutumin nan ya raina ta.. Taɓe baki tayi ta shige zuwa gadon tana kallon kayan bacci masu taushi da Aishan ke sanye dasu ba karamin kyau ya mata ba, shi kuwa Allah andi inda ya samo shi.
Bayi ta shiga shima tana mamakin kyaun shi, duk abubuwan anfanin ciki bata taɓa gani ba tunda ita ba kallo take ba, kuma gidansu akwai na zamanin sede fa ba irin wannan ba, da ɗan dube dube da taɓe taɓe ta samu ta yi tsarki tare da alwala bata san gabas ba amma ta so tayi shafa'i da wutiri kafin ta kwanta haka dae ta kwantar da Junior akan gadon ta kashe Acn da wutan kan ta kwanta, tunani ta faɗa na yadda zasu yi rayuwa, tana so ta rayu ko don daukar fansar Usman tana so ta zama wani abu ko don su umma, sede ta ina zata fara shine bata sani ba. A wannan dare bacci ɓarawo ne kawai ya ɗauke ta ba wai don tayi niyyar yi ɗin ba.
Da asuba ma se hasashenta tayi tayi sallah, tana nan zaune tana azkar har gari yayi haske, Aisha ta tayar ta kaita bayi tayo fitsari da alwala, kayan ta na jiya bata dawo dasu ba babu ko hijab haka hidayat ta cire nata ta bata ta saka tayi nata sallar.
"Aisha wani hali kuma Kika ɗauko wadda ban koyar dake ba? Kin san shi a ina da zaki maƙale mishi? Sannan wannan bakin ban hana shi zuba zance anyhow ba?"
Da faÉ—a take maganan hakan yasa Aisha fara hawaye.
Tsaki hidayat tayi kan tace
"magana fa nake miki!"
Baya ta ja tace
"Mama Daddy ne fa..!"
"Daddyn gidanku? Kin....."
Shiru tayi sbd knock da aka yi, mikewa tayi ta sanya hijab É—inta ta je ta buÉ—e cook na jiya ne da abinci a tray, ajiyewa yayi da muryarshi na yarbawa yace
"Good morning ma, Ma Oga said I should call Aisha for him"
Tun kan ya rufe baki Aisha tayi waje da gudu, gyaÉ—a kai hidayat tayi tace zaki dawo ki sameni, amsa mishi gaisuwar tayi ya juya ya fita..
Oat ne se bread da kuma omelet, madaran oat É—in a wani karamin jug me garai garai se suger cubes suma a bowl daban, ga fork da spoon da kuma tissue..
Bismillah tayi ta karya, sossai ta koshi kuma taji daaɗin karin junior ta ɗauko ta bashi Nono, tana nan zaune cikin saƙa da warwara ta ji maganan Aisha daga parlor Dukda bata ji nashi ba amma yadda Aishan ke magana ta san dashi take maganan.
Mikewa tayi ta maida waist bag É—inta ta É—aura a kwankwaso ta saka Junior a baya, tare da sanya hijab É—inta suka fito..
Zaune yake yayi relaxing bisa kujera sanye da kananun kaya three quarter da armless black cotton shirt hankalinshi na kan system da yake operating yayinda Aisha dake rike da pop corn tana zaune daga gefenshi tana surutu sede ya gyaÉ—a kai ko yayi murmushi, daidai fitowanta Wayanshi ya dauki ringing.
ÆŠagawa yayi ya kara a kunne yace
"what again?"
Bata ji me aka ce ba ya wani ɓata fuska yace
"wait.. Daadida you kept me at this country for long... Ba zan iya zuwa wani wuri ba kuma yanzu after all I didn't fucking care abt his health or well being..."