Sashe 18
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka Sarah ta fashe dashi tare da fad'in, "Tun da na taso nake tsan-tsan da jikina. Bana k'aunar irin rayuwar da y'an uwana suke yi. Abun yana mun ciwo sosai a zuciyata, hakan ya saka na d'auki alwashi in Sha Allah babu wani d'a namijin da zai sanni matsayin y'a mace, sai mijin da ya biya sadaki ya aure ni. Amma ka rusa min tsari, ka cuce ni kayi min ciki. Ka jefeni da bak'in fentin da ba zai tab'a goguwa ba a rayuwata. Aure na saura sati hud'u, na dad'e ina burin zama matar aure, amma ka rushe min wannan burin, ka jefa ni a sahun sauran y'an uwana masu tab'o a goshi. Yanzu mai zan ce da wannan d'an idan ya fito duniya. Ta yaya zan yi masa bayani idan ya tambayeni ina mahaifinsa. Tabbas ka aikata abunda kace zaka aikatan, dama wancen ranar kace min sai ka min abunda har abada ba zan tab'a mancewa ba, kuma tabbas har abada bazan mance ba, kuma wannan abu zai ta bibiyata har mutuwata. Mai nayi maka bawan Allah? Mai yasa zaka min wannan cutar? Shin baka da k'anwa ne? Idan wani yayi mata abunda kayi min, ya zaka ji a zuciyarka? Baka tunanin Allah zai iya rama min abunda kayi min a kan y'ay'anka! Duk abunda kayi sai an......" Bai bari ta k'arisa ba ya saka tafin hannu ya toshe mata baki tare da k'ureta da idanu kamar zai fashe da kuka. "Nayi maki rantsuwa da girman ubangijin daya halicceki, ya halicceni da duk abunda yake cikin duniya, wallahi, tallahi ban tab'a zina ba, ba d'abi'ata bace. Na bar abunda ya faru tsakanina dake matsayin K'addara ko kuma ince maki jarabawa. Sarah tun lokacin da wannan abun ya faru, ina dai rayuwa ne kamar ina cikin farin ciki amma kuma a bad'ini abun ba haka bane. Shaidan ne da kuma zafin zuciya ya rinjayeni. Amma ni banda niyyar cutar dake. Ke shaida ce a wancan ranar da niyyata shine cutar dake, duk da na fahimci ke d'in cikakkiyar budurwace, da ba zan kyaleki ba sai na ratsa jikinki. Allah yayi sai nayi ajiya a cikin shiyasa har na samu natsuwa a wajen jikinki. Ki yafe min Saratu! Ki yafe min tabbas na b'ata maki record. Amma ina so ki saka cikin ranki, wallahi tallahi tun bayan da abun nan ya faru Allah ya jarabceni da zazzafar soyayyarki, kuma nayi maki alk'awarin sai na share maki hawaye na cika maki burinki na zama matar aure. Ni nan _Ibrahim Khalil Nasuruddeen_ zan aureki in killaceki a cikin gidana. Zan taya ki rainon d'anmu ko y'armu har ya fito duniya, bayan nan kuma ko sati baza ki k'ara a gidanku ba zan aureki." Mik'ewa Sarah tayi tare da fad'in, "Bana fatan ka kasance matsayin mijina. Domin ban san a matsayin mai zan rik'a kallonka ba. Cuta dai ka riga ka gama cutata. Ka b'ata min record. Idan har na aureka zan rik'a kallo kamar ba don Allah ka aureni ba. Kaje kayi rayuwarka nima nayi tawa. Kaje ka samu y'ar masu kud'i da asali dai-dai kai, nima kuma idan ina da rabon auren a duniya, Allah zai had'a ni da dai-dai ni." Da sauri _Khalil_ yasha gabanta tare da fad'in, "Kar ki min haka Sarah, dan Allah kar ki hukuntani ta haka. Wallahi tallahi, Allah shine shaida na akan irin k'aunar da nake maki. Dan Allah don't reject me Saratuuu." Gitta shi tayi tare da fad'in, "Y'ay'an masu kud'i zasu iya yin komai saboda suna da wanda ya tsaya masu, ko da kud'in su zasu iya taka kowa kuma ya taku. Na san idan kaso yau ba zan k'ara kwana a duniya ba, sai dai ina rok'onka da girman ubangijin ka fita daga harkata, kar ka k'ara kusanto inda nake ko kuma ka nuna ka sanni. Idan kayi min haka, wata k'ila in iya ji a zuciyata zan iya yafe maka." Kallonta ya dunga yi yana jin k'una cikin zuciyarsa, "Sarah rayuwarki a hannuna take da zaki ce idan naso ba zaki kwana a duniya ba yau? Dan Allah kar ki k'ara wannan maganar. Da mai kud'i da talaka duk d'aya ne a wajen ubangiji. Ke baki san talaka yafi mai kud'i kwanciyar hankali ba. Bama wannan ba, kin san da cewar idan Allah yaga dama sai ya kwace dukiyar da ya bawa mai kud'in ya bawa talaka har sai wannan mai kud'in ya dawo yana naima k'ark'ashin talaka. Dani dake bamu da wani bambamci Sarah. Dan girman ubangijin ki gafarceni kar ki min azaba da rashin amincewarki." Kau da kai Sarah tayi tare da fad'in, "Bud'e min k'ofa in wuce gida, don idan zamu wuni mu kwana mu kuma k'ara kwana amsa ta d'aya ce a gare ka. Kaje ka naimi dai-dai da kai." Wani abune yazo ya tokare wuyarsa, tun da yake a duniya bai tab'a furtawa wata mace Kalmar so ba a rayuwarsa, sai dai shi ba zai iya k'irga adadin matan da suka furta masa kalmar ba. Y'ay'an masu kud'i, turawa har da indiyawa, amma bai tab'a bawa d'aya daga cikinsu full attention d'insa ba balle har soyayya ta k'ullu. Amma wai yau gashi gaban k'aramar yarinya yana rok'onta akan ta soshi tana wasa da zuciyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke, miskilancinsa suka hau kai tare da jik'imarsa, wani irin kallon gefen idanu ya bita dashi tare da fad'in, "Haka kika ce? So be it! Amma kuma ni zan tabbar maki babu wannan macen da _Khalil_ zai bud'e baki yace yana sonta ta k'i. Kamar yanda d'ana yake kwance a cikin mahaifarki, to haka _Khalil_ zai kasance cikin zuciyarki, sannan kuma wallahi babu wannan namijin da ya isa ya shiga gonar _Khalil_. Idan har ba _Khalil_ zaki aura ba, to zo rubuta ki ajiye babu ke babu aure!" Yana gama fad'in haka ya koma ya zauna ya soma danne-danne cikin computer yayi kamar ya manta tana cikin office d'in. Sarah kuwa da ta gaji da tsayuwa sai ta sulale k'asa ta zauna tana mai da numfashi. Da gefen idanu ya kalleta, sai kuma ya d'ago gaba d'aya tare da fad'in, "Wallahi wallahi idan baki tashi a k'asan nan ba kika bari nazo wajen nan zan baki mamaki!" A fusace Sarah tace, "Wani mamaki? Nace wani mamaki ne kuma ya rage baka bani ba." Ba tare da yace komai ya mik'e a fusace. Ko kamun yayi taku d'aya ta mik'e da sauri ta zauna a kan kujeran dake fuskantarsa. Wani dariya ne ya taho masa amma yayi saurin mayar dashi tare da kau da kai yana murmushi don dama ba zuwa wajenta zai yi ba, kawai barazana ce domin ta bar tiles d'in saboda sanyi. Zama yayi tare da cigaba da abunda yake yi. Ita kuma Sarah sai harare-harare take yi. Sun kwashi kusan awa guda sannan ya mik'e tare da fita ya kullo k'ofar. Sarah na ganin ya fice kuma ya kullo k'ofar ta kifa kanta akan desk d'in ta fashe da kukan bak'in ciki. Shi kuwa _Khalil_ yana fita suka ci karo da doctor Kamal dama kuma wajen _Khalil_ d'in zai zo. "Wajenka dama zan zo." Gyara tsayuwa yayi tare da yin bake-bake a k'ofar office d'in ya wani ci d'aci tare da fad'in, "To gani!" Sai da doctor Kamal ya kalli k'ofar office d'in sannan yace, "Ka kira ni emergency akan inzo nan kai zaka je yin wani abu, sai kuma gaka na ganka tare da wannan yarinyar. _Khalil_ ba halinka bane. Dan Allah kar kace zaka zubar mata da cikin dake jikinta. Y'an iskar yara sai sun gama yawon banzan su a tit....." A mugun tsawace _Khalil_ yace, "Enough! Enough doctor Kamal Isah Bashir! Kar ka k'ara jifan Sarah da wad'annan kalmomin. Sarah ba irin matan da kake tunani bane." Baki bud'e doctor Kamal ke kallon _Khalil_ don bai tab'a ganinsa a irin wannan yanayin sabida mace ba. Macen ma mai d'auke da cikin shege. A iya sanin da yayi wa _Khalil_ ya tsani y'an iskan mata. " _Khalil_ this lady that you're protecting haka, she's prostitude! Duk abunda zata fad'a mak......" Bai kai k'arshen zancen ba yaji wani gigitaccen mari ya sauka akan kuncinsa sai da yayi saurin saka hannu ya dafe kuncin yana mai kallon gefe-gefe. Ganin babu kowa kuma babu wanda yaga komai sai ya kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Ibrahim ni ka mara? Ni ka mara saboda ina fad'a maka gaskiya." Wani kallon banza yayi masa tare da fad'in, "To hell with the fucking stupid gaskiya gaskiyarka. Idan bakinka ya kuma kuskuran kiran matar da zan aura da karuwa, na rantse maka da ubangijin rana da wata sai na d'aureka kuma babu uban da ya isa ya fito da kai. Kuma cikin jikinta it's mine. Na fad'a da babban murya, cikin dake jikin Sarah, nawa ne! Kuma duk uban da ya isa ya kira ta da karuwa yaga abunda *_Ibrahim Khalilullah Nurudden_* zai aikata." Yana gama fad'in haka ya wuce fuuuuuu ya nufi pharmacy domin d'auko mata magunguna don tun d'azu yake lura da ita jiri take gani kuma babu k'arfi a jikinta. Shi kuwa doctor Kamal da mugun tsananin mad'aukakin mamaki yabi _Khalil_ d'in da idanu. Don ya mugun sanin hakinsa. In fact tare suka yi karatu a _London_ har kammalawan su. Yasan yanda ya tsani Zina da kuma mazinatan. Sannan yaga mata kyawawa iri-iri, turawa, indiyawa, larabawa duk bai fad'a halaka ba sai akan wannan tatsitsiyar yarinyar duk da ita ma kyakykyawar ce. Shafa kumatunsa da suka ji mari yayi tare wucewa ya bar wajen. _Khalil_ kuwa sai da ya d'auko duk magungunar da yasan Sarah zata buk'acesu sannan ya dawo office d'in hannunsa d'auke da leda mai tambari da sunan asibitin still kuma fuskansa a mugun d'aure. "Ki tashi in mayar dake gida." Ya fad'i sounding command. Cikin sauri ta mik'e shi kuma ya fita tabi bayansa. Kulle k'ofar yayi tare da fad'i, "Kiyi tafiya a hankali kar ki fad'i. Ko in rik'e ki?" Da jin haka tayi saurin yin gaba don taga alama sam bai da kunya. Har wajen motarsa suka isa, shi ya bud'e mata gidan gaba ta shiga sannan ya zaga ya shiga driver sit sannan ya tada motar yayi reverse ya bar cikin asibitin. A hankali ya dunga tafiya ba tare da ya k'ara ce