Sashe 56
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace
"kika sake rainamin hankali wallahi zan bajar dake wato daga leke har kin karance sunanta kin riƙe daram a kwanyar ki! Ka ji wani sharfadina...!"
Jikinta har yana tsuma tace
"don Allah ka bani wayan nan yanzu zan kawo maka!"
Bata jira Cewar shi ba ta fusge tayi cikin gida hankali a tashe cikin wani irin yanayi tana kwala kiran sunan umma, tsallake Yusuf dake zaune bisa taburma hannunshi É—aya a wani irin kwarmaÉ—e da alamun wani abu ne ya same shi se kudaje ke bi yama yama tayi kan Umma..
"Umma....ummaaaa hidayat fa! Kalli ki gani wallahi hidayat ce! Wai ta auri babban ɗan kwallo ba'a ƙasar nan ma suke rayuwa ba yanzu ma suna Saudia a chan aka ɗaura musu aure..... Don Allah umma ki ce min ba ita ba ce..... Umma ki ce min rayuwarta tafi namu lalacewa.... Wayyoooo"
Kuka Surayya ke yi kaman wacce uwarta ta mutu na hassada da baƙin ciki kiri kiri, umma jiki na mazari ta fisge wayan tana saka idanu aiko tayi baya zata hantsula da azama gayen da ya biyo bayan Surayya ya riƙe Wayanshi yace
"ka ji min tsohuwa zata yi min tsalalar tsiya, babu a Hausee..!" Yadda ya kira house É—in se ka sha dariya har cikin ka ya kulle, amma su kam suna cikin wani irin alhini wadda ya fi karfin dariya.
Da sauri Yusuf ya miƙa hannu ya karɓi wayan, kwarai ya gane Hidayat don tarrr kyakyawar fuskanta ya fito cikin wani army green designer jalbab me matukar kyau.
Lallai yana ganin hotunan wannan É—an kwallon me kama da Larabawa, a ina hidayat ta samo shi? Taya aka yi rayuwarta ta samu wannan cigaba?
Har gayen yayi gaba da Wayanshi babu wadda ya iya motsawa a cikinsu, Surayya kuka wiwi umma ta Daskare.
"Yanzu yarinyar nan tayi wannan kuÉ—i ta manta da asalinta? Ashe haka amana yace?"
Umma ta iya fusgo maganan da bata san ma me take nufi ba, kaman ba ita ce tayiwa hidayat kora me muni da É—anyen goyo tace wadda ya HaÉ—a ya raba kuma babu gado bare a samu matsuguni ba.
Surayya tace
"Umma in ita bazata iya neman mu ba saboda babu Abba mu mu neme ta"
Se a lokacin yusuf ya gyara rufan hannunshi yana kade kuda yace
"ke kin san waye Moh'd Raed kuwa? Ta ina zamu fara ganin iyalinshi? Ni yarana ma da ban san a wani hali suke ba!"
Surayya tace
"kaman gaske yaran ka damu dasu kaima! Karka manta dae mu da kai kar ta san kar ne, ya Yusuf ko sunan ƙaramin baka sani ba... Kana nan fatalwar Usman na maka yawo har yayi sanadiyar mota tabi ta kan hannunka baka daddara ba...!"
Hannu ya kai ze Mareta ta kauce, nan kowa yayi zurfi cikin Tunanin yadda zasu ga Hidayat. Har yanzu babu me kaunar hidayat a cikinsu sede ganinta da cigaba ya kwadaita musu kusantarta ko zasu fita daga wannan kangi da suke ciki sun manta a baya da suke da wadata gidansu bashi da maraba da Kangin bauta ga Hidayat.. Ita umma yafiyar ta take so su nema ko zasu ga da kyau rayuwarsu ta gama taɓarɓarewa ta tabbatar ko kuɗin ta basu ta Barsu dashi ba ze anfanesu ba in bata yafe musu ba barin ma ita da Yusuf.
****
"Assalamu Alaikum"
Hidayat ta shigo gidan da disashiyar muryarta.
Mahaifiyar ummi dake zaune tana tatar kamu ta amsa tana kallonta, fuskanta a rufe yake rabi sede daga Fararen yatsunta zuwa kalar yadin hijab ɗinta da flat designers da suke kafafunta na Findi mahaifiyar ummi ta san ba irin baƙin su bane.
"Baiwar Allah sannu da zuwa!"
Da gudu hidayat ta karasa ta zube gwiwowinta kasa tare da É—aura fuskanta kan cinyar mahaifiyar Ummin tana kuka tace
"Mama!"
Kamshin ta da ya daki maman ne ya É—an sakata jan lokaci kan ta É—ago ta tana shirin magana suka HaÉ—a idanu, gabaÉ—aya idanunta ta waro waje..
"Hidayat!!! Ummmiii! Ummmiii zoooo hidayat! Ga Hidayat!!"
Da gudu ummi ta fito daga parlornsu tana cewa
"Mama hidayat kike kira kaman?"
Ai suna hada idanu suka rukunkume juna suna kukan yaushe gamo, da kyar suka tsagaita kukan ummi ta ja hidayat parlor suka zauna ummi na cewa
"Hidayat ina kika shiga haka a duniya? Nayi nema har na gaji nayi kuka har na gaji, nayi ta sadaka da Adu'ar duk inda kike Allah ubangiji ya dafa miki yayi riko da hannayen ki, hidayat misalta tashin hankalin da na shiga a tsawon lokacin nan da na rasa ki ba karamin abu bane"
Hidayat ta É—ago ta buÉ—e baki zata yi magana kamshin mouth wash É—inta Seda ya saka ummi lumshe idanu, hakwaranta farare Kal a jere ga wani na Makkah guda É—aya dake kyalli, gabanta ne ya fadi se a lokacin ta lura da irin kyaun da Hidayat tayi, hannunta dake rike da na Hidayat É—in ta motsa wani irin taushin hannun yasa tace..
"Na shiga uku ni ummi! Allah yasa su umma basu yi nasarar wargaza miki rayuwa ba! Hidayat don Allah ki yi min magana ko hankalina ze kwanta! Ina Aisha? Ina junior?"
A rikice ummi take.
Hidayat tace
"Ki kwantar da hankalinki ummi, umma basu yi nasarar wargaza min rayuwa ba, ummi na dawo a gareki a yanzu da aure me ƙima da mutunci bisa kaina wadda aka ɗaura shi a cikin masallacin fiyayyen halitta shima kuma ya zama shaida... Na dawo a gareki a yanzu da auren ɗan uwana wadda muke ƴar goggo da ɗan kawu.... Ummi yanzu maganar da nake miki mahaifina uba a gareni na bari rai a hannun Allah na taho nan.... Ummi ki bani shawara mijina baya ƙasar ko izinin fitanshi ban nema ba na taho nan..! Ya zan yi?"
Ummi tace
"duk ban gane ba hidayat? Taya hakan ta kasance? Ya aka yi duk waennan abubuwan suka faru ga rayuwarki alhali kin bar gaban Yusuf ba cikin cikakken natsuwa ba? Hidayat me yasa baki zo nan ba a sadda Yusuf ya sake ki umma tayi miki korar kare? Duk na samu labari ne saboda na koma muka yi kaca kaca da Yusuf anan na san ya sake ki na je gidan umma ma ba kunya suka bani labarin cin kashin da suka miki! Da kika fita ina kika yi?"
A hankali hidayat ta fara bata labarin abubuwan da suka faru, idan ta zo wurin Raed bata sanin sadda siririn murmushi kan subuce mata barin ma irin ƙauna da soyayyar da ya nuna mata na hakika, tana zuwa na yau ta fashe da kuka yayinda ummi ta rukunkumeta tana kukan farin ciki.
"Amma hidayat ban san ke baki aiki da hankali ba se yau! Tashi oya muje na san duk inda suke hankalinsu a tashe yake! Hidayat ina hankalinki? Ki saurare mahaifinki mana ki ji uzurinshi kan ki yanke mai hukunci? Ko kin manta duk wannan abunda ya faru already a rubuce yake? Kaddarar ki ce a haka kuma dole ki karɓeta a haka ko baki so! Karki yi watsi da ni'imar ubangiji mana hidaya idan kika duba yadda rayuwarki ta koma yanzu, idan kika duba irin kalar mijin da Allah ya miki zaɓi, idan kika duba ƴaƴan da Allah ya maye miki gurbin Usman dasu ai se ki gode mishi da ni'imominshi... Ke fa kika ce kin yi Adu'ar bayyanar ahalinki a ɗakin Allah inda ba'a mai da Adu'ar bawa, me yasa da Allah ya amsa miki Adu'ar zaki juya baya a gareshi Kiki farin ciki?"
Kai hidayat ke gyaÉ—awa hakane a ko yaushe ummi daban ce a rayuwarta, hannu ummi ta sa ta share mata hawayen dake zuba tace
"a lokacin da na bar gidanki a hanya ta ta zuwa nan aka sace min waya a adaidaita ko da naje welcome back kuma sun ce ba ni nayi register Sim É—in ba so ba ze yiwu ayi welcome back ba, ni duk a tunani kina chan gidanki se ranar weekend na shirya na je, a nan ne nake samun mummunar labari makotanki karan kansu sun shiga matukar damuwa da tashin hankalin wannan abu, ko da zanje wurin umma tare muka je da su uku sede duk hankali tashe rai ba daaÉ—i muka baro unguwar, na neme ki har a gidan redio sede shiru Baba yace in hakura in biki da Adu'a, ko wani juma'a sena yi sadakar in kina raye Allah ya bayyana min ke...! Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah na gode maka da wannan sauyin rayuwa naki"
Tana kai nan ta sake rungumarta, Mama ce ta shigo tace
"ya fa kamata ku tashi kuyi sallolin da suka wuce ku ku ci abinci haka nan"
Duba time ummi tayi se taga almost 11 na dare, ita kanta hidayat se lokacin ta lura se hankalinta ya tashi ta tabbatar yaranta na chan hankalinsu a tashe basu ganta ba, tun biyar da wani abu ta shigo gidan.
Mikewa tayi tace
"Mama zan wuce ni kam"
Mama tace
"A'a hidayat, kika san kan ki isa wani abu ya same ki ba fata ba baki sauke hakkin Allah ba? Ko bazaki ci komai ba kiyi sallah kan ki É—au hanya"
Haka dole tayi alwala ta fara gabatar da sallah, da ta idar ma sha É—aya da rabi na dare, Gashi baban su ummi yayi tafiya bare ya maidata a machine nashi, damuwanta yaran hankalinsu a tashe yake ta sani Daadida ma duk yadda aka yi yanzu tana cikin tashin hankalin rashin ganinta, tayi wauta ko waya bata Riko ba...
Wayan ummi ta karɓa ta saka layinta na Nigeria ta danna kira, ringing na farko aka ɗaga wani mummunan faɗuwa gabanta yayi jin husky voice ɗinshi yace a hargitse...
"WHERE ARE YHU??"
#Vote
#share
#comment
       🖤Gureenjoh🖤
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرØÙ…Ù† الرØÙŠÙ…
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763
AND ON AREWA BOOKS @gureenjo
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*PAGE 37*
*FREE BOOK*