Sashe 54
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai yaji tausayinta kasancewar babu ƙarya ta jigata da yawa. Bayan komai ta lafa. Da kansa ya cicciɓeta har bayi ya galgasa mata jiki. Ko a wajen sanyata cikin ruwan zafi tayi dauriyan ba kaɗan ba. Babu abunda take yi sai ciccije baki da faɗin "Wassh!" Har ya kammala gasatan sannan ya nannaɗota cikin towel ya dawo da ita kan gadon sannan ya buɗe ƙaramin fridge ɗin dake ɗakin ya ɗauko ruwan gora tare da ɓallo paracetamol da pain killer ya miƙa mata, hannunta na rawa ta karɓa ta watsa a baki tare da korawa da ruwa sannan ta kwanta tare da dunƙulewa waje ɗaya tana rawar tsari. Kashe wutan ɗakin yayi tare da hawa kan gadon ya lulluɓesu da bargo sannan ya jawo ta jikinsa ya rungume. Nan da nan baccin wahala yayi gaba da ita, shi kuma sai ya tashi zaune ya jawota a hankali ya ɗaura kanta a saman cinyarsa. Hannu ya kai ya kunna bedside lamp mara haske wanda ya bashi daman kallon fuskanta sosai, sai sauke ajiyar zuciya take yi. Baccin ma a shagwaɓe take yinsa. Don sai wani kwaɓe fuska take yi tana ƙara shigewa jikinsa dama kuma Sarah akwai son jiki kamar mage. "You're my early paradise, my one and only, my four in one, infact my everything. You're _Khalilullah's_ happiness! Without you Sarah, I can't survive. Sarah a yau mun haɗe mun zama ɗaya, ke _Ibrahim_ ce, _Ibrahim_ kuma kece. Saratu baki na ba zai iya misalta maki yanda nake jinki a raina ba, yanda kika bani farin ciki a yau, Allah yayi maki sakayya da gidan Aljanna." Kamar a mafarki haka Saratu take ta jin maganganunsa. Gam ta kamo hannunsa ta riƙe, cike da magagi irin na bacci ta soma faɗin, "Kai jinin dake yawo a jikina ne, duk wani bugun zuciyata da tunaninka take tafiya, _Khalil_ tun lokacin Sarah ta soma tozali da kai ka sace zuciyarta, kuma a kullum bata taɓa fasa addu'ar Allah ya mallaka mata kai ba. Rayuwar Sarah Nuhu, da taka take tafiya. Tsayawar taka dai-dai take da tsayawar bugun zuciyar Sarah. Sarah ta mallaka maka komai nata, a yau da kuka zama ɗaya kuma, ta ƙara damƙa maka akalar rayuwarta. Ka taimaka ka rungumi Sarah a ko wani irin hali, don Sarah tayi wani oath akan cewar, no matter what, kuna tare for rever and ever." Wani irin murginata yayi tare da yi mata rumfa ya shiga kissing ɗinta yana faɗin, "Nagode wife, nagode. And I promise babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu. Mun riga mun zama hanta da jini." Wasu mahaukatan French kiss ya soma bata. Ganin gaba ɗaya ya soma fita hayyacinsa don har ya soma ƙoƙarin komawa gidan jiya ta soma turesa tana faɗin, "Ka tausaya min, wallahi akwai zafi. Ciwo yake min kuma bacci nake ji." A kunne ya raɗa mata, "Kiyi haƙuri ki bani sau ɗaya kawai, zan biki a hankali ta yanda baza kiji zafi irin na ɗazu ba, don Allah wifey." Shuru tayi hawaye na gangaro mata. "Inyi?" Ya faɗi a tausaye. Ɗaga masa kai tayi tana mai danne kukan da yake taho mata. "Allah ya miki albarka!" Ya faɗi tare da yi mata kiss a goshi sannan ya kai hannu ya kashe bedside lamp ɗin. Wannan karan tafi karon farko shan wahala, don sai ya zame mata kamar fami. Sai dai ba ƙaramin dauriya tayi ba. Babu kwarorowa sai "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un" da yayi ta shan kira da kuma su Lami, Baba da kuma sauran ƴan uwanta. Bayan komai ya natsa ya kuma yi mata gashi karo na biyu tare da wankan tsarki, shima yayi sannan suka kwanta yaja masu bargo nan da nan bacci yayi awon gaba da dukansu don dare yayi sosai biyu ma ta wuce. Sun so makara sallar asuba saboda jimawar da suka yi basu yi bacci ba. Da sauri _Khalil_ ya diro daga kan gadon jin alamar za'a tada sallah a masallaci. Sauri-sauri ya ɗaura alwala tare da sanya doguwar rigar jallabiya sannan ya fita zuwa masallaci. Bayan an idar da Sallah ya fito, a ƙofar masallacin suka haɗu da ya Abdul-Hakeem. Hannu ya bawa _Khalil_ suka tafa tare da faɗin, "Ango-ango, ango ka sha ƙamshi. Ai na ɗauka yau an ɗauke maka sallar asuba yau. Don tuntuni nake ta kallon hanya ko zan hangi fitowar ka." Ya ƙarisa maganar yana dariya. Dariyar shima _Khalil_ yayi tare da faɗin, "Babu wani jin daɗin da zai zo min a cikin duniyar nan da zai hanani gaida Ubangijina. Ai ta hakan ne zan nuna masa jin daɗin abunda yayi min domin ya dauwamar dani a cikin farin ciki." Hannu ya Abdul-Hakeem ya kai ya mari ƙeyarsa kaɗan tare da faɗin, "Ƙanina har wani girma da natsuwa naga ka ƙara daga jiya zuwa yau. Allah dai ya ƙaro zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba." Da "Ameen" _Khalilullah_ ya amsa daga nan gaba ɗaya suka nufi side ɗin Hajiya kasancewar haka suke tun farko, ana saukowa sallar asuba sai sunje sun gaidata sannan kowa ke komawa ɗakinsa. Sai da suka yi knocking sannan ya Abdul-Hakeem ya murɗa handle ɗin sannan suka shiga. Zaune suka sameta a kan darduma tana lazumi. Sai da ta kammala sannan suka haɗa baki wajen faɗin, "Hajiya barka da asubha. Kin tashi lafiya?" Da murmushi ta amsa da, "Lafiya ƙalau Alhamdulillah! Ya kwanan iyalan naku?" Duka suka amsa da, "Lafiya ƙalau." "To ma sha Allah! Abdul-Hakeem ya ake ciki da masu tafiya yau? Kasan Maiduguri ba nan kusa bane. Jirgin za su bi koko yaya?" Hajiya ta faɗi tana kallon ya Abdul-Hakeem. "Eh jirgi zasu bi Hajiya, don ya Abdullah kamun ya juya zuwa Abuja jiya, sai da ya bani kuɗi naje nayi masu booking flight. Jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na safe. Sai a faɗa masu su kasance cikin shiri." Hajiya tace, "To shikenan. Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi da kuma kare ku daga sharrin maƙiya na kusa da na nesa." Da "Ameen." Suka amsa sannan suka tashi suka fita. A parlour suka taras da Laure tana kakkaɓar kujeru, cikin sauri ta gaida ya Abdul-Hakeem kasancewar basa ƴar wasan da suke yi ita da _Khalil_, a taƙaice ya amsa tare da fita daga parlour ɗin. Sai ta juyo ta kalli _Khalil_ tare da faɗin, "Yanzu dai ko darajan amarya naci ai, don Allah a ɗan sammin turaren." Ta ƙarisa maganar a marairaice. "Za'a sammiki albarkacin amarya kamar yanda kika ce. Anjima kizo ki karɓa." Washa baki tayi gaba ɗaya haƙoran sai suka yo waje. Da sauri yaja baya tare da faɗin, "Wallahi idan kina so mu shirya kar ki kuskura ki firgita min mata da wannan haƙoran naki kamar yanda kika firgita ni." Da sauri tace, "Halit......" Sai kuma ta fasa ƙarisawa ta canza maganar, "Ba zan ma ƙara buɗe bakin ba." "A'a ƙarisa abunda kika yi niyyar faɗi kawai. Da kuwa kinyiwa turarenki." Ya faɗi yana hararenta. "To ai shiyasa ma nayi gum da bakin nawa. Ho na Saratu, bada kanka a sare!" "An ƙara miki turare ɗaya." Faɗin _Khalil_. Wani tsalle ta buga na jin daɗi shi kuma yayi dariya tare da fita daga ɗakin. Ko da ya koma ɗaki sai ya taras har Sarah tayi sallah ta koma ta kwanta. Ya gane hakanne ganin hijjab ɗinta a kan sallaya. Jallabiyar jikinsa ya cire ya ninke sannan ya ɗauki hijjab da sallayar ya ninke ya ajiye sannan ya hau kan gadon ya jawo Sarah jikinsa ya ja masu bargo suka. Hamdala yayi jin jikinta ya rage zafin da ya ɗauka jiya. Don kwana tayi da zazzaɓi. Basu suka farka ba sai ƙarfe sha ɗaya. Ta riga shi farkawa don motsinta yaji ya tashi tare da shafa fuska yace, "Good morning my angel!" Lumshe idanu tayi tare da faɗin, "Good morning, happiness." Kiss yayi mata a goshi tare da faɗin, "Ya jikin naki?" Gyaɗa masa kai kawai tayi tana ɗan cije baki saboda jikinta da yayi mata tsami. Naga kamar baza ki iya tashi ba, let me carry you." Ba tare da ya jira abunda za tace ba yayi wuff da ita. "Ni bayi zan shiga, ni dai bayi zani ka sauke ni dan Allah!" Ta faɗi tana harhaba ƙafafunta. Shi kuma ƙin ajiyeta yayi har sai da ya direta a cikin jacuzzi tub sannan ya fita domin bata damar taimakon kanta. Wanka tayi sosai ta gargasa jikinta sannan ta saka rigar wanka fara ƙal ta ƙulle igiyar sannan ta leƙo, sai da ta tabbatar baya nan sannan ta fito daga bayin ta saka silipas dinsa ta fita daga dakin da sauri ta koma nata ɗakin don babu kayanta a cikin ɗakinsa. Sai da ta fara ƙarewa ɗakin kallo tukun tana yaba kyawunsa sannan ta isa wajen mirror ta shafawa jikinta mai me ƙamshi da saka laushin fata. Simple make-up ta tsantsarawa fuskanta sannan ta feshe jikinta da turare sannan ta miƙe ta isa wardrobe ɗinta ta ɗauko wani haɗaɗɗan less wanda aka masa ɗinkin riga da skirt. Ya amshi jikinta sosai. Gaban madubi ta dawo ta tsantara ɗaurinta kuma dama ita gwana ce wajen iya ɗaurin ɗankwali. Turarensa ta ɗan fesa kaɗan a jikinta sannan ta ɗauko gyale ta yafa. _Khalil_ na kitchen yana ƙoƙarin soya kwai yaji door bell, sai da ya juye kwan a plate ya kashe gas sannan ya fita ya buɗe ƙofa. Washe baki Laure tayi tare da miƙa masa kwalaban fiya-fiya guda biyu. "Ke daɗi na dake rashin hankali, wannan kwalaban kuma na minene?" Turo baki tayi tare da faɗin, "Yo ba kai kai min alƙawarin turare har biyu ba." Riƙe ƙugu yayi tare da faɗin, "Sai kuma aka ce don nayi maki alƙawari sai kizo min ɗaki da sassafe kina damuna da buga ƙofa." Kallon basket hannunta tayi tare da faɗin, "Aunty Maryamu ce fa ta aiko ni na kawo maku abun kari shine na taho da kwalaban don ka saka min turaren. Ina amaryar taka? Ni ƙamshin kwai ma nake ji yasin?" Ta ƙarisa maganar tana shinshine-shinshine. "To baƙar mayya, ban abunda aka aiko ki ki wuce ki bani waje. Kuma ki takuran in hana ki turaren, yasin." Ya ƙarisa maganar kamar yanda take yin magana, daidai suka ji ƙarar takalmin Sarah tana saukowa daga steps. Juyawa yayi da saurin jin daddaɗan ƙamshin turarenta da