← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 112

Sashe 37

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 6 min read

saba yi ba a gaban Abdullah sabida suna shakkarsa. _Khalil_ kuwa da ya samu labari, sai da ya shiga d'aki ga kulle k'ofa sa hau tik'ar rawa kamun nan ya kira Sarah ya shaida mata abunda ake ciki. Itama dad'i ne ya kasheta. Bayan sun gama wayar ta fita tayi alwala ta dawo d'aki tayi raka'a biyu ta dunga rok'on Allah akan Allah yasa ayi wannan auren kada shima ya rushe kamar na baya. Don sosai ta saka _Khalil_ a cikin ranta. Bayan magriba _Khalil_ yazo har gida ya fad'awa Baba in Sha Allah gobe iyayensa zasu zo domin neman auren Sarah. Baba ya shaida masa babu komai sai sun zo. Bayan fitar _Khalil_ sai da Baba yayi hawaye tuno y'an uwansa na _Wamba_ don da yana tare dasu, da su zasu karb'i wannan aure. Haka nan ya aiki Sarah ta kira masa abokansa guda uku wanda suka had'a Sana'a tun suna matasa. Da sukan zo gidan su dubasa, amma ganin irin tijara da zagi da Lami take masu, sai suka d'auke k'afarsu a gidan, sai dai idan suka had'u da Sarah sai su aiketa da gaisuwa, idan kuma suna da d'an wani abu, sai su bata ta kai masa. Har gidan suka zo, da suka ji dalilin kiran kuwa, ba k'aramin farin ciki suka ji ba, kuma suka tabbatar masa da goben in Sha Allah dasu za ayi komai. Washa gari misalin bayan la'asar, sai ga jiniyar motocin sojoji, su kawu suna cikin nasu motar, shi kuma ya Abdullah yana cikin nashi a tsakiyar convoy, sai kuma wata sabuwar mota dal da wani soldier ke driving. A k'ofar gidan suka yi parking. Soldier ya bud'ewa ya Abdullah mota tare da sara masa ya k'ame. Bai fito ba, nuni kawai yayi masu da wata mota. Cikin k'ank'anin lokaci sojoji suka kwashe gaba d'aya abunda ke cikin motar suka yi ciki da su. Buhunhunan shinkafa kamar za'a bud'e shago, manya-manyan galolin manja da mangyad'a, huhunan goro, katon-katon na sweet da chewing gum, wani k'atoton centre carpet wanda kud'insa ya kai 500k, sai wasu had'ad'd'un takalma k'afa ashirin da wani k'atoton akwati wanda babu komai a cikinsa sai lesses da atamfofi masu tsadar gaske da kuma Key d'in mota. Gaba d'aya uban kayan, kayan saka ranar auren Sarah da _Khalil_ ne. Har dasu gas da manya-manyan stainless steel irinsu bokiti da. Irin dai al'adar da ake yi. Ga manya-manyan juices na kwali da na goro har da ruwan gora kala-kala. Lami kuwa mad'aukakin mamaki ne ya kamata don bata san da zuwansu ba. Baba bai fad'a mata ba, haka ita ma Sarah bata ce komai ba. Sai da aka gama shigar da kayan tsaf sannan ya Abdullah ya ziro k'afarsa ya fito dai-dai lokacin da su uncle suma suka fito. Abokan Baba su suka yi masu jagora har cikin d'akin Baba, sosai ya Abdullah yaji dad'in ganin gyaran da _Khalil_ d'in yayi wa baban da kuma ganin ya soma samun sauk'i. Bayan gaishe-gaishe sai suka fara magana akan abunda ya kawo su. "Aure dai bama so a saka ki da tsayi. Idan ma baku shirya ba, mu ashirye muke don bama buk'atar komai naku." Fad'in uncle Ridwan. Sam maganar bata yiwa ya Abdullah dad'i ba. Kuma sai da hakan ya nuna a fuskansa. A natse ya Abdullah ya soma magana, "Baba, uncle yana nufin idan babu takura, muna so kar bikin ya wuce sati biyu. Kar ka takura kanka, Saratu kawai muke buk'ata a gidanmu, amma idan kana ganin kana da naka uzurin, za muyi na'am da duk lokacin da ka saka." "Kaji d'an iskan yaron nan yana k'ask'antar damu a gaban wannan wulak'antaccen fak'irin mutumin. Shi har ya isa yana talaka ya ja da maganar mu" fad'in Uncle Ameeru amma cikin zuciya. Ba Baba bane yayi magama, abokinsa Baba Isma'ila ne yace, "A'a babu komai. Lokacin da kuka saka d'in ma yayi. Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi." Cike da girmamawa ya Abdullah yace, "To mun gode Allah ya saka da alkhairi. Ga wannan makullin motar, Hajiya ce ta bada kyauta a bawa mai sunan mahaifiyarta Sarah, kaya kuma gasu nan duk Hajiya ce ta lissafa mana muka sayo, tace na al'ada ne da ake yi idan za'a saka rana. Ga kuma sadaki nan." Ya fad'i hakan yana mai mik'a bunch d'in dubu-dubu guda biyar, jimilla ya kama dubu d'ari biyar cif. "Wannan kud'in ai sunyi yawa. Ba sayar da Saratu za muyi ba ai. Makullin mota kuma, ina naiman alfarma ku rik'e a wajenku duk lokacin da Sarah ta shigo gidan, sai ku damk'a mata." Sosai ya Abdullah yaji dad'in rashin ganin kwad'ayi a fuskan baba, sai yayi murmushi tare da fad'in, "Baba ai sadaki bai yawa duk da albarkan ake nema. Amma duba ga yanayin da muke ciki yanzu, ko billion aka bada kud'in sadaki, ai bai yi yawa ba. Zan dai mayar da makullin motar sai tazo tukun kamar yanda ka buk'ata, amma maganar rage sadaki kam ayi hak'uri." "To Allah ya sanya alkhairi ya sa ayi damu." Gaba d'aya d'akin aka amsa da amin. Bayan tafiyarsu, Baba ya ce su Baba sama'ila ko wannen su ya d'auki buhun shinkafa d'aya ya tafi dashi. Nan Lami ta daka tsalle tace ba zai yuwu ba tunda ba ubansu ya kawo ba. Ai kuwa Baba ya haukace mata kuma basu bar gidan nan ba sai da buhun shinkafa kowa d'aya. Don buhunar shinkafar guda ashirin ne ciff. Nan Lami ta dunga surfa bala'i ba'a fad'a mata za'a zo kawo kud'in auren Sarah ba, sannan kuma tace dole a fito da sadakin a raba. Ko kallonta Baba bai kuma yi na ya koma d'akinsa tare da yiwa sadakin Sarah mummunar b'oye don yayi rantsuwa kwandala ba zai bata ba tunda ba hakkinta bane shima kuma ba nashi bane. Gaba d'aya yaran gidan basa nan lokacin da aka kawo kayan auren Sarah. Sarah d'in ce kawai ke gida don ita bata zuwa ko ina. Lokacin da suka dawo kuwa, ba k'aramin rud'ewa suka yi ba ganin uban kayan saka ranar Sarah da aka kawo. Da Lami ta fad'a masu har da mota, yanke jiki Aina'u tayi ta suma, babu wanda yayi tunanin bak'in ciki ya saka ta ta suman. Data farfad'o kuwa kuka ta fashe dashi. Tambayarta suka soma yi, sai tace masu ciwon kai da basir ne ke damunta. Mintuna biyar bata k'ara yi a gidan ba. Ameeru, duba nan kaga abunda aka turo min da b'oyayyiyar number, karanto muji don Allah. Ni na kasa fahimta. _ASSALAMU ALAIKUM. NA SAN ZA KAYI MAMAKIN WANNAN SAK'ON DA NA TURO MAKA. ABUNDA YA SAKA NA TURO KUWA, GANIN GIDANKU GIDAN MUTUNCI NE, KUMA MAHAIFIN KHALIL YA RASU KOWA NA GANIN GIRMA DA K'IMARSA HAR KUWA YAZU DA BAYA CIKIN DUNIYAR. NA SAN BAKU YI BINCIKE BA GAME DA GIDAN DA KUKA JE KUKAI KAYAN AURE BA. TO INA MAI BAKU SHAWARA KU KOMA DA KYAU KUYI BINCIKE, DOMIN DAI YARINYAR NAN BA TA KWARAI BACE. BATA JIMA DA ZUBAR DA CIKI BA. RUFA-RUFA AKAI MAKU. GIDAN NAN BA GIDAN MUTUNCI BANE DOMIN TAKEN GIDAN SHINE *GIDAN KARUWAI* IDAN KUMA BAKU YARDA DA MAGANATA BA, ZA KU IYA YIN BINCIKE DOMIN TABBATARWA. DON YAYYIN YARINYAR BABU WACCE BATA AJIYE SHEGE BA. IDAN KUMA HAR KUKA AMINCE WANNAN YARINYA TA SHIGO CIKIN ZURI'ARKU, TO KAMAR FA RUWAN KWATA KUKA D'IBA DA HANNUNKU KUKA ZUBA A CIKIN RUWA MAI KYAU!_
Chapter 37 · 0% Book details