Sashe 98
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yanda gaba ɗaya yanayinsa ya canza, sai ta soma ja da baya kaɗan-kaɗan tana kuma murza tafin hannunta a lokaci guda, sai dai gabanta ne ya yanke ya faɗi da ƙarfin tsiya jin bata ji wannan sanyin da ta saba ji ba a duk lokacin da ta murza tafin hannun, da saurin ta fiddo tafin hannun tana kallo gabanta na wani irin zullon tashin hankali, "Na shiga uku tafin hannuna yayi baƙi!" Ta faɗi da ƙarfi ganin har hayaƙi yake yi, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Khalil ya wani irin shaƙo wuyanta tare da ɗagata ya buga a ƙasa dai-dai lokacin da Laure ta shigo parlourn da gudu tana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Hajiya hayaƙi a ɗakinki." Cak ta tsaya tana mai kai hannu kan maƙogwaronta tare da kallon Hajiya da itama take kallonta cikin tsantsan mamaki da kuma farin ciki. Laure nuna bakinta tayi sannan ta nuna Hajiya cikin mamaki, hajiyan sai ta gyaɗa mata kai alamar eh tabbas taji fitar muryanta. Kuka Laure ta fashe dashi tare da kai goshinta ƙasa tayi sujada. Khalil kuwa wani irin kwallon tashin hankali ya riƙa yi da Aina'u tana buguwa da edge ɗin bangon ɗakin yana faɗin, "Mahaifiyata kika ɗaga hannu kika mara? Mahaifiyar tawa!!" Baki, kai da hancin Aina'u sai tsiyayar da jini yake yi tsabar naushi da Khalil ke aza mata, da sauri Hajiya ta nufi Khalil tare da faɗin, "Mu'azzam ka sake kyaketa haka, ka kyaleta nace!" Faɗin Hajiya da ƙarfi, shi kuwa Khalil bai saurareta ba ya cigaba da naushin Aina'u a duk inda ya samu a jikinta, fuska, baki, ciki da ƙirjinta duk sun nausu, sai da Hajiya ta shiga tsakiya tukunna Khalil ya dakata da dukanta, ita kuwa Aina'u sai tsiyayar da jini take yi, tafin hannunta kuwa ta murza yafi sau shurin masaƙi. Ganin Hajiya a tsakiyarsu, da sauri ta rarrafa ta fice daga ɗakin ta nufi ɓangaren Sarah riƙe da cikinta. Tana shiga sama ta haura zuwa ɗakin Khalil ɗin tare da duƙawa ta janyo tukunyar tsafinta, sai dai tana gama fuddoshi ya bada sautin fuuus ya watse a ɗakin, nan da nan ɗakin ya ɗauki wani irin ɗoyi, kuma hayan yayi daidai da wani irin murɗawa da cikin Aina'un yayi, ƙafafuwanta su hau wani irin rawa, idanunta na wani irin far-far-far kamar wacce kwayar idanunta zasu faɗo ƙasa, nan da nan wani irin guguwa ya tashi a tsakiyar ɗakin na kusan tsayin mintuna biyar kamun _Hell Ofulafu_ ya bayyana a tsakiyar ɗakin rabin fuskansa a ƙone, shi kuwa mummunar halittar nan gaba ɗaya jikinsa a ƙone yake. Wata shimfiɗeɗiyar bulalace a hannun Hell Wanda gefe-gefe bulalan wasu irin manya-manyan ƙayoyi ne masu matukar tsini da kaifi, jikin Aina'u wani irin rawa ya ɗauka ganin Hell da wannan bulala. Ɗaga bulalan yayi tare da shimfiɗa mata sai da ya zagaye jikinta har zuwa kan fuskanta, wani irin ihuu ta saki wanda ya ɗauki gidan gaba ɗaya, nan da nan jikinta ya hau tsirtuwar jini har zuwa fuskan, don bulalan yana sauka a kan fatan jikinta ya taho da fatarta, haka ya dunga zubaba mata bulalan tana ihu tana birgima, bayan ya gama farfashe jikinta sannan ya zaro wata doguwar ƙarfe wanda kallo ɗaya zaka yiwa Ƙarfen zaka tabbatar ya ɗauki awanni a cikin wuta saboda irin jan da yayi. Ba tare da tausayi ba ya dunga ɗaura wannan ƙarfen a ko'ina na fatar jikinta, Aina'u tsabar azaba ko kuka ta kasa yi sai wani jan numfashi da ta riƙa yi. Hello bai haƙura ba sai da ya banƙare Aina'u sannan ya fiddo da wani abu kamar kwaɗo mai matukar muni da azababben wari ya tura cikin gabanta sai har sai da tsintsiyar hannunsa ya shige ciki. Aina'u wani mahaukacin gurnani ta saki wanda ya taho da wani mulmulallan jini da bakinta, Hell na ciro hannunsa a gabanta jini ya biyo baya baƙiƙƙirin mai masifaffan wari. Wani irin dariya ya shiga ɓaɓɓakawa kamun ya dafa mummunar halittar nan suka ɓace, Aina'u kuwa sai wani irin birgima da buga kanta a ƙasa take yi saboda mummunar azabar da take yi mai wuyar fasaltuwa, bayan jinin dake biyu jikinta da gabanta, wani manya-manyan tsutsotsi da ƙananan baƙaƙen kunamu suka shiga fitowa ta gabanta kuma masu cizo da tsungulin, Aina'u sai zaro harce take yi tana wani irin surutan gigin azabar da take ji a cikin jikinta. Wani irin ɗaukar zafi jikinta ya soma yi kamar ana dafa mata jikin, da kyar ta iya cire komai na jikinta tana wani irin gurnanin azaba, kuka ta fashe dashi gani yanda tsokar naman jikinta ke yankowa yana faɗowa kuma duk tsokar data faɗo, wasu fararan tsutsotsi ne ke mamaye wajen suna tsungulin jikinta. Hatta naman dake wuyanta zazzagowa yayi ya faɗo kana ganin tafiyar maƙogwaronta, idanunta sunyi wani irin ɓulu-ɓulu sun zama abun tsoro, cikin ƴan wasu mintuna gaba ɗaya kamannin Aina'u ya sauya ta koma wata abun tsoro, fuskansa ya mokaɗe, bakinta ya turo yayi tsini kamar na kare, haƙoranta sun turo sunyi cirko-cirko a baki. Ɓangaren Hajiya kuwa, Khalil na tsaye ya yanke jiki ya faɗi yana wani irin jijjiga kamar mai farfaɗiya, ruɗewa Hajiya tayi tana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Laure! Laure!! Laure na shiga uku ki taimaka min ya zanyi." Daidai nan aka murɗo ƙofar aka shigo, ya Abdul-Hakeem ne da Aunty Maryam ce wacce tayi wani irin mahaukacin rama kamar wacce ta tashi daga ciwo, "Alhamdulillah, Abdul-Hakeem taimaka min mu kaita asibiti dan Allah!" A raunane Aunty Maryam tace, "Hajiya ba asibiti za'a kai shi ba, daddyn moon ɗauke shi ka mayar dashi kan kujera ka bashi wannan maganin mu gani." Ta ƙarisa maganar tana mai fiddo wani goran magani a cikin jakarta. Cicciɓarsa ya Abdul-Hakeem yayi tare da mayar dashi kan kujera sannan ya karɓi goran hannun Aunty Maryam ya bude tare da buɗe bakin Khalil yayi bismillah ya zuba masa har sau uku. Cikin minti ɗaya ya miƙe da sauri yana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Ya faɗi hakane tare da ɗaura hannunsa biyu a kai yana girgiza kai. "Hajiya meke damuwa? 'Hajiya mafarki nayi ko? Ba gaskiya bane duk abunda na gani ko? _Ƙanwar matata_ bata zo cikin gidan nan ta raba ni da matata ba ko? Hajiya Sarah tana ɗakinta ko?" Dafa shi Hajiya tayi tare da faɗin, "Kwantar da hankalinka Khalil, dawo cikin na tsuwarka." Da sauri Khalil yace, "Hajiya natsuwata baza ta taɓa dawowa ba har sai kun faɗa min duk abunda nake tunanin ya faru bai faru ba. Hajiya kinsan abunda ke min gizo a idanuna kuwa? Hajiya kin san bala'in da nake gani kuwa!" Da wani irin ihu yake maganar domin kwanciyar da yayi da Aina'u agaban twins da Sarah kawai yake dawo masa cikin idanunsa. "Khalil ba mafarki kake yi ba!" Faɗin ya Abdul-Hakeem. Wani irin duum Khalil ɗin yaji a cikin kansa, "Dagaske ne na koreta, dagaske ne da kaina na kori matata, dagaske na kwanta da _ƙanwar matata_ agaban matata da ƴaƴana. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wai meke faruwa dani ne, ku faɗa min!" Ihun da yayi sai da ya razana kowa a cikin ɗakin. Ya Abdul-Hakeem ya kalli Aunty Maryam tare da faɗin, "Mommyn moon yi masu bayanin da kika min!" Hawaye na kwaranyo a idanun Aunty Maryam ta soma faɗin, "Hajiya tun da uwata ta haife ni, ban taɓa ganin azzaluma kuma mushrika irin Aina'u ba, duk wani bala'in dake faruwa a cikin gidan nan sanadinta ne, Aina'u itace sanadin kurmancewar Laure, rashin lafiyar da kika yi har ya zazzago da idanunki, rashin kiranki da ya LTG da ya barrister, domin ita ta karkatar da hankalinsu da barin nemanki, mutuwar jinjirar Nafeesa da kuma korata da daddyn moon yayi har da dakatar dashi da akai a wajen aiki. Aina'u matsafiyace ta gaske, domin bokanta a tare da ita yake koda yaushe, tana matsa tafin hannunta yake bayyana a ciki, sannan kuma tana kallon komai da kowa dake cikin gidan nan ta cikin tafin hannun, har kisa tana iya aikatawa ta hakan. A ranar da na kamata tana magana da bokan, a ranar ta saka ya Abdul-Hakeem ya sake ni, sannan tayi min kashedi akan idan har na faɗawa wani abunda naga tana yi, sai tayi min irin abunda tayiwa Laure. Tun da na bar gidan nan, kullum a firgice nake kwana har na tsawon shekara ɗaya da rabi duk da cewar wata na biyu a gida baban moon ya turo min da text akan ya mayar dani sai dai kuma inyi haƙuri ba zai iya dawo dani cikin nan gidan ba, a hakan nayi ta hakuri ina kai wa Allah kukana babu dare babu rana, ban taɓa tunkarar kowa da Maganar ba, sai ranar da naje taron wani wa'azi a makarantar da nayi sauka, sai nayi katari malamin yana ta wa'azi akan harkan bin boka har da kuma addu'o'in da mutum zai lazimci yi domin kariya, tun da na fara wannan addu'o'in babu dare babu rana ina roƙon Allah ya karya alkadarin Aina'u da tsinannun matsafanta, cikin ƙanƙanin lokaci tsoran Aina'u ya fita daga cikin zuciyata har na nemi mijina na bashi addu'o'in shima da kuma magungunar da zai riƙa sha da kuma turare gidan, to sai kuma kwanakin baya yazo ya faɗa min kin kawo almajirai sunata sauke alƙur'ani, sosai hakan yayi min daɗi ganin zamu haɗa hannu mu yaƙi azzaluma Aina'u. Khalil kayi haƙuri, Allah zai saka mana kai da matarka, domin ta cutar da kowa na cikin gidan. Kuma Allah ba azzalumin bawansa bane, baya taɓa kama mutum da laifin da ya aikata ba da gangan ba, kayi komai ne bisa tsafi da makirci irin na shaiɗaniya kuma annoba Aina'u." Da wani irin speed Khalil ya bar ɗakin ya nufi nashi side ɗin, Hajiya da ya Abdul-Hakeem har da Aunty Maryam da Laure suka bi bayansa. Khalil bai tsaya murɗa handle ɗin ƙofar ba, kafaɗa ya saka ya bugi ƙofar da wani irin mahaukacin ƙarfi sai ga ƙofar a ɓalle, faɗawa ɗakin yayi idanunsa a rufe tsabar zafin zuciya da fusata, dai-dai nan ya Abdul-Hakeem ya faɗo ɗakin shima, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Faɗin ya Abdul-Hakeem da ƙarfi saboda ganin wani mummunar halitta mai ban tsoro a nannane kuma fatar jiki na zagwanyewa sannan tsutsotsi na fita, ga kuma