Sashe 61
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasa jurewa hidayat tayi ita kaÉ—ai ta san me take ji a gabaÉ—aya ilahirin jikinta, yau mahaifiyarta ce gabanta bata mutu ba ashe, me yasa Abba ya ce mata ta mutu? Me yasa yayi mata karya abunda ba É—abi'arshi ba? Taya aka yi ta barta a zani ta tafi bayan ta san zalunci irin na umma??? Me yasa komai ya faru a haka??
Kasa ɗaukarta kafafunta suka yi ta tafi suuu zata faɗi daidai lokacin Aisha ta isota ta taro ta suka yi ƙasa a tare suna masu kallon juna ido cikin ido, kaman an ce kyatt suka wani rungumar juna suna fashewa da kuka me tsananin cin rai da taɓa zuciya.....
#Vote
#share
#comment
        🖤Gureenjo🖤
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763
AND ON AREWA BOOKS @gureenjo
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*PAGE 40*
*FREE BOOK*
Shiru parlorn ya ɗauka Aisha na riƙe da Hidayat har lokacin ta ɗaura kanta bisa cinyar ta tana shafawa, Allah kaɗai ya san me ke tafiya cikin ran Raed don gabaɗaya be taɓa sanin menene ainihin ciwo a zuciya ba seda yaga irin kalar kukan da Hidayat take yi, gabaɗaya he wasn't his self yana riƙe da Junior da ya fara rikici, hamza na zaune gefen Abba da yayi shiru kawai amma shi kaɗai ya san me ke tafiya a zuciyarshi.
Daadida ma na zaune gefenta buzayen nan ne namijin yana riƙe da Hajiya da take ta so ta fisge, gyaran murya mahaifin Rashida yayi yace
"Toh Alhamdulillah aka ce komai yayi farko zae yi ƙarshe, sannan duk nisan jifa ƙasa zata dawo, abubuwa da dama sun faru wadda kawunanmu duka suka kasance cikin duhu Dulum tunda ga wacce aka tabbatar da mutuwar ta zaune a gabanmu, sannan ga hajiya dake wasu maganganu kaman wacce ta samu taɓuwar kwakwalwa, na tabbatar kowa a nan yana son sanin me ya faru? Taya abubuwa suka kasance a haka? Yaya kowannenku yayi rayuwa?"
Shiru ya É—an yi kan ya cigaba
"Aisha! An auro ki an raboki da iyaye da en uwanki aka tsallake gari ya gari aka kawo ki har garin Kano, aka kuma damka amanarki hannun Hajiya Balaraba, ta karɓa hannu bibbiyu wadda seda kowa yayi sha'awar zamanku ake yiwa Usman dacen samun maatan kwarai kwatsam se kuma abubuwa suka juye, shin me ya faru?"
Ba tare da ta kalli hajiya balaraba ba tace hawayenta ya kasa tsayuwa
"Kaman yadda duk kuka sani sunana Aisha haifaffiyar garin mambila na jahar Taraba, na taso nayi rayuwa da iyaye na kaɗai ba tare da wani ilimi akan zama da kishiya ko kishi ba, ko da aka kawo ni garin Kano wallahi da zuciya ɗaya na shiga gidan yaya balaraba, a yadda ta karɓeni ta riƙe ni kaman ƙanwarta kowa se yayi sha'awar zaman mu, da ita zamana lafiya amma da mijina gashinan.... Mun Rayu cikin wannan aure da daaɗi ba daaɗi, dukda son juna da muke, matsalar da muka fara fuskanta shine a duk sadda ranar kwana na ya zagayo jini ne ze balle min baze tafi ba har se ya bar wurina ya koma wurin balaraba, tun bamu damuwa har abun ya zo ya fara damun mu saboda ina neman shekara da aure babu abunda ya taɓa shiga tsakaninmu.
Da farko iyayena na so samu da matsalar, don damuwar har ta saka ni fara rama Dukda Alhj be taɓa nuna damuwa ba yana hakuri yana kuma Adu'a nima yana kokarin kwantar min da hankali da cewa lafiya ta ƙalau Dukda kankatar shekaruna na san ba lafiya ba, ranan muna zaune da Yaya balaraba se take tambaya ta..
"Ni kam Aisha lafiyanki kuwa? Kwanan nan fa se rama kike tayi ko de mun kusa jin kukan jinjiri ne kike ɓoye min?"
Nayi murmushi nace
"wani irin kukan jinjiri bayan abunda ya dame mu ya damemu"
Tace
"ban gane ba?"
Nan na faɗa mata duk abunda ke faruwa, ban san kowa a Kano ba, bani da ƙawa bayan mahaifiyata a lokacin kuma sede ziyara, basu da waya a gida bare in faɗa mata damuwata ta waya, na ɗauki dukkanin yarda da amana na baiwa yaya balaraba, tashin hankalin da ta shiga a sadda taji wannan labari ko Alhj se haka, tayi ta damuwa tana maimaita maganan bayan kwana biyu ta nemi mu je wurin wani malami ya duba matsalar kilan mutanen ɓoye ne.
Ban yi mata musu ba na tambayi Alhj, ze nuna rashin amincewa na saka mishi rikici don a ganina ba shine a cikin matsalar ba, Allah kaÉ—ai ya san irin azabar ciwon mara da nake sha a duk bayan kwana biyu, haka ya kyale mu muka tafi malamin nan ya tabbatarmin da matsalar sheÉ—anu ne ga abunda za'a kawo a fara jinya.
Seda nayi jinyar wata ɗaya zuwa biyu kan jinin ya fara ɗaukewa, a sannan hankalina ya fara kwanciya don ko ze zo bayan kwana biyun baya ciwo kaman baya, a sadda na fara murnan samun sauƙi a sannan Alhj ya ƙaurace min, baya cin abincina, baya kwana ɗakina magana wannan in ze Haɗa mu sede ya faɗawa yaya ta faɗa min, ita na samu da wannan matsalar ma ina kuka nake gayamata ga abunda ke faruwa tsakanina da Alhj, da kanta ta ajiye mu don yi mana sulhu buɗan bakinshi se cewa yayi na zama ƙazamiya komai nawa yana wari shiyasa baya son zama kusa dani da mu'amalantata don ko abincina kyama yake bashi.
Nayi kuka sossai na shiga damuwa, se in yi wanka sau biyar a rana, nayi ta yawon tambayar Yaya ko tana jin wari jikina se tace ita kam bata ji komai ba, a lokacin Hamza na ƙarami sossai dashi nake yini nake kwana yana debe min kewa gabaɗaya na barwa Yaya Alhj ina me cigaba da Adu'ar samun sauƙi wurin ubangiji ina kuma yin maganin wannan malami da yaya ta kaini wurinshi.
A taƙaice wannan matsala seda ta kaimu kusan watanni takwas, matar abokin Alhaji ita ce mace na biyu da take kaman ƙawa a gareni a Kano ta girme mini don zata yi sa'a da balaraba hakan yasa bana iya buɗe mata cikina gabaɗaya, har na je gida na dawo babu wadda ya san ina cikin damuwa saboda ganin irin farin cikin ganina da su Mama suka yi yasa na kasa faɗa musu matsala ta kar na saka su cikin damuwa.
Bayan na dawo ne na kai mata ziyarar wani ɓari da tayi, nan take tambaya ta ni kam shiru ba ciki ba labari? har ga Allah ban so fitar mata da sirrin aurena ba sede abun na damuna, nan na bata labarin komai, bani da maraba da naani a gidan Alhj Usman, don komai na hamza a wurina yake, haka girki daga nawa har na Yaya ni nake yi ita ta kwana da miji.
Salati ta saki ta fara yi min faÉ—a akan kishiya ko ya take ka ji tsoronta, ban hanaki zama da kishiyarki lafiya kuma da zuciya É—aya ba sede fa ki kiyaye ki zama me lura da hange, ni ba son raba zaman lafiyanku nake ba sede akwai Ayar tambaya me girma akan Hajiya Balaraba.
Tashin farko na nuna mata ban yarda ba, don har ga Allah duk wadda ze zagi ko ya kushe yaya har raina haushinshi nake ji, duk yadda ta so fahimtar dani na kasa fahimta se ta koma ta bayan fage, mahaifinta malami ne ta mishi bayanin komai ya neme ya ganni, roko na ta dinga yi akan kar na faÉ—awa Yaya haka ban faÉ—a mata ba na fita muka je.
Adu'o'i da tofi ya bani da wasu magunguna akan in na fara sati biyu kar in fita ko ina, hayaƙi kuma in yi tayi a ɗakina, sossai ruwan da ya bani na sha ya taimaka mini, inda na dawo gida nake magungunan, kaman kuwa an toshe min baki ban fadawa yayar ba se bayan da na gama maganin ranan da rana muna zaune a babban parlor se ga Alhj.
Da sauri na tashi zan shige É—aki don kusan haka zaman namu yake a sannan yayi saurin cewa
"Aisha! Ina zaki daga shigowa ta?"
Daga ni har yaya da mamaki muka tsaya muna Kallonshi.
Yace
"kawo min ruwa pls"
Na wuce kitchen na Haɗo mishi ruwa na kawo ya karɓa yayi godiya yana me kallona, zan tafi yasa na zauna hira suke da yaya ya kan sako ni ciki Dukda shakkar amsa shi da nake ji don ban manta wahalar da na sha a watannin daga gareshi ba, ko hanya muka Haɗa bani da maraba da kashi a wurinshi.
A ranar a tare muka ci abincin rana da yamma ya fita damu shopping, yana ta kokarin janyo ni jiki yayinda yaya take nan shiru kaman ruwa ya cinye ta.
Bayan mun dawo a lokacin ma bayan isha'i se gani nayi Alhaji yayi É—aki na, da lallami yasa na saki jiki yayi ta min rantsuwar be san meyasa yayi min abunda yayi ba, tsakanin miji da mata se Allah, se a ranar Allah ya nufi tabbatuwar aurenmu bayan kusan shekara biyu.
Washegari da Yaya ta fahimta se ta ɗauke min wuta, gashi Alhj se riritani yake yana lallaɓani, in na mata magana se ta share ni na sameta har ɗaki nake tambayar ta lafiya? Tace
"ban san me kika daukeni ba Aisha! Ni kam a matsayin ƙanwa na dauke ki ashe har zaki iya tsallakeni ki je wurin wata neman taimako? Yanzu kin bata aikin malaminmu na farko kuma ya ce akwai matsala don aljanun da ya raba ki dasu na farko zasu iya dawowa"
Na tsorata nayi ta bata hakuri tace ba ruwanta sede mu koma wurin malamin, duk a zatona hajiya Adama(matar abokin Alhj) ita ta gayamata.