← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 74

Sashe 72

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zata yi magana hidayat ta gwabe mata baki saboda haushi da ya kusa kashe ta ita zata yi fooling ta taho night club? Allah kaÉ—ai ya san me yaran turawan nan suka koyamata.

Zuwan Raed ne ya katse su ganin shigan jikin Norah da kuma yadda ran Hidayat ke ɓace ya san akwai matsala, kafadan Norah ya riƙe yake cewa
"are you OK? Me yasa take kuka?"

Ya jefawa Hidayat maganan yana sake kallon bakinta da har ya É—an yi jini.

            DIDDIGAR ƘAYA
(Mai wuyar Tsincewa)

Gureenjo🥰😍

Paid book
300

Tsokaci/Dandano

Wani mahaukacin gigitaccen Marin da yake barazanar ɗauke mata ji da gani ya sauke mata wadda seda ta kai ƙasa dafe da kuncinta hawaye na aikin ambaliya kaman an buɗe lalataccen famfo bisa saman fuskanta.

"Rufe min baki! Shashasha,munafuka,marar hankali... Har kina Tunanin akwai wani banzan dalilinki da ze hana wannan É—aurin auren? Ke har kina da bakin ja da wannan auren? Wato so kike ki nunawa duniya cewa ya tabbata ke É—in tantiriyar marar kunya ce ko? Toh bari ki ji in faÉ—a miki ko da aljani ne be isa hana wannan aure ba idan har ba shine ya zo yace ya fasa ba kin yi kaÉ—an ki hana wannan aure!"

Cikin matsanancin kuka me taɓa zuciya wadda be daaɗa shi me sauraron da ƙasa ba don ko a jikinshi ta fara cewa
"Na yarda baba Alhj....a ɗaura aurena jibi, na yarda ka zaɓa min miji a ko ina...! Ko yaya yake... Ko mai talauci ko nakasarsa,komai tsufa ko yarantarsa..! Komai fari ko baƙin halin sa zan zauna dashi akan da ku Haɗa aurena da Wannan azzalumin. Don Allah Baba ka taimakeni.."
Ta karashe da kuka sossai har tana shiÉ—ewa.

Wani mugun kallo ya watsa mata yace
"ko mutuwa zaki yi se an É—aura aurenki a jibi Da FAIZAN! Kuma ko me ze miki se kin zauna dashi wawuya, butulu baki isa kin sa na yi jayayya da yayana akan abunda yake taimakona ze yi ba! Na tabbatar shi karan kanshi Faizan É—in ba son auren tantiyar Æ´ar iska irin ki yake ba..!"

Wani irin karyayyen kallo take yiwa mahaifin nata, kai tsaye yake kiranta Æ´ar iska a gaban idanunta, wani irin kuka me cin rai take yi ba laifin kowa bane laifin su ne iyayen nata, su suka jefa ta duk wani rayuwa da take ciki a yanzu amma taya zasu kasa yi mata adalci su HaÉ—a ta da wadda kap duniya babu wadda ta tsana irin shi? Wani irin zama zasu yi? Shima fa ya tsane ta fiye da yadda ita take tsanar shi.

Da gudu ta miƙe ta fice tana me tsananta kukanta, ba tare da ta damu da dumbin jama'ar da suka taru a gidan don sheda wannan mummunar kaddarar baƙin auren ba kaman yadda ta sa mishi suna, a kan cinyar mahaifiyarta ta zube tana kuka a ruɗe

"Ammi! Baba Alhj basa ƙauna ta Ammi, Ammi don Allah kiyi wani abu kar su kasheni tun kwana na be ƙare ba! Ammi wallahi na tsane sa Ammi bana sonsa bana ƙaunarsa, ki tausaya min Ammi..!"
Shafa kanta Ammin take cikin baƙin cikin da yake daskare bisa zuciyarta, in akwai wadda ta tsana a rayuwar nan To mahaifiyar Faizan da Mahaifinshi me ze sa komai na rayuwarta da ahalinta se da umarnin su za'a aiwatar?

Allah kaÉ—ai ya san irin zaman da suke yanzu da mai gidanta duk saboda su, me yasa ne ita bata da Æ´anci a nata gidan da mijinta? Me suka fi su? KuÉ—i ko suna? Me yasa Sulaiman a ko yaushe umarnin Prof shine gaba da na kowa? Ina soyayyar da Jaddah ke ikirarin tana yiwa Fauziyya É—in?

"Fauziyya kiyi haƙuri, duk yadda zan yi wurin ganin na hana aiwatuwar wannan aure na yi sede babu nasara sakamakon hakan ma aurena rawa yake, ki daure zuciyarki ki bari ayi auren amma ba zan taɓa yi miki dole ki zauna ko kiyi biyayya ba... Wannan karo ma Aisha tayi nasara a kaina"

Sakin Ammi tayi ta sake mikewa ta fice da gudu, idanunta a rufe suke mafita kawai take nema, sashen Jaddah ta shiga a gigice Sam bata lura da mutanen da suke wurin ba, ta fara cewa

"Zan kashe kaina! Wallahi tallahi zan kashe kaina.... Duk ranar da aka yi Adu'ar aurena da Wannan azzalumin ina me rantsuwa zan mutu! Sede a kai gawata É—akin sa.. Ku gafarceni Jaddah..."

Natsatsiyar muryar da take bayyana fushi da wani irin ciwo ne ta ratsa kunnuwanta, muryar da ta tsana fiye da na kowa da komai a duniya, sautin da take jinshi kaman saukar aradu a kunnuwanta da ma gangar jikinta...

"Ka ji ba Baba? Ban taɓa yi muku jayayya ba se a wannan karo, baba bana fatan Haɗa jini da fasiƙa...! Idan har aka ɗaura wannan aure an cutar da ni da iyalina..."
Sauƙar gigitaccen mari ne ya hana shi ƙarasawa.

Jajayen idanunshi ya ɗago ya zuba mata na mintuna kan ya miƙe a zuciye kaman kububuwa ya fice....

"Menene hujjar ki na ƙin wannan aure?"
Jaddah ta jefa mata tambayar karon farko tana kallonta.

Shiru tayi tana kuka sossai don Kalmar fasiƙa da ya jefe ta dashi har tsakiyar zuciyarta take jin zafi da raɗaɗin shi.

"Baki da hujja? To fitar min daga É—aki"
Kallon ban yarda Jaddahta bace a zaune anan take jefa mata kan ta yi baya baya ta fice da sauri tana kuka.

Dafe kai Jaddah tayi cikin jin ciwon wannan abubuwa da suke faruwa a cikin zuri'ar ta...

***Shin ya kuka gani? Menene hasashenku kan wannan sabon littafi? Su waye ne waennan ahali? Me yake faruwa a cikin wannan gida? Menene musababbin tsanar da suke yiwa juna? Meyasa kowa ya buɗe baki da kalmar fasiƙa yake jefan Fauxa? Wani irin zama zasu yi bayan Haɗa Wuta da Auduga inuwa guda? Akwai fa'ida a wannan aure ko babu? Za'a daura ko kuwa?

Duk ku biyo ni a cikin wannan littafi nawa me suna DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa)
Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank

Karku sake a baku labari.

🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...
   (DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

                      *PAGE 47*
LAST PAGE

*FREE BOOK*

"yarinyar nan wai har tayi girman fooling É—ina, ce min fa tayi zata get together ta kuma fita da decent dressing amma yanzu ji dress dake jikinta? Ya Subhanallah"

A sanyaye yace
"calm down die hard baki gani gabaÉ—aya hankalinta ya tashi? She's just a teenager for goodness sake"

Norah ɗin ya riƙe yana goge mata bakin nata, duk fuskanshi ya bayyana damuwa, Kallonsu ta tsaya yi kerere lallai Raed be ɗauko hanyar tarbiyatar da yaranshi ba, Juyawa kawai tayi ta koma mota ta zauna da kallo ya bita har ta rufo kofar kan ya kamo hannun Norah ya sanyata bayan mota shima ya shiga ya ja suka bar wurin.

Har suka yi nisa babu wadda ya iya magana, chan ya dube ta ganin yadda take fushi ita kaÉ—ai..

"Baby gurl please you need to calm down, ba wani abu me muni kika samu yarinyar nan tana yi ba..."

Katse shi tayi
"ba abu me muni ba ka ce? OK shikenan! Nunamin kawai zaka yi Æ´ar ka ce baka so in hukunta ta bayan ka san laifin da ta aikata babba ne, taya zata yi irin wannan rayuwa tana Æ´ar musulma?"

"Ya Subhanallah! Hidayah me ya kawo wannan magana?"

Shiru tayi bata ce komai ba har suka isa gida, duk ta riga su fita ta haura ta shige É—akinta, ko da suka hauro da Norah kuka take yi

"am sorry dad na Haɗa ku faɗa da mommy I had no idea night club zasu ja ni naje, wlh I dressed like this saboda zuginsu ban taɓa ba, ka tayani ba mommy hakuri duk su suka faɗa min abunda zan faɗa mata ta barni na fita ba zan ƙara ba"

Zaunar da ita yayi shima ya zauna yace
"kin san mommynku is my first cousin sis ko?"
Kai ta gyaÉ—a ya ce
"yau ko bani da rai she have all the right da zata zauna daku ta hukuntaku idan kun yi ba dae dae ba, sannan karya bashi da kyau kin yi ƙarya saboda ki aikata saɓo in kin mutu me zaki cewa Allah?"

Kuka take yi ta sake cewa
"am sorry"

Yace
"Yafiyar Allah zaki nema sannan ki ba mommynku hakuri idan ta huce, Thank God we are leaving France 2morrow, je ki cire kayan nan ki kwanta ok?"

Kai ta gyaɗa ta miƙe ta nufi ɗakinta, ɗakin hidayat ya kurawa idanu yana nazarin ɓacin ranta a saninshi tana da sanyin hali da ko laifi aka mata cikin natsuwa take hukunci, amma kuma kwarai be ji daaɗin kalmarta na wai ze nuna mata Norah ba ƴarta bace, mikewa shima yayi ya nufi ɗakin shi, tun da ta tare gidanshi basu taɓa raba wurin kwanciya ba se ranar.

Babu wadda yayi baccin kirki a ranar asuba farko ta fita ta fara HaÉ—a musu break, bayan ta gama ta bi su ta tashesu suka fara yin sallah kan suka yi wanka suka hau shiri, Farrah ta aika ta tada Norah ta dawo, har gari ya É—an yi shaa kan suka fito suka karya, ko da ya zauna a dining ma
"Good morning"
Kawai tace tare da saka mishi abinci ta tura mishi, kaÉ—an ya ci ya koma parlor da suka bar komai an dae rufe da Fararen kyalle, suna gamawa suma Paul ya gama fitar da akwatunasu suka bar gidan zuwa Airport anan suka samu Rashida suka yi sallama, har suka sauka Riyadh Motoci kusan biyar suka taryesu babu wadda ya cewa wani komai se yaran ke ta hayaniyar su.
Chapter 72 · 0% Book details