Sashe 105
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read
dani matuƙa, Kuma idan har Hajiya tayi nasarar rabani da matata, hmmm!" Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin da sauri hawaye na zubar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya Abdallah ya kirawo wani mai akori kura ya bashi 50k ya toshe hanci tare da saka glove, bayan lulluɓe jikin Aina'u ya kinkimeta ya saka a bayan akori kuran ya tada mota ya nufi jama'a road can gidansu Lami. Lokacin da aka shigo da Aina'u gidan, ihu Lami ta riƙa yi tana tuma a ƙasa, su Na'ima kuwa tsoron Allah ne ya ƙara huda zukatansu, duk da halin Aina'u sai da ta ɗan basu tausayi. Saboda tsananin warin da take yi, ɗaki ɗaya da akai masu ƙatoto saboda kiwo suka share sannan suka ajiye ta a ciki, babu abunda take yi sai tone-tonen abubuwan da tayi. Lami na jin sunan _Hell Ofulafu_ gabanta ya buga da ƙarfi ta fito daga ɗakin tana faɗin, "Rose Merry! Rose Merry ce kawai zata iya kai Aina'u wajen Hell! Yesu Almasihu ka kawo ƙarshe Rose a wannan rana mai albarka ta Sunday." Faɗin Lami tare da fizgar zanin dake kan igiya ta fita fuuuuuuuu. Saboda tsabar tashin hankali Lami ko abun hawa bai hau bata hau ba, haka tayi ta tafiya a ƙafa har ta isa gidan Rose Merry. Knocking ta hau yi a ƙofar gidan kamar zata ƙarya duk da kuwa akwai kwaɗo dake nuna alamun mutanan gidan basa nan, don anty Rose Merry idan ta tafi church duk Sunday bata dawowa sai bayan la'asar ko kuma gab la'asar. "Madam ai gidan a kulle yake, kalli padlock ɗin mana." Faɗin wata bayarabiyar mata mai ɗauke da ƙaton bawon gorunan magani a kai, sai a sannan ta kalli kwaɗon tare da kai hannu ta taɓa, zamewa tayi ta zauna akan dakalin gidan, don ji take ba zata iya taɓa tafiya ba tare da tayi ido huɗu da Rose Merry ba. Ta kusan awa ɗaya a wajen kamun Aunty Rose Merry ta ƙariso wajen cikin shigar farar atamfa mai ratsin sky blue, sai farar rigar less da kuma sky blue ɗin gwaggwaro. Tana ganin Lami ta washe baki tare da faɗin, "Elizabeth Akanchewa Uchendo, ƙawata, my childhood friend." "Stop that nonesense Rose Merry David Anthony! I came here to ask of what you did to my daughter! You've poisoned my daughter's heart Merry, Yesu Almasihu ya tsine maki, Ƙawancena dake babu alheri a ciki, ke guba ce, ke shaiɗaniya ce, kin kai min ƴata wajen azzalumin nan _Hell Ofulafu_, tun ranar farko da kika fara kai ni Abia na san wannan mugun mutum ne mara imani, duk tsafin da ake yi a gidanmu, baza su iya rashin imanin da Hell yake yi ba, yanzu na ƙara tabbatar da cewa kece kika kashe min ɗana Lukman, kuma ki sani, na rantse da tsafin Babana, You will pay for what you did!" Lami na gama faɗin haka ta juya zata bar wajen, da hannu ɗaya Aunty Rose ta jawo kafaɗanta tana wani irin murmushin mugunta, sai da ta juyo da Lami gaba ɗaya sannan ta kyasta babban yatsarta da kuma manuniya tare da faɗin, "Hey Elizabeth, do you think I came all the way from Nassarawa state to Kaduna, just because of our friendship? You're a fool, a big fool Elizabeth! Nazo Kaduna ne domin mijinki, don mijinki Elizabeth! Tun ranar da na fara ganin Nuhu, naji ina matuƙar ƙaunarsa, amma kuma sai kika min shigar sauri, sannan kuma kin tuna abunda Akanchewa Uchendo ina nufin mahaifinki yayi wa Babana, yayi masa asiri ya raba shi da mamana, ya raba shi da duka arzikinsa sannan ya mayar dashi makaho, Ni kuma gani har yanzu ban taɓa aure ba. Kina tunanin sai ni kuma in zuba maki idanu ki auri ɗan gidan malaman can, sannan kuma in barku kuyi zaman lafiya?" Sai ta girgiza kai tare da ɗaukar ƙafa ɗaya a kan dakali sannan tace, "Bari na faɗa maki abunda baki sani ba Elizabeth, nice sanadin lalacewar duka ƴaƴanki, Ni na kai sunanki wajen Hell, nayi amfani da kwaɗayin duniyarki, na saka Hell ya sakaki kika kai ƴaƴanki ga halaka, sannan ɗan ki tilo namiji na saka masa cutar sata da kuma shaye-shaye, ƴa ɗaya ce ta gagare ni, ita ce Saratu, Ni na saka Hell ya saka maki tsanar mijinki da jin haushinsa da kuma rashin ganin ƙimarsa, sannan Ni nasanwa mijinki karayar arziki bayan na nakasta ƙafarki, ƴarki kuma Aina'u, banyi mata komai ba, jinin mahaifinki ne ke yawo a jikinta, don ita ce tayo gadon ubanki gaba ɗaya har ta damesa ta shanye. Kuma Lami yanzu aka fara wasan a tsakanin mu. Ban san mai Aina'u tayi ba, amma tun da tace min tana so in haɗata da Hell na tabbatar Aina'u ɗiyarki ce, domin bata yada halinki dana mahaifinki ba. Mu zuba ni da ke Elizabeth!" Tana gama faɗin haka tayi wani murmushi tare da kaucewa ta nufi wajen ƙofa ta buɗe tare da shiga ta bugo ƙofa. Lami ta jima a tsaye tana jujjuya maganganun Rose Merry kamun taja jiki a sanyaye ta nufi gida. "Ai da zafi-zafi akan daki ƙarfe Hajiya Mariya, Ni dai idan har ba'a tsayarwa Habbooba miji ba, nayi wa Khalil kamu!" Faɗin Hajiya tana murmushi..............