Sashe 73
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 2 min read
kasa tambayar ina Aunty Maryam ɗin duk da kuwa bata ganinta, wani irin mahaukacin tsoron Aina'u take yi, idan ta ganta gabanta faɗuwa yake yi, Nafeesa ma haka, wannan dalilin ne ya saka ta tattara tabi mijinta duk da dama shima abunda yake so kenan, don dangi sun taso shi gaba akan ta dawo gidan auranta. Zaune Hajiya tare a kan kujera ta rasa abunda ke damunta, ga Laure dake gefenta wacce lokaci bayan lokaci take saka bayan hannu ta share hawayeta, tayi wani irin mugun rama, hatta a fuska sai ƙasusuwa suka fito mata, babu komai a fuskan dai idanu da haƙora yaƙaƙau! Fitowa Aina'u tayi daga ɗakin da Hajiya ta ware mata tana fito, babu wanda ya iya ɗago idanu ya kalleta a cikinsu, "Hajiya ko kin san wannan abun dake hannuna?" Faɗin Aina'u tana mai kai mazaunanta akan kujera, ɗagowa Hajiya tayi ta kalli hannun nata tare da girgiza kai. Sakawa a baki Aina'u tayi tare da kunna lighter ta kai kan wiwi ɗin tayi masa wani irin zuƙa tare da faɗin, "Wiwi ce!" Zaro idanu Hajiya tayi tare da yin gum, Laure kuwa babu inda jikinta baya rawa ga warin hayaƙin mara daɗi mai tada zuciya kuma babu wanda ya isa ya tashi a cikinsu. Sai da tasha murɗi biyu sannan ta kwanta akan three sitter tare ɗaura ƙafa akan saman kujeran tana kallon Tv, can kuma ta juyo ta kalli Laure tare da faɗin, "Ke, tashi ki canza min channel zuwa MBC action." Da sauri Laure ta tashi ta nufi wajen TV ɗin daidai lokacin da Khalil yayi sallama ya shigo ɗakin domin shaidawa Hajiya yana son shi da Sarah su tafi India domin a duba masa jikinta, don gaba ɗaya result ɗin tasa-tasan da aka yi mata a asibitin bai nuna tana ɗauke da matsalar komai ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya! Warin wiwi fa nake ji a ɗakin nan." Da sauri Laure da hajiyan suka kalli juna sannan suka kalli Aina'u da ta wani irin ɗaure fuska. "Hajiya......." Tun kamun ya ƙarisa Hajiya tayi saurin faɗin, "Ni dalla ka isheni da magana, to ni nasha wiwin!" Zaro idanu Khalil yayi, sai kuma ya mayar da dubansa izuwa wajen Aina'u tare da faɗin, "Dan ubanki kece kika sha wiwin ko?" A watse ta kallesa tare da faɗin, "Hajiya ce tasha, ko baka ji ta baka amsa ba." Wani wawan mari Khalil ya ɗauke fuskan Aina'un dashi tare da faɗin, "Dan ubanki zo ki bar gidan nan tun da ba gidan ubanki bane......"