← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 112

Sashe 99

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read

ƙananan kunamu baƙaƙe masu cizo dake fitowa daga gaban Aina'u, gaba ɗaya tayi watsi da kayan dake jikinta. Rintse idanu yayi tare da faɗin, "Allahumma arji'ini fi musibati wa aklifni khairan minha, wannan wacece haka? Hajiya kar ki shigo don Allah!" Ya fadi don baya son Hajiyar ta razana. Amma tuni Hajiyar ta sako kai ta shigo ɗakin, zuuu ta tafi zata faɗi saboda razanar da tayi ganin Aina'un. "Nice Aina'u, ku taimaka min ku kaini asibiti, wallahi mutuwa zan yi, ku taimaka min!" Faɗin Aina'u, wanda bai san abinda ta aikata ba, dole yaji tausayin halin da take ciki. Maƙogwaro a waje, tsokar fata sai yankowa take tana faduwa tsutsa na cin ramin wajen da tsokar ta faɗo, ga tsutsotsi da baƙaƙen ƙananan kunamun dake fitowa daga gabanta masu azabar harbi da ciwo, idanu sun zazzago, baki ya turo uwa na kare, ga kuma zafi da mummunar wari da jikinta yake yi, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Faɗin Hajiya tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Aina'u, kece kika dawo haka? La haula wala quwata illah Billah! Aina'u kin ga ƙarshen aikata sharri ko!" Hajiya na ida zancenta Aina'u ta ɗuka kamar kare ta hau kukan jaki kamar zata fasa ɗakin, can kuma kamar an tambayeta ta soma confessing abubuwan data aikata, "Abia naje nayi mummunar tsafi domin in samu zuciyar Khalil, ban san sau nawa wani inyamuri mai suna Ugo yayi amfani dani ba, nayi kwanaki cikin tukunyar tsafi, sannan na kashe mutane babu adadi, daga cikin akwai jikanki ƴar wajen Nafeesa, ni na sadaukar da jininta wa Hell, sannan nice na kashe Nafeesa da mijinta ta hanyar tura aljani ya tsotse jininta sannan ya bude tukunyar gas wanda hakan yayi sanadin rayuka da dama. Nice na kashe ƴaƴan ƴan uwana duka ta hanyar tura aljani ta suffar maciji ya sare shi, nice na kashe ɗan adaidaita sahu saboda rashin tafiya da sauri da yayi har na rasa damar kashe ƴan biyun Sarah tun suna jarirai, Ni ce na tura Muneeba cikin duniya wanda har yanzu tana ta tafiya bata san inda kanta yake ba, nice nayi wa Khalil mummunar tsafi yayi ta amfani dani ba cikin hayyacinsa ba, sannan nice na tura na saka Hell ya tura aljami mantau cikin kwakwalwar Ya Abdullah da ya barrister domin su manta dake Hajiya har abada, nice nayi asiri Abdul-Hakeem ya saki matarsa domin ta gano sirina, sannan na saka aka dakatar dashi daga wajen aiki, kuma duk na samu ƙarfin tsafin nan ne ta silar kwanciyar aure da nayi da mahaifin da yayi sanadin zuwana duniya domin hakan shine cikar tsafina, na samu nasarar kwanciya dashi ne ta sanadin tsafin da nayi masa sannan na juye masa sak Lami, sai bayan ya gama amfani dani sannan hankalinsa ya dawo jikinsa, baƙin cikin haka ya saka ya yanke jiki ya faɗi, dalilin faɗuwar da yayi shine silar ciwon da yake fama dashi yanzu na shanyewar ɓarin jiki." Tsabar zuciyar Hajiya ta kasa ɗaukar abunda taji daga bakin Aina'u, faɗuwa ƙasa tayi a sume. Khalil kuma yayi kan Aina'u da dukan fitar rai. Sai Abdul-Hakeem ya rasa wa zai riƙe a cikinsu, daka ƙarshe dai ya bawa Hajiya taimakon gaggawa ta hanyar fitar da ita daga ɗakin ya yayyafa mata ruwa, sai da ta farfaɗo tukun ya koma ɗakin ya riƙe Khalil dake neman kashe Aina'u, "Baka da hankali ne Khalil? Mai yasa zaka kashe gawar da ba taka ba? Ai wannan yarinyar bata buƙatar komai na hukunci daga gare mu, hukuncin da Allah ma yayi mata tun a nan duniyar ya isheta wallahi." "Ka barni na kasheta dan girman Allah Ya Abdul-Hakeem!" Fadin Khalil yana kuka sosai. "Wallahi ba zan bari ka rage mata nauyi ba. Ɗan yatsarka ɗaya ma ba zan bari ya kuma taɓata ba." Ya faɗi tare da kama hannunsa ya fito da shi daga ɗakin sannan ya jawo karyayyan ƙofar ya rufe. Ƙasa suka sauka inda Hajiya take tana kuka sosai, idanunta sun kaɗa sunyi jajur tuno autarta Nafeesa. Kallon Khalil Hajiya tayi tare da faɗin, "Kaga sakamakon rashin ji ko Khalil? Da ace baka ɗurawa ƴar mutane ciki ba, yaushe har wannan bala'in zai shigo cikin gidan mu. Ka kwaso mana dangin matsafa, dangin masifa da bala'i cikin gidanmu muna zaune lafiya! Me za ayi da irin wannan tsinannen zuri'a, wallahi haɗa zuri'a da irin yarinyar nan mafisa ce babba rayuwa, ina jin dama ace ban haifeka ba Khalil, da duk haka bai faru damu ba. Sanadinka rayuka da dama sun salwanta, ƴata, autata Nafeesa ta kashe min ita, ta ashe ƴarta wacce idan ina ganinta zanji sanyi, ta kashe mijin, ta kashe kowa! Allah ya isa tsakani na da wannan ƴar iskan yarinyar. Ibrahim, aurenka da Saratu bai amfane mu da komai ba sai bala'i da masifa, kuma ka rubuta ka ajiye, idan har nice nayi naƙuda sannan na tsuguna na haifeka, ba amince maka ka dawo da Saratu cikin gidan nan ba, ƴaƴa kuma a dawo dasu zan riƙe!"
Chapter 99 · 0% Book details