Sashe 61
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read
yayi tare da faɗin, "Let me take a shower, yanzun nan zaki fara jin kiran sallar magrib." Ya faɗi hakane tare da soma cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai boxer sannan ya shiga bayi. In a few minutes ya fito yana tsane jikinsa, ya samu har Sarah ta fito masa da kayan da zai saka. "Allah ya yi maki albarka Wife, jiki dai yana ta ƙara improving, ma sha Allah! Kin yi amai yau?" Gyaɗa masa kai tayi tare da faɗin, "Sau ɗaya kawai. Amma babu zazzaɓi sai ciwon mara, amma yanzu ban jin komai." "Ina sha Allah zaki zo ki daina gaba ɗaya." Ita ta taimaka masa wajen shiryawa. Yana gama saka kaya yayi mata kiss a goshi tare da fita daga ɗakin don an soma kiraye-kirayen sallah. Da ya sauko bai ga Aina'u a parlour ba, tsaki yayi tare da faɗin, "Da ƙafafuwan da kika zo zaki gudu. Na san maganin ki." Ya faɗi tare da ficewa daga ɗakin. Bai dawo ba sai da aka idar da isha'i. Yana shigowa ya sami Aina'u da Sarah a parlour suna hira, bai ce komai ba ya haura sama, ko gaba shigewa bai yi ba Sarah ta miƙe tabi bayansa. "Shegiya fitinanniya mayyar miji, za kici ubanki ne." Faɗin Sarah ƙasa-ƙasa. Tun daga nan bata ƙara jin motsi Sarah ba sai washe gari ƙarfe sha ɗayan safe, shima Khalil ta rako wande ke sanye da ash ɗin suit na kamfanin _Tom Ford_, gashin kansa yayi luwai-luwai yasha gyara. Sai ƙamshin _Imperial Majesty_ yake yi. Dama kuma Aina'u ta jima tana zaune tana duban hanya ta inda zasu fito. "Ina kwana? Har zaka fita kenan? Ka tsaya kayi breakfast mana na girka maka." Ba tare da ya kalleta ba yace matata ta riga ta bani abinci na kuma ƙoshi, Wife bye-bye ki kular min da kanki." Ya ƙarisa maganar yana mata kiss a goshi. Hannu ta ɗaga masa tana faɗin, "Allah ya tsare, kar dai ka bar min kanka da yunwa, ka tabbatar kaci abinci." "Ina sha Allah" ya faɗi tare da fita. Aina'u kuwa kamar zata fashe don baƙin ciki. "Sarah mai nayi wa mijinki ne? Naga kamar bai son zamana a cikin gidan nan." Kamo hanunta Sarah tayi tare da faɗin, "Kar kice haka Ai'n, Khalil nada kirki sosai, don dai baku saba bane kawai. Amma da kun saba zaki ce na faɗa miki." "To ni naga sai wani shashsha min ƙashi yake yi. Idan baku son zamana ai sai in tattara in wuce gida." Faɗin Aina'u. "kin cika ƙorafi wallahi, menene abun ɗaga jijiyoyin wuya haka? Sai dai idan kin gaji ne sai in tashi in ɗauko maki kuɗin mota a ɗaki." Faɗin Sarah. "To babu inda zanje ina nan a nan sai naga abunda ya turewa buzu naɗi." Aina'u ta faɗin cikin zuciya, amma a zahiri sai tayi gum. "Tashi muje side ɗin Hajiya." Faɗin Sarah tana miƙewa. Aina'un ma miƙewa tayi tabi bayan Saran. "Tooo, wannan mai suffar karuwai ɗin kuma daga ina, gashi dai tana ɗan kama da Aunty Saratu." Faɗin Laure cikin zuciya don jiya basu haɗu ba. Suna haɗa idanu, Aina'u ta sakar mata wani hararar da ya kaɗa ƴaƴan hanjinta tayi saurin kau da kanta. "Su Aina'u ne, sannunku ku ƙariso mana." Faɗin Hajiya tana nunawa Aina'un kujeran kusa da ita. Kamar mutuniyar kirki ta duƙa kamar jiya ta gaida Hajiya da kuma Aunty Maryam ɗin da tayi mata kallo ɗaya ta kau da kai. Laure kuma saurin juyawa tayi ta bar parlourn don kar ta gaida Aina'un don za su iya zuwa sa'anni ko Laure ta bata shekara guda. Anan suka yi yininsu, Sarah bazata taɓa iya tuna when last taga Aina'u na sallah ba sai yau da suka kai har la'asar a side ɗin Hajiya, amma kana ƙarewa sallar kallo zaka fahimci akwai naƙasu a cikinta, don dungure-dungure kawai take yi. Satin Aina'u guda, amma kullum bayan sun gama hira a side ɗin Hajiya sun dawo bata ƙara saka Sarah a idanu sai kuma gobe ƙarfe sha ɗaya ko sha biyu idan za tayiwa Khalil rakiya don tunda yayi aure bai cika fitar sassafen nan ba sai an kira shi emergency kasancewar akwai doctors a asibitin. Yau Aina'u ta shirya tsiyar da za tayi masu wanda zai hana su bacci, sai da ta bari dare yayi sosai sannan cire ribbon ɗin kanta ta hargitsa gashin kanta sannan ta kalli kanta sosai a madubi, daga ita sai wata transparent doguwar rigar bacci ko bra babu sai wani ɗan iskan pant mai igiya, murmushi tayi sannan ta isa wajen ƙofa ta fita ta nufi sama. Sai da ta isa ɗakin da ta tabbatar da nan ne suke ciki sannan ta riƙe handle ɗin ta soma jijjiga ƙofar da ƙarfi tana ihu tare da knocking. A wannan lokaci kuma Khalil na duniyar nishaɗi shi da matarsa suna raya sunna...........