← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 74

Sashe 32

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In shaa Allah we will all be happy again..!"
Da kyar ta iya faɗan hakan tana share fuskanta tare da ƙin Kallonshi.

Be fahimci me take nufi da we will da tace ba hakan yasa ya miƙe tsaye yana me ci gaba da kallonta ya kai babban yatsanshi ya sosa giranshi kan ya juya ya fice kawai.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tare da bin bayanshi da kallo har ya fita, mikewa tayi taje toilet ta wanke fuskanta Tare da fitowa ta sauka kasa ta É—auko junior wurin Miss Mary, ta dawo ta karasa HaÉ—a musu table É—in duk fuskanta ba wani fara'a tana jin hayaniyar su daga wani room kuma na gidan dake daura da na Dad É—in nasu bata De leka ba ta koma É—aki tare da shayar da Junior tana Tunanin mafita, ta yadda zata shiga rayuwarshi a hankali ta samu ta karkato da hankalinshi zuwa bautar Allah É—aya.

Har dare yaran basu dawo sun dame ta ba, ko da Aisha ta shigo ce mata tayi Daddy ne ya hana su zuwa kar su takura ta she need a space, murmushi kawai tayi ta shirya yarinyar ta kwanta.

Norah ma ta shigo ta mata good night ta kalleta tace
"Norah hope u prayed?"

Kai Norah ta gyaÉ—a mata tace
"we prayed with Aisha in my room"

Murmushi tayi tace
"ok kiyi adu'a kan ki kwanta"

Tace
"good night miss hidayat!"

Ta juya ta fice.

Kwanan Father biyar ya tafi duk yadda ya so ya sa Raed sallamar Hidayat kin amincewa yayi, dama kuma su abunda basu iya ba takurawa yara Dukda hidayat ta fahimci sarai baya kaunar ta sede tana mishi uzuri don ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar Raed ɗin kuma ta san duk me ƙin ta a bayan umma ne.

Ta kan yi waya da ya hamza akai akai don shi da gaske yake son ta yake kuma yana so ya aureta anytime soon.

Sanadiyar shakuwarsu da Farrah kuwa shine rashin lafiya da tayi, hidayat ta kula da ita sossai wadda ya kawo kusanci tsakaninsu har yarinyar ta fara son ta, ta kuma fahimci daga miss hidayat har Aisha basu da wani nakasu kawai dae dama kishin Aisha take.

Zaune yake a parlor yana aiki a system É—inshi yayinda yaran suke tare da Hidayat a É—aki a irin wannan lokaci ne take musu tarihin annabawa, sanin yana parlor yasa ta fara first move É—inta cikin danne fargabar da ya cika mata ciki tace
"mu yi tarihin nan a parlor"

Aiko da gudu suka fito itama ta fito, kallo É—aya ya musu dukansu ya maida idanunshi kan abunda yake yi suka samu wuri suka zauna tare da saka ta a tsakiya.

Ba tare da ta kalleshi ba ta fara musu da
"yanzu bari mu fara yin tambayoyi akan darasin mu na baya, wa ze gaya min annabawa nawa Allah ya ambaci sunansu a Qur'ani?"

Dukkansu uku suka É—aga hannu ta nuna Farrah.
Da sauri yarinyar tace
"25"

Hidayat tace "Attakbir"
Suka ce "Allahu Akbar"

"To wa ze kira min sunayensu É—aya bayan É—aya?"

Norah ta É—aga hannu ta mike ta fara lissafo su daga kan Annabi Adam (As) har zuwa kan Annabi Muhammad (SAW) zuwa lokacin hankalin Raed ya fara yowa kansu.

Alama he started getting Interest akan abunda suke yi, tace
"to a Tarihin wa muka tsaya ma?"

Suka É—aga hannu ta nuna Aisha.
"Annabi Nuhu(As) inda yayi katoton jirgi saboda tseratar da kanshi da mutanenshi tare da dabbobi daga ruwan É—ufana"

Itama takbir tasa aka mata, daga nan ta cigaba musu da tarihin cikin muryarta me sanyin daaɗi, gabaɗaya hankalinshi ya Mika musu yana jin tarihin kuma yana mamaki don be taɓa ji ba, tana yi har ta zo inda ɗan Annabi Nuhu (As) ya ƙi shiga jirgin yace ze hau saman tsauni ruwa baze same shi ba amma daga karshe shima ya mutu don yana daga cikin taɓaɓɓu.

"Wani darasi kuka koya cikin wannan Tarihi?"

Nora ta É—aga hannu tace
"Ba zaka ɓoyewa Allah ko ka guje mishi ba in de har ya tashi kama ka da laifukanka"

Takbir ta sa aka mata tare da Satan Kallonshi se suka HaÉ—a idanu, fuskewa yayi ya maida kanshi kan system ya cigaba da aikinshi da ya ma manta me yake yi.

Wa'azin Bin othman ta kunna musu a iPad É—in ta inda yake magana akan sallah.

Inda ya É—auko ta da zafinta yake cewa
"Allah madaukakin sarki cikin Suratul Maryam aya ta 59 yana cewa 'se waensu en baya suka zo a bayansu suka tozarta sallah kuma suka bi sha'awowinsu. To da sannu a hankali za'a jefa su cikin gayyah"
Allah SWT ya kuma cewa 'sede wanda ya tuba, kuma yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai' shima cikin Suratul Maryam aya 60."

Babban Sahabin nan ibn Abbas Allah ya qara masa yarda yace "ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba a'a kawai sun kasance sun jinkirta yinta ne akan lokacin ta"
Kunga kenan da wannan fassarar ta ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai waenda suke jinkirta sallah akan lokacinta wato basu yinta se lokacin da suka ga dama wannan aya akan su take, waenda suke wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wanchan ayan ba tana magana ne akan kafirai bane a'a tana magana ne akan waenda suke ikirarin su musulmai ne!
Saed ibnul musayyib imamat-tabi'ina Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wanchan Ayar sai yace
"sune waenda basu yin sallar azahar har se lokacin la'asar, basa yin la'asar har se lokacin magrib basa yin magrib har se lokacin isha kuma ku sani duk wadda ya mutu yana a cikin wanna hali be tuba ba lallai alkawarin Allah a tattare dashi ita ce wutar gayyah!
Wato wani Kwari ne a cikin wutar Jahannama wadda yake da zurfi mai nisa  kuma zasu dinga cin wani mummunan abinci me wari da ɗaci da uquba"

Lokacin magrib da yayi ne ya sakata tsayar da Wa'azin tana me satar kallon shi, tsikar jikinshi tayi wani irin tashi idanunshi sun sauya, saboda yadda bin Othman É—in ke Wa'azin dole In kana cikin masu aikata irin laifin hankalinka ya tashi.

Jin tana cewa yaran suje su yi Sallah ya saka shi ajiye system ɗin shima ya miƙe ya nufi ɗakin shi don yin sallar.

Da kallo ta bishi har ya shige, he's so soft and gentle sannan zama da yayi da su Philip ya hana shi tabuka komai a addininshi wadda ba laifin kowa bane laifin Mahaifinshi ne, kuskuren shi shine da ya girma ya mallaki hankali me yasa be nema sani da kanshi ba? Allah ba ze karɓi hujja akan Babanshi ba sede a karan kanshi.

Tana fata ya sauya a hankali.

Yana shiga yayi alwala ya zo ya gabatar da sallar bayan ya idar ya zauna se ya rasa Adu'ar da ze yi, be san ta yadda ake tuban ba cikin wani irin ciwo da zafin zuciya ya É—aura fuskanshi bisa tafukan hannunshi hawaye masu zafi suka gangaro mishi.

Wasa wasa kullum tare dashi ake jin tarihin annabawa da kuma wa'azuzzuka, wani Wa'azin mufti menk da yayi akan girman uwa da kuma muhimmancin yi mata Adu'a idan ta rasu yasa ya kasa rike hawayen shi wadda a idanun Hidayat suka ganganro da sauri ta kauda kanta itama idanunta na cika da hawaye.

Ita karan kanta in ta ji irin Wa'azin nan se tayi kuka, mahaifiyarta mutuwa tayi sede bata san ta yadda ta same ta ba har ta faɗa hannun Abba, bata taɓa Tunanin ta hanya me kyau aka sameta ba Dukda yadda Abba ke yabon halayyar mahaifiyarta kan rasuwar ta.. Tambayoyi ne Bila adadin a kwakwalwanta sede bata da me amsa mata.

Magananshi ne ya katse mata Tunanin da ta tafi.
"Miss hidayat! Ya ake Tuba?"

Ta kalleshi da kyakyawan idanunta da suka cika da hawaye murmushi na wanzuwa a fuskanta tace
"sharudan tuba guda uku ne, na farko yin nadama bisa abubuwan da ka gabatar na zunubanka.na biyu ɗaura niyyar cewa bazaka sake aikata irin waenan laifukan ba nan gaba a cikin rayuwar ka, abu na uku shine ka dena aikata aikin saɓon nan take ko da ka kasance kana chuɗanya da ita"

Kai yake gyaÉ—awa cikin fahimta tace
"idan da hali ka yawaita ambaton Allah in shaa Allah ze yafe maka duk wani zunubanka"

A hankali yace
"thank you! I want to learn from you"

Da sauri ta kalleshi shima kallonta yake alamun tabbaci, ya sake cewa
"ki faÉ—i ko nawa ne zan biya ina so na koyi abubuwan da kike koyawa yaran nan! I want to pray for my mom"

Wani irin daaÉ—i ne ya rufe ta cikin murmushi da har yake nuna hakwaranta tace
"bana son ko Naira daga gareka, zan yi saboda Allah.. Nima ba kwararriya ba ce koyo nake har yanzu"

Ze yi magana wayanta ta ɗauki ƙara Aisha dake rike dashi tace
"laaa Daddy hamza ne"

Karɓar wayar tayi Dukda yadda take jin kaifin idanunshi kanta hakan be hana ta ɗauka ba tace
"nayi fushi fa!"

Daga ɓangaren shi yace
"Afuwan gimbiya ai in kika yi fushi da ni se in kashe kaina...!"

Dariya sossai tayi kaman gaske, yace
"kina Tunanin wasa ne ko hmm, yanzu ma kasa hakura nayi da kewar ki dake addabata na taso na zo har Paris"

Wara idanunta tayi tace
"Da gaske don Allah?"

Yace
"sa wasa"

Tana dariya ta mike ta shige É—aki suna me cigaba da wayan inda ya tabbatar mata da gaske yana Paris yanzu fa rabon da ya ganta yayi 3months, kuma ita yake son kallo da yamman nan, da kyar ta yarda zasu fita da yaran gabaÉ—aya.

Shiryawa tayi cikin doguwar Abaya black and red ta sa red shoe, tare da riƙe handbag red ta fito tace
"gurls who's in for outing"

Ihu duka suka yi kan suka miƙe da gudu kowa yaje ya fara shiri don ta koya musu saka mayafi duk nata ta babbasu tace su ke rufe kansu in zasu fita.

Tunda ta shige ya jingina da kujera tare da lumshe idanunshi, yana jinsu suna hayaniyarsu har suka fito ta kalleshi tace
"Daddy mun fita"
Chapter 32 · 0% Book details