Sashe 48
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
garkuwa dani domin kud'i. Tunda kaga da zan ba'a yi hakan ba sai da aure na ya kusa kuma da d'an Chief Justice Nurudden Muhammad." Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "Ubangiji Allah ya kare ki daga sharrin mutum da aljan. Wannan aure kuma, idan ma anyi hakan ne domin a fasa,in sha Allah an riga an d'aura a sama, shaidar duniya kawai ake jira. Tashi kije ki kwanta, in Sha Allah da safe zan je can gidan liman Muhammadu inyi masa bayani komai. Ni kai na ban ji a jikina Muneeba zata had'a baki da wasu domin a sace ki. Amma zan je gidan gobe da safe." "To Baba Allah ya kai mu." Sarah ta fad'i tare da ficewa daga d'akin ta koma nasu. "Sarah kin tab'a karanta littafin hausa mai suna _Ayi dai mu gani_?" Fad'in Aina'u tana mai danna wayarta. Kallon Sarah tayi tare da fad'in, "Kin fara karatun novels ne na hausa?" Sarah ta fad'i tana mai kallonta. Ba tare da Aina'u ta kalleta ba tace, "Eh, yau kwana uku da na fara da wani littafi mai suna _Iska na wahalar da mai kayan kara_, yanzu kuma _Ayi dai mu gani_ nake karantawa." Girgiza kai Sarah tayi tare da fad'in, "Gaskiya ban karanta ba. Ban ga kinyi lalle ba, kuma har nan na turo mai lalli d'azu da safe. Su Na'ima duk anyi masu ja da b'aki." Tab'e baki Aina'u tayi tare da fad'in, "Ni kinsan lalli bai dame ni ba. Kuma da safe bani nan naje kitso. Za kuyi wani program ne?" Zama Sarah tayi a bak'in gadon tare da nannad'o gashin ganta ta tura cikin hula ta k'eya tare da jawo hulan har zuwa goshinta saboda kar gyaran kan da akai mata ya lalace. Tace, "Eh, naga duk su Na'ima ma sunyi kitson ai. Ni ko da da nake saka attachment, ba zan iya yin wannan uban k'ananan kitson ba. Na'ima muga naki, kamar yafi na Aina'u k'anana ko?" Sarah ta fad'i maganar tana kallon kan Na'ima wacce taja hulan kanta baya. "Wai! Gaskiya kitson yayi k'ana. Sauk'in ta ma a can inda kukai kitson ake tsefe maku." Nuratu tace, "Ni ko kinga nawa bai kai nasu k'anana ba. Ghana weaving akai min manya." Ta fad'i maganar tana mai jan hular kanta. "Ni da Hassana fixing kawai akai mata. Don wallahi naji bazan iya zaman kitson ba. Basir!" Fad'in Marfu'a tana mai zame Fadwa da ta gama shayar da ita daga jikinta ta kwantar. "Amma dai ba anan zata kwana ba ko? Don na tsani kukan daren nan da take yi. Duk ta hana mutum bacci." fad'in Aina'u. "To nan zata kwana. Ni ban san wani uban gulmar ce ta dawo dake kwana anan d'akin ba, ai da a d'akin Lami kike kwana." Cike da rashin kunya Aina'u tace, "To nan d'in naga damar dawowa da kwana. Ai gidan ubana ne." Ficewa daga d'akin Sarah tayi ganin zasu fara raba halin nasu da suka saba. D'akin Baba tayi sallama ta shiga. Zaune ta same shi a kan gado yana kallon Sunna Tv. "Baba dan Allah wayarka zaka ara min." Ba tare da yace komai ba ya d'auko wayar a gefensa ya mik'a mata ita kuma ta amsa tare da ficewa. Number d'in _Khalil_ tayi dialing, ringing biyu yayi sai yayi rejecting tare da biyo kiran. Sarah na d'agawa yace, "Assalamu alaikum Baba." Sarah sai ta canza murya tare da fad'in, "Wa'alaikassalam d'ana." A tare suka saki dariya, _Khalil_ yace, "Ke nine d'an naki? Za kiyi bayani gobe a irin wannan lokacin." Hararar wayar Sarah tayi tare da fad'in, "Bayanin mai zan yi? Ni babu wani bayani da zan yi." Dariya _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Kuma kin san na mance y'an iskan da suka d'auke min ke sun yar da wayarki, wallahi na kira yafi sau shurin masak'i, dole ma gobe da sassafe in kawo maki waya. Ba zan juri rashin jin muryanki ba." "To bayan gobe zamu kasance tare har abada." Sarah ta fad'i a kunyace. "Na'am, maimaita dan Allah love." K'it ta kashe wayar tare da mayarwa Baba wayarsa. Daga can kuwa _Khalil_ kamar ya fasa ihu, yana tsoron kira yaji wayar a hannun Baba. Washa gari da sassafe kamar yanda _Khalil_ ya fad'i, sai gashi da sabuwar waya k'irar LG mai tsananin kyau da tsada, wani tsohon MTN sim d'insa ya saka mata a ciki ya kawo mata. Na'ima ta fito zata shago ta gansu a tsaye suna magana. Wani irin kyau suka mata, sai taga kamar anyi su don juna ne don ba k'aramin dacewa suka yi ba. "K'anina ayi hak'uri haka, anjima kad'an zamu kawo maka ita." Murmushi kawai _Khalil_ yayi ita kuma ta wuce. Dai-dai nan Muneeba ta iso wajen, tana ganin _Khalil_ ta juya da sauri. Shima _Khalil_ da sauri yabi bayanta yana kiran sunanta don jiyan sunyi magana sosai da ya Abdul-Hakeem ya fahimtar dashi Muneeba bata da hannu a ciki. "K'awarmu dan Allah kiyi hak'uri da abunda ya faru jiya. Tashin hankali ne ta saka nayi abunda nayi. Koma wanene a matsayina abunda nayi shi zai yi. Kiyi hak'uri kinga ma na kama kunnena. Kar ki manta ke kika ce min in kula da k'awarki sosai kada tayi kuka. To hud'ubarne ya shiga kunnena." Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Naji tsoro jiya, banyi bacci ba. Mama kwana tayi tana mun fad'a. Sai da baban Sarah yazo gidan mu yayi mana bayanin anga Sarah sannan hankalinmu ya kwanta. Wallahi ko a cikin mafarkina bai tab'a zuwarmin in cutar da Saratu ba." "Naji na yarda dake Muniba. Dan Allah kiyi hak'uri." Fad'in _Khalil_. Sai da ta murgud'a baki sannan tace, "Na hak'ura dan ba halinka ba." Sai ta juya ta kalli Sarah data k'ariso ta rungumeta tare da fad'in, "Alhamdulillah k'awata. Duk wanda yayi maki wannan abun Allah ya tona asirinsa." Da Ameen Sarah ta amsa tare da jan hannunta bayan ta d'agawa _Khalil_ hannu. Baki _Khalil_ ya bud'e tare da fad'in, "Har munyi sallama." Muneeba tace, "Anjima zamu kawo maka ita sai kaga dama ka barta tazo wajen mu." _Khalil_ kuwa cikin zuciyarsa cewa yayi, "Kamar kuwa kin sani. Don ina raba Sarah da wannan gidan, ko zata zo to tabbas ina jiranta a waje, tana gama gaishe da Baba zata fito mu wuce." Kan kace me, gaba d'aya gidan su Sarah ya cika da mutane har da y'an unguwa da basu tab'a shigowa ba. Don Na'ima gida-gida tabi ta kai masu chewing gum. Bamu abunda ke tashi sai k'amshin soye-soyen nama sa, rago da kaji. Don shanu k'osassu biyu aka yanka, raguna hud'u kaji d'ari da hamsin. Y'an matan zumunta kuwa sun fi hamsin sunyi ankon wani koriyar atamfa sai hada-hada suke yi baki na motsi. Sarah kuwa komawa gidansu Munee tayi don acan suke sitting. Mai make-up tazo ta tsan-tsara mata kamar ka sace ka gudu. K'arfe d'aya da mintuna sha biyu wasu uban jiniya mai tafe da convoy na ya Abdullah suka shigo layin kasancewar k'arfe d'aya da rabi za'a d'aura auren anan masallacin layinsu. Sai ga tawagar manya-manyan mutane da abokan mahaifinsu. Jos road kamar zata tsage sabida mutane. Muneeba hannun Sarah ta kama suka koma can d'akin Baba mahaifin Muneeban sabida kiran wayarta da _Khalil_ d'in yake ta yi don wayar Sarah na hannunta. Kuma nan gidan ma a cike yake da k'awayensu na islamiya da poly. Don duk sai da Na'ima ta gayyace su. Bayan ta bata wayar ta fita. Sarah na picking ta jiyo zazzak'ar muryan _Khalil_ na mata wak'a, If you make me clean I will be clean. If you make me whole I will be whole. If you make me yours I will be yours And I won't run anymore. If I seek you, will I find you there. If I call your name will you still hear Is it too late or can I start again Can I begin again Oh. Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Can you drown it in the deepest sea. Can you cast it far as west from east Can you raise me up to live again So I can live again Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go I'm surrendering my will You are crumbling all the walls I've built My defence is coming down Down I can't deny you I am broken open wide Now you can come inside My defences have come down Down I can't deny you I'm surrendering my will You are crumbling all the walls I've built My defence is coming down Down I can't deny you I am broken open wide Now you can come inside My defences have come down Down I can't deny you Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Don't ever let me go Don't ever let me go. "I will never let you go. Never, ever!" Fad'in Sarah. "And I'll always be there for you my love. Sai mun had'u anjima." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. Aina'u na tsaye a tsakar gida abun duniya duk ya isheta ta jiyo shalar da ya tsayar da bugun numfashin ta zube a k'asa sume. "An d'aura auren _Ibrahim Khalil Muhammad Nurudden_ da amaryarsa _Saratu Nuhu_ akan sadaki naira na gugan nera har dubu d'ari biyar, lakadan ba ajalan ba."