Sashe 28
Kowa Ya Ga Zabuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaman yadda bukar ya faÉ—a hakan kuwa ta kasance, bukar mutum ne me tsananin zafi, HaÉ—a rai da rashin mutunci kwata kwata akan dukiyar shi bashi da mutunci, haka matanshi su su huÉ—u rass babu wacce ke ganin hakwaranshi da sunan dariya, ba mutan gidan ba har na waje shakkar shi suke, mahaifiyar da ta haife shi ma bata tsira ba Dukda ba ze zage ta ba sede itama yana shimfiÉ—a mata doka, amma matan suna shan bauta da aiki.
Mairamu ce ta farko wacce tunda ya aureta in ta samu ciki baya zama in ya zauna kuma ta haihu Æ´aÆ´an basa zama se su sha ciwo na watanni kaÉ—an su koma, a haka ya auro na biyu badi'ah yaranta huÉ—u mata.
Se Naja'atu itama yaranta uku mata se Amaryar zarah yaranta biyu suma mata ne, suna tsananin kishi da Maryam saboda yadda daga mijin har surkar suke nuna sun fi kauna da sonta Dukda shi Bukar ba gane mishi suke ba sede kam zasu iya cewa hakan saboda ganin bayan Daadida ita ce kaÉ—ai kan É—an tankwara shi kaÉ—an amma sauran ko gwadawa basu isa yi ba.
A gidan ko wani karshen wata ana kawo hatsi buhu guda, idan har Rogo ya jingine musu su zasu yi wahalar maida shi gari sede ya dinga turo abun miya sun dinga cin rogon kenan har se buhun ya kare se ya sake jingine wani hatsin, yana jingine shinkafa gumi, Gero, dawa, masara duk abunda yayi niyya amma fa guda É—aya idan sun gama aikin se su raba ko wacce ran girkin ta ta san yadda zata sarrafashi kowa ya ci, ko Maggi ne zaka sa a miya se ka jira ya shigo kan ya kirga ya baka, haka in nama ne a kirge yake wai don kar a mishi Almubazzaranci.
Sannan wankin shi shima in ya taru matan yake jibge ma wa haka zasu raba su dirza, sannan aikin wurin dabbobbinshi da tsabar yawansu aka mishi lakabi da MAI NAGGE wato me shanu, yadda in har ka shigo garin mambila kace Gidan Bukar mai nagge kowa ya sani, tsabar zafin shi har dabbobin su kan san da shigowar shi, in kana so kuyi rashin M ka raina shi ko ka mishi wasa da dukiya.
Mairamu ta raini cikin nan nata cikin tsanani da azaba saboda laulayi me zafi take yi, hakanan ga ayyukan gidan tunda tunkunyar gidan lamba goma ce, daga shara har wanke wanke bata iya sede Daadida ta karɓa mata wadda da kyar take barin ta yi don ta dinga rokonta kenan akan ta bari ba se tayi ba se in ta nace ne zata sakar mata
Ranan girkin ta haka zata tashi tun da duhu ta fara shara ta gama ta É—aura koko na kari bayan nan tayi wanke wanke ta zo ta É—aura abincin rana, tana saukewa za'a maida ruwan na dare, gashi wani lokacin se ana tsaka da yi za'a shigo da buhun hatsi saboda baya so a mishi asara ko kwari su shiga hakan ya sa baya bari hatsi ya kwana yana shigowa ya gani kin shiga uku da sababi.
Kaman yau cikinta na cikin wata na hudu har ya fara fitowa, zaune take tana wanke wanke hannunta na rawa saboda cimar cikinta ya ƙi shi, Jan masara ne kuma tunda aka kawo banda koko da safiya bata iya cin komai saboda cikin ya ƙi jan masara.
Shigowa yayi da gyaran murya wadda ya sa duka sauran matan gyara zama suna shiga taitauyinsu, kallon kwatar buhun gero da ya ajiye musu yayi ya sake haɗe rai yace
"wannan kuma kason waye ne don wulakanci zata bar min dukiya a gantale?"
Badi'ah tace
"ka ganta chan uwar laulayin duk duniya"
ÆŠagowa Maryam tayi tace
"kayi hkuri ba wai na ƙi yi bane ayyuka ne suka min yawa ga rashin karfi saboda bana iya cin jan masaran nan"
Yace
"ke kika jiyo ni de abunda na sani in ga hatsina a gyare tass"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Hawaye take tana aikin da wahala, daga karshe kaman kullum se Daadida ce ta fito ta taimaka mata da dare kuma ta shirya ta tafi turaka..
A kullum Adu'ar Daadida be wuce Allah ya sauya mata hallayyarshi ba sbd baƙin bafulatani ne ba a fuska ba a zuciya saboda yana da arzikin da ze iya fidda kunci a gidanshi sede hannun shi a dunkule yake, yana da halin daukar masu aiki sede ba ze yi ba, yana da ilimin Addini amma ta rasa meyasa baya aiki dashi shi kuma haka Allah ya halicce shi yaranshi in sun ganshi kaman sun ga mala'ika, baya son yara mata iyakacinsu dashi cimarsu bayan nan duk wata hidamar ƴarki ki san yadda zaki yi.
Wahalar da ta sha a cikin ba ƙarami ba gashi bata da kowa banda mijin saboda Fulanin tashi ne en uwanta kuma sun tafi bata san inda suka yi ba, da shi ta dogara wannan yasa yake anfani da rashin kowan yake mata yadda yake so, har dukanta ya taɓa yi da cikin saboda ɗan hatsaniya da suka samu da Zarah ta lauye maganan.
Cikinta yana wata tara amma har lokacin babu hidimar da ya É—auke mata, idan taje garken na dabbobinshi shara sede ta saka gwiwowinta a cikin kashi take iya sharar gabaÉ—aya jikinta se ya samu kashin dabobbin kan ta gama tun tana amai kaman zata amaye hanjin cikinta har ta koma daure dankwali a hanci da bakinta kan ta iya sharewa.
Uban wankin shi ne jibge take tiƙa Dukda bayanta dake a sage cikinta kuma na juya banda idanu da hanci babu abunda zaka gani a jikinta se fari kaman aljana in ji faɗar Kishoyoyinta da ta rasa me ta tsare musu suka sako ta a gaba bayan ita ce uwargida ma.
"Mairamu ki aje wankin nan ki zo ki huta hakanan ko ba É—azu kika ce baki jin daaÉ—i ba?"
Cewar daadida cikin tausaya mata
Tace
"Daadida bari na gama kin san in ya shigo ya samu ma magana ne"
Zarah dake surfe ta taɓe baki ta fara wake waken habaice sbd haushin yadda surkuwar tasu ta fi damuwa da Mairamu suke ji ba kaɗan ba.
Badi'ah tace
"mu da muke ba Æ´aÆ´a ba aikin ya kashe mu ba"
Naja tace
"Ai karshen alawa dae ƙasa Allah kuma ya sa shi ɗan ba me jin maganan na gaba da shi bane da tuni an sa ya kora mu waje"
Mairamu ta miƙe tsaye tana rike baya tace
"amma dae ya kamata ku dinga sanin maganan da Zaku ke faÉ—awa Daadida ko bata haife ku ba ta haifi uban Æ´aÆ´ayenku bare ma a haihuwa duk ta haife ku.."
Zarah da ta fi raina ta akan kowa tace
"don ta haifeshi se me? Shi É—in ya É—auke ta uwa ne? Ta je ta fama da damuwar ta ba ta zo ta tare a gidan surakai ba mana taga in mun bita mun faÉ—a mata magana ko ba haka ba?"
Tayi maganan tana kallon Su Naja a tare suka ce
"kwarai kuwa"
Maryam zata sake magana Daadida ta hanata tace ta je ta zauna zata karasa wankin.
Duk abubuwan da Bukar ke yi babu abunda yafi komai ƙona ranta irin yadda yake da mahaifiyarshi, mace ta dauki cikin ka ta Rena ta haife ka girma kana mata yadda ka ga dama? Anya yana son gamawa da duniya lafiya kuwa? Ai iyaye ba abun wasa bane.
Karshe dai Daadidan ce ta mishi wankin ta shanya, cikin dare Mairamu dake dakinshi nakuda ya tasar mata, duk yadda tayi dashi da ya taimaka ya kira mata ko Daadida ne yace in ya fita a É—akin wutar Allah ta ci shi.
Da kyar ta iya mikewa cikin azaba ta fito ruwa har yana bin kafafunta ta fara bubbugawa Daadida wadda yayi sanadiyar farkawar matan suka fito suna kallo har Daadida ta shiga da ita, ta sha baƙar wahala kan ta haihu gab asuba kukan yaron ya karade ilahirin gidan.
Fitowa Daadida tayi ta shiga É—akinta ta kwaso abubuwan da zata bukata wurin karasa ayyukan badi'ah tace
"ta juye kenan to Allah ya ji kan rai tun kan lokacin yayi"
Har Daadida ta saka hannu a kofan É—akinta wurin komawa ta juyo tace
"Tabbas ta juye santalelen lafiyayyen É—a namiji kuma in shaa Allah shine me jan ragamarku nan gaba shine kuma shugaban Æ´aÆ´ayenku, ranshi a Hannun Allah yake ba hannun ki ba bare ki fara mishi hasashen mutuwa ke ba Alanmusuru ba"
Shiru duk suka yi suna kallonta saboda maganan ya dakesu, shiganta suka kalli juna Naja tace
"kaman namiji fa tace?"
Badi'ah tace
"kwarai abunda tace kenan"
Zarah tace
"Ah bamu ga ta zama ba fa"
A ruÉ—e kowacce tayi É—akinta sbd kalmomin Daadida na zama magaji kuma shugaban gidan abun be musu daaÉ—i ba Sam ya kuma dake su.
Ko da gari ya waye Daadida ta fito taje tayi sallama kofar É—akin Bukar ya leko kai yace
"Mama lafiya kuwa?"
Tace
"yarinyar nan ta sauka kuma tunda ta haihun nan bata wani jin daaÉ—i ya kamata ka kaita asibiti a duba ta"
Yace
"wa? Tabb ai abunda kuma ba zan iya ba kenan mama ba zan kashe kuÉ—ina a banza ba"
Tace
"yaron ma fa bashi da cikakken lafiya Bukar Haba don Allah ka ji tausayinsu mana"
KarkaÉ—a kunnenshi yayi yace
"Me kika ce?"
Tace
"nace yaron bashi da cikakken lafiya"
Wara idanunshi yayi yace
"kina nufin namiji ta haifa?"
Kai kawai ta gyaÉ—a mai ganin kaman ya ruÉ—e ai se ya sheke da dariya wadda ya saka badi'ah, zarah da najah Kallonshi cikin dumbin mamaki.
Jiki na rawa yayi É—akin Mairamu Daadida tayi musu wani kallo na ba kun gani ba kan ta bi bayanshi, aiko farar É—aya yaron ya shiga ranshi matuka gaya.
A take ya kaisu asibiti aka duba lafiya su aka rubuta magunguna ya sayo, har kaji biyu ya yanka mata Daadida ta sarrafa mata shi ta samu ta É—an ci cikin mamakin sabon halayyar Bukar É—in lallai É—an ta ya zo da albarka.
Hidima kam ya musu har ran sunan shi ya naÉ—ama yaron suna Muhammad Daadida kuwa tace Raed za'a kira shi tunda dae ya tabbata shine shugaba in ba Bukar.