← Book details Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 74

Sashe 57

Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasa kawai take da yatsun hannunta tana alwalar kuda wadda babu ruwa, motar ta ɗauki shiru banda sanyin Ac da fitinannen kamshin shi babu abunda ke tashi, yadda yake tuƙi kaman ba ze tafi ba tunda ya ɗauko ta yasa ta ɗan ɗago ta saci Kallonshi.

Da suke Gaisawa da Ummi kaman ranshi ba'a ɓace ba amma kallo ɗaya ta mishi taji bata so ta sake Kallonshi cikin wannan ɓacin ran ko ba Sanadiyarta ba bare sanadin ta, a hankali tace

"Paaapi!"
Be amsa ba Dukda muryar da tayi anfani dashi É—in ba karamin shigarshi yayi ba, Raurau tayi da idanu muryarta na rawa tace

"am so sorry....! Na san ban kyauta ba amma..."
Kukan da yake son kubce mata ne yasa tayi shiru, kaman ze share ta sede ba ze iya ba, parking yayi gefen titi ya zuki iska ya fesar a lokaci É—aya ya sanya hannu ya yaye hijab É—in jikinta ya cire kan ya mirginota zuwa cikin jikinshi ya rungume.

Dukkansu idanu suka lumshe suna jin kewa, soyayya da kuma tausayin juna.

Hawayenta ne yake diga mishi har cikin fatar kirjinshi, ƙara sanyata yayi jikinshi cikin taushin murya ya ɗago haɓarta yace
"shhhh! Baby gurl you cried enough today pls don't start again now..."

Hannunta ta ɗaura bisa rigar shi ta kara riƙe shi jin yadda yake sake mannata da jikinshi cikin salo.
"My fatherrr....!"

"Shhhh baby don't say anything about him, ba laifinshi bane now u know who that evi...."
Da sauri ta saka tattausan hannunta ta rufe lips É—inshi.

"Duk munin halayyar iyaye babu inda aka mana umarni da mu ci mutuncinsu ko mu zage su, Paapi I love you and bana son fushin ubangiji ya hau kanka saboda Baba Buba, pls find a place in ur heart and forgive him É—an Adam ajizi ne..."

Kallon mamaki yake jifan ta dashi yace
"after all he have done to you? And my aunt? I mean ur mother?"

Kai ta gyaÉ—a tace
"Besides ni na yafe mishi, please forget the past and focus on the future..! Kaga ba don shi ba kila we will end up as cousins not lovers, ba don shi ba kila da baka min taimakon da ze sa in ji duk duniya babu wadda bana so ko kuda ya taɓa ba kaman kai... Maybe I wouldn't have given birth to Usman, Aisha and Junior you! Ka ga every disappointment is always a blessing..! Had it been be maka abunda ya maka ba da pastor polycap be ɗauke ka ka zama the greatest footballer of our Era ba..."

Yadda ta kare maganan da wink yasa ya saki wani malalacin murmushi, lip É—inshi ya kai yayi pecking idanunta da ta lumshe, ya dawo yayi na hagu kan yayi kissing nose tip É—inta daga karshe ya dira a lips É—inta.

Seda ya gaji don kanshi ya gyara mata kwanciya yana saka hannunshi na hagu ya tallabo chin É—inta yana shafawa a hankali yace
"Baby gurl you are a blessing indeed! I love you"

Tace
"nima haka yayana!"
Fuska ya ɓata yana turo lips yace
"what?? What's nima haka again? I said I love you"

Dariya tayi har hakwaranta na fita tace
"love you more..!"

Kiran Wayanshi ne ya katse shi, a hankali ya saka hannu ya É—auko ba tare da ya raba ta da jikinshi ba ya manna a kunne, mintuna biyu ya sauke ya kalleta yace

"ur dad regain his consciousness and yana so ya ganki please die hard don't cry again for my sake..! Allah baki ji yadda na shigo Nigeria da rashin daaÉ—in zuciya ba when ever Tunanin kin yi kuka ko kina kai yayi crossing mind É—ina, and please don't ever go out again without my consent I was totally upset É—azun nan!"

Lakace mishi kumatu tayi har dimple ɗinshi ya Luɓa suka yi dariya a tare tace
"I won't in shaa Allah, am sorry"

Kai ya gyaÉ—a kan ya taimaka mata ta koma mazauninta seda suka saka hijab a tare kan ya tada motar suka yi tsadaddiyar Asibitin da dama chan aka saba kai Alhaji Usman kuma anan suka kawo Baba Buba.

****

Da kwatancen Daadida suka iso Amenity room ɗin na VVIP wadda bashi da maraba da gida sbd haɗuwa da tsaruwarshi, hannunsu riƙe cikin na juna yayi knocking kan ya tura ita kuma tayi sallama..

"Hidayat!!!"

Muryoyi biyu suka yi kiranta wadda ya sakata tsayawa chakkkkk kaman an dasa ta, da sauri ta kalli wadda ya kirata na biyun ta maida kanta ga na farkon wadda shine mahaifinta ta kara maida idanunta ga na biyun muryarta na rawa tace

"Ya Hamza???? Me kake yi anan? Dama ka san wannan??"
Ta Nuna Alhj Usman don har yanzu bata san da wani suna zata iya kiranshi ba.

Yace
"Hidayat..! Wannan ai mahaifina ne, me kike yi anan? Dama kece hidayat da yake ta kira tun farfaÉ—owarshi?"

Hajiya tace
"kai! Kai!! Kai ni fa kun kulle min kai... Kowa hidayat hidayat hidayat! Daga mijina har É—ana? Ke wai wacece ke ne nikam? What's the meaning of whole this??"

Alhj Usman yace
"Hidayat jini na ce! Hidayat Æ´ata ce ta cikina! Hidayat É—iyarmu ce ni da AISHA! ita ce ribar soyayyar mu.."

Duuuuummmm haka Hajiya da Hamza suka yi, shi kam tsabar kaduwa ne, hidayat da yake hauka da mutuwar so har yanzu yana kan kallon likita sbd aman jini da be dena ba da damuwa ita ce yanzu ake cewa uban su ɗaya? Kenan ko ba Raed sun haramtawa juna ko menene? Kwarai yana iya tuna ya taɓa jin sunan Aisha chan chan baya matsayin matar Mahaifinshi... Da sauri ya kalli hajiya da ta zabga wani ashariya tace

"Wallahi baze yiwu ba! Alhaji me ki....ka..ke nufi? Wace Aishar??? A ina ka samo ta bare har ka san wannan me kama da sadaka yallar É—iyar ta ce?"

Daga hidayat, Raed har Daadida sede wannan ya kalli wannan suna rarraba idanu tsakanin hamza, Hajiya da kuma Alhaji.

Murmushi yayi yace
"kwarai da aniya wannan jinin Aisha ce da baki so gani ba a duniya Hajiya Balaraba, hamza! Hakuri zan baka ina kuma baka tabbacin cewa bad deeds É—in mahaifiyarka ne Allah ya ramawa baiwar Allah ta hanyar jarabtarka da matukar soyayyar Æ´ar uwarka jini É—aya, ita mahaifiyarka na faÉ—i tashi wurin ganin ka tsira yayinda a baya tayi faÉ—i tashi wurin ganin ta raba auren sunna ta raba uwa, uba da Æ´ar su sede dayake Allah ba azzalumin bawansa ba Kaine ka wahala Sanadiyarta don ko ba komai da a gabana hidayat ta tashi da baka mata wannan son mutuwar ba..."

Dishi Dishi hamza ya fara gani, ya kalli hajiya ya kalli Abban shi se kuma ya kalli hidayat, idanunshi ya sauka bisa hannayensu dake sarkafe cikin na juna da Raed, runtse idanu yayi wasu zazafan hawaye suka zubo.

Hidayat hajiya ta zubawa idanu jin kalaman da Abbanta yake faÉ—a game da ita, kenan itace silar komai? Kenan ita ce ta raba ta da farin ciki da jin daaÉ—i na rayuwar wannan duniya?

Shigowar likita ne yasa duk suka kalli kofa, yace
"ya kamata ku barshi ya huta hakanan duk abunda Zaku tattauna ku bari gobe da safe jininshi ya hau har ya wuce misali.."

Daadida tace
"hakane Dr, yanzu zamu tafi in shaa Allah zamu hakura da jin koma menene seda safe"

Hamza mikewa yayi da niyar fita se ya yanke jiki ya faÉ—i, Hajiya ta kurma ihu tayi kanshi tana cewa
"Hidayat ce! Wallahi Hidayat ce! Duk itace, ita ce fa wallahi itace...!"

Yadda take maimaita kalma É—aya zaka yi tunanin akwai matsala a kwakwalwanta, Dr kiran nurses yayi aka É—auki hamza zuwa wani room É—in don dama shima ba'a sallame shi a asibitin ba yana kan medication ne.

Hannu hajiya ta sa a kai ta kurma ihu tana nuna hidayat tana cigaba da faÉ—in duk ita ce wallahi duk ita ce ta rusa mata gida..

Raed dae bayanshi ya maida hidayat yana mata wani irin disgusting look, gangan Alhj Usman suka koma ya É—an duka ya gaida shi, ya amsa cikin kulawa yana murmushi.

Daadida tace
"Sannu da jiki Alhj Allah yasa kaffara ce"

Ya amsa da
"Ameen mama na gode! Amma don Allah kan ku wuce ku duba yaya Buba tare muka zo yana next room"

Shiru Raed yayi Daadida ta fara share hawaye tace
"Allah sarki! Duk abunda yayi maka baka duba ba ka nufe shi da alkhairi? Allah ya saka ya sa a mizani mun gode... Raed ka gani ko? Ka ga irin zuciyar mutanen kirki? Shi fa salwantar mai da iyali yayi a lokacin be ma sa ran sake ganinsu ba hakan be hana shi taimakon shi ba se kai da ya haifa ya kawo duniya zaka Gaza yafe mai laifukanshi gareka..!"

Hannunshi dake cikin nata ta É—an matse ya kalleta da idanunshi da suka rine da ido ta mishi alamar please! Ya kalli Daadida yace

"na yafe mishi already albarkacin macen kirki Hidayat..! Kiyi hakuri yanzu zan je na duba shi"
Rungume su duka tayi tana kuka en jikokinta da bata da Kamarsu a duniya.

A hankali Raed ya saki hannunta ya kama na Daadida ya ja suka fito yana yiwa hidayat kallon be careful Dukda hajiya tayi gaba already tana kaÉ—a zani sbd birkicewar da tayi har lokacin bata dawo daidai ba.

A hankali hidayat ta taka gaban gadon ta ja kujera ta zauna tana kaucewa kallon da Alhj Usman ke mata, muryarta na kakkarwa tace

"Saan..nu Ab....ba "

Lumshe idanunshi yayi yana jin sanyi na ratsa shi, tunda ya farfado se yanzu yake jin wani abu na farin ciki na shiga cikin zuciya da ruhinshi, dukda yayi babban rashi sede ya gode Allah da ya bar mishi hidayat É—in ma.

"Sannu princess!"
Se ta kalleshi jin sunan da ya kirata dashi, a tare suka sakarwa juna murmushi.

Yace
"princess yau zaki zauna da Abba ko? I want to spend the night listening to ur stories Ina so every single thing na rayuwar da kika yi kar ya wuce ni..! I've missed a lot bana so in sake missing ko da second ne na rayuwarki.."
Chapter 57 · 0% Book details