← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 74

Sashe 69

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka koma gida mood É—inta be dawo daidai ba Dukda yadda yake ta comforting É—inta, bayan sun yi wanka suka kwanta nan ne ya mata ainihin rarrashin da ya kamata suka yi bacci hankali kwance..

Washegari aka kira shi wani meeting na Kano pillars Kaduna, kwana biyu ze yi don ze shiga Abuja sannan ya dawo, ya so tafiya da ita amma ta ƙi.

Gidan Abbanta ta koma, Laure ta nemi Maami da ta bata wasu kudade ta shiga kasuwa don sun riga sun zama kaman dangi babu wani kunya ko nauyi tsakaninsu, aiko ta bata dayawa ba tare da ta tambayeta me zata yi dasu ba.

Sayayya taje ta yi sossai ta fara gyaran hidayat, tun tana kunya har ta sake tana kwasan ilimi wurin Laure, har Maami bata take ta sha, kwana uku kaÉ—ai suka yi gyaran ciki da waje seda hidayat ta sauya, a ranar da ze dawo da safe ummi ta zo ta É—auke ta suka tafi saloon suka wanke kai daga nan suka je gidan kunshi inda aka zuba mata kunshi ja da baki wadda yayi mugun amsar ta, rabon ta da kunshi tun sunan Junior shima ba wani me kyau bane chan.

Ta fito a Amaryar ta se shining take, azahar a gidanta ya mata Baaba Laure na ta tsokanarta ko a jikinta, Maami dae se dariya bata ce musu komai ba.

Ita da ummi da Rashida suka raka ta gidanta, suka yi en goge goge tunda ba datti yayi ba suka HaÉ—a mishi abinci, tuwon semo miyan kubewa da yaji naman rago tayi, rashida tayi rice da vegetable sauce se chicken kebab, ummi kuwa zobo ta hada se ta É—an taya su da ayyukan suka shirya dining dab magrib...

Sallama suka mata dama da motan Rashida suka taho, rashidan ta sauke Ummi kan ta wuce gida.

Bayan sallahn magrib ta shirya cikin Atampha riga da skirt da ya zauna ya fitar da shape É—inta sossai, isha tayi kan tayi light make up ta É—aura dankwalinta É—as.

Kallon kanta take tana murmushi lallai rayuwa wani abu ne me cike da darasi iri iri, a da ina ta san wani wankan jiran miji amma ji ta a yanzu rayuwa babu zagi, ba firgici, ba duka, ba yunwa ba rashin sutura, babu ya zan yi yau da rashin lafiyana da na yarana, rayuwa ta sauya mata zuwa kololuwar daraja cikin dangin ta da jin daaÉ—i.

Sam bata ji shigowarshi ba sbd nisa da tayi cikin Tunanin se ganin mutum tayi tsaye bayan ta mirror, tsorota tayi zata kurma ihu yayi hanzarin zagaye ta ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana dariya.

"Matsoraciya ni ne fa!"
Ajiyar zuciya me karfi ta sauke se ta sauke hannunshi tana tura baki a shagwabe tace
"shine ka tsorata ni..!"

Yace
"Toh kin ɓace a Tunanin da ban san na menene ba har fa sallama nayi baki amsa ba"

Juyowa tayi tana zagaye hannunta a kwankwasonshi ta É—aga kai tana kallon shi sbd tsawo da ya É—ara ta tace
"bani da wani tunani se naka paapi..! I missed you sossai"

A goshi yayi mata peck yana fadada murmushinshi yace
"missed you more baby gurl"

Kan tayi wani magana ya riƙe bakinta cikin nashi, da kyar ta dakatar dashi duk suna sauke numfashi tace
"mu je kayi wanka ka ci abinci"

Kallon lips ɗinta kaɗai yake a shagwaɓe..

Dariya take mishi ganin abunda yake yi kaman wadda ta hana shi wani abinci me daaɗi, ƙara rungumota yayi ya sake fara kissing ɗinta yana murmuring
"bari nayi maganin me mini dariya..."

Janyewa tayi tana sake dariya, yana jefa mata rikitaccen kallon yace
"Baby gurl I can't stop myself from kissing your lips...cause you are the reason why I turned so romantic"

Jan shi tayi zuwa toilet tana blushing,
"ni de ba ruwana! yi wanka abinci na jiranka"

Yace
"bazaki taya ni ba?"

KafaÉ—a ta make tace
"so kake in ɓata wankan da ko nayi kyau baka kai ga cewa ba?"

Wara idanu yayi ze yi magana tayi saurin rufe toilet É—in tana dariya.

Ɗakin shi ta koma ta ɗauko mai kananun kaya da armless abubuwan da yafi sakawa, ta feshe su da turarukan shi kan ta kai mai ɗakinta ta sauka ƙasa gabaɗaya ta zauna.

Saukowanshi yasa ta É—aga kai tana Kallonshi suka sakarwa juna murmushi, a nan tsakar parlorn ta shirya mai abinci don ita bata cika son zaman dining ba ko don bata saba chan bane oho, tana zuba abincin yana bin hannayenta da kallo seda ta gama kan ya riko hannayen yace

"hannunki yayi kyau sossai baby gurl I love this..."
Yayi maganan yana bin zanen lallen da yatsanshi wadda ke tada mata tsikar jiki, yace
"zaki dinga yi min? Ban taɓa sanin suna da kyau haka ba"

Kai ta gyaÉ—a tace
"amma fa in mun koma Paris da wuya a samu wurin yi"

Yace
"and ur dressing ban san haka kayan Hausawa ke da kyau ba, u look so breathtaking die hard I love you..!"

Murmushi kawai ta saki tace
"ga wani abincin Hausawan ma I know bazaka iya tuna Last da ka ci ba I cooked it myself I promise you will love it"

Yaukin kubewan yake kallo yana ɓata fuska, da kanta ta wanke hannu ta ke yankan tuwon tana bashi, ba karya yayi daaɗi sossai da kuma ya cinye Leda biyu se yaji ya koshi fiye da yadda yake koshi da abinciccikan turawa, zobo ta bashi ya sha yana lumshe idanu yace
"amma fa Daadida na cuta na, bata taɓa min tayin irin abubuwan ba when ever I visited her"

Yayi maganan yana tura baki, dariya take yi tana cewa se ta faɗa mata santi ya saka yana mata sharri kilan da ta bashi ya ƙi ci ne...yana ce mata yanzu ma ya baro ta asibiti se Wayanshi ya katse shi.

Picking yayi da "hello!"
Da sauri ya miƙe tsaye yana cewa
"What???"

*****

Tun da Hidayat suka Barsu anan sun jima sossai zaune suna Tunanin abubuwan da suka aikata a rayuwa, barinma umma da Yusuf in suka tuna abunda suka aikata se su ji kaman su kashe kawunansu, basu taɓa sanin rayuwa zata juye musu haka ba.

Se yanzu Allah ya ɗaura mishi tsananin ƙaunan yaranshi sede kuma sun riga sun mishi nisa babu yadda ya iya, da kyar ya iya maida kanshi gida ya rufe kanshi a ɗakin matarshi da ta gudu ta Barsu bayan ta gama dasu.

Hannunshi da yake ji kaman ana yagalgalawa don ciwo yake kallo yana maimaita kalaman Hidayat, yayi karatu ya san me hannunka me sanda yake nufi, shin me anfanin rayuwarshi a yanzu? Yayiwa Allah laifuka masu yawan gaske, yana neman sassauci wadda tuba yayi kaɗan, Allah ya riga ya yanke dukkanin hukuncin laifukan shi shin ze zauna ya cigaba da ganin iftila'i kala kala ko ze nemawa kanshi sassauci wurin karɓar hukuncin da ta dace?

Kwana yayi be runtsa ba, da sassafe ya miƙe ya fice daga gidan ba tare da yacewa kowa komai ba.

Ko da ya isa inda za shi seda yayi jiran awa biyu kan aka buɗe, ya miƙe ya shiga.

"Don Allah alkali nake nema?"

Mutumin ya kalleshi yace
"ko lafiya kake nemanshi?"

Yace
"abu me matukar muhimmanci ne ya kawo ni"

Yace
"ka É—an yi hakuri yanzu zaka ga ya shigo"

Zama ya sake yi minti minti se su HaÉ—a idanu da secretary É—in be damu ba, illa kawai zuciyarshi da baya jin daaÉ—in ta ko kaÉ—an.

Chan se ga alkalin ya iso bayan wani É—an lokaci yayi umarni da a shigar da Yusuf, bayan ya shiga ya zauna suka gaisa ya tambayeshi me ke tafe dashi?

"Na kawo kaina ne a yanke min hukuncin laifukana bisa tsarin shari'ar musulunci ko zan samu rabauta ranar gobe, nayi abubuwa masu yawa wadda bana Tunanin a yanzu in na mutu zan ji ko da kamshin aljanna ne... Ka taimakeni yallaɓai"

Girgiza kai alkalin yake yi kwarai Allah na son Yusuf da tuba da har yayi wannan tunani
"ko zan so sanin menene ka aikata haka?"

Cikin kuka yace
"na aikata zina da matan da ba zan iya kirgawa ba, abu mafi girma da na aikata shine kisan kai! Na kashe ɗana na cikina da hannayena saboda ya karewa mahaifiyarshi dukan kawo wuƙa da nake mata!!"

Salati alkalin nan ya saki ya sake sakewa, a hankali Yusuf ya dinga bashi tarihin rayuwarshi da Hidayat har karshe, Seda alkalin nan ya zub da hawaye, shiru ya kasa magana.

"Ka zalunce wannan baiwar Allah, ka cutar da rayuwarta, lallai lallai kan kowani hukunci da za'a yanke maka ka fara neman yafiyanta, Allah kan yafe laifin dake tsakanin shi da bawa amma baya yafe laifin tsakanin mutum da mutum wannan tsakaninku ne"

Yace
"a yanzu babu inda zan iya ganin hidayat in nemi yafiyar ta, ina so a sadda za'a yanke min hukunci in yi video sakona ya isa zuwa gareta watakila bayan raina zata yafe min, ina kuma so labari na ya zama izina ga mutane, a lokacin da ka samu dama kayi aiki me kyau da ita kan ta kubce maka wallahi wallahi tsakani da Allah na fara son hidayat sede ganin bata da galihu bata da gata sheÉ—an yayi nasara a kaina na cutar da ita na san babu wadda take dashi a duniya da ze kwantar mata enci na manta Allahn da yayini me kuÉ—i da dangi itama shine yayi ta..."

Ajiye shi aka yi, bayan dogon zama tsakanin manyan malamai aka yanke mishi hukuncin bulala na laifin zina se kisa ta hanyar rataya bisa kisan Usman da yayi, yayi kuka sossai a sadda ya ji hukuncin wadda aka bashi kwana biyu ya gyara tsakanin shi da Allah ya tuba iya yadda ze iya kan kwana biyu ya cika😭😭

             DIDDIGAR ƘAYA
        (Mai wuyar Tsincewa)

Gureenjo🥰😍

Paid book
300

Tsokaci/Dandano

Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.
Chapter 69 · 0% Book details