← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 112

Sashe 60

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aina'u, lafiya?" Faɗin Sarah cike da mamaki. Aina'u wani haɗe rai tayi tare da faɗin, "Ban gane Lafiya ba. Ko bakya son gani nane in koma inda na fito?" Sauke ajiyar zuciya Sarah tayi tana ƙara kallon akwatin ta gefen idanu tare da faɗin, "Ya zaki ce haka Ai'n, kawai nayi mamakin ganinki ne." Aje akwatin tayi a nan tsakar ɗaki tare da zama akan one sitter tace, "Wash, akwatin nan ba dai nauyi ba, daga gate zuwa nan kamar zan mutu haka naji. Nazo taimaki ne ganin baki da lafiya, ina nan har ki haihu." Wani miyau Sarah ta haɗiye jin abunda Aina'un tace, ita damuwarta ɗaya, rashin kamun kan Aina'un na yawan surutun faɗi ba'a tambayeka ba. Bata so kyakkyawar alakar dake tsakaninta da Hajiya da kuma Aunty Maryam ya samu matsala sanadin Aina'u. "Ya ubangiji Allah maji roƙon bayi, kasa zuwan yarinyar nan gidan nan alkhairi ne." Sarah ta faɗi cikin zuciya. Taɓe baki Aina'u tayi ganin Sarah ta faɗa dogon tunani, cikin zuciyarta ta furta, "Kuma wallahi zama cikin gidan nan dole." Jiki babu kwari Sarah ta miƙe tare da faɗin, ɗauko akwatin naki na nuna maki ɗakin da zaki sauka." Miƙewa tayi tana wani taɓe fuska tare da jan akwatin, ta cikin second parlour suka bi zuwa bedrooms ɗin dake ƙasa, "Zaɓa ɗakin da kike so a cikin ukun nan sai ki zuba kayanki a cikin wardrobe." A yatsine Aina'u tace, babu ɗaki a sama ne sai nan ƙasa? Nafi son saman." Sai da Sarah ta kalleta sannan tace, "Eh babu, don can ɗin daga ɗakina sai nashi." A gadarance Aina'u tace, "To kuma bazan iya zama a naki ɗakin ba ko? Tunda ai naga a ɗaki ɗaya kuke kwana ke da Khalil ɗin." "Aina'u bafa zai yuwu ki zauna a sama ba, don zaki shiga haƙƙin mijina da ni karan kaina. Kiyi zamanki anan zaki fi walawa." Ba tare da Aina'u tace komai ba ta buɗe ɗaya daga cikin ɗakunan dake a jere ta leƙa, girgiza kai tayi irin bai matan nan ba ta buɗe ɗayan, shima dai bata shiga sai da ta duba na ƙarshen sannan ta fito ta dawo na tsakiyar ta soma jera kayanta cikin, duk da halin da Sarah ke ciki sai da ta taimaka mata wajen jera mata kayan. Bayan sun gama suka dawo parlour. Ko zaman mintuna biyar bata yi ba ta tashi tare da faɗin, "Tunda ba'a man tayin abinci ba, bari nayi wa kaina." Tana gama faɗin haka ta shige cikin kitchen tana waƙa. Da idanu kawai Sarah ta bita sannan ta girgiza kai. Indomie ta dafa da kifin gwangwani sannan ta ɗauko avocado Juice ɗin da Aunty Maryam ta haɗawa Sarah ko zata ta fito ta zauna a ƙasa. Wani irin kakarin amai ta soma yi tare da toshe bakinta tayi hanyar toilet ɗin dake parlour ɗin da sauri ta soma sheƙa aman a ƙasa. Aina'u kuwa wani taɓe baki tayi tare da faɗin, "Gama shan baƙar wahalar tukun, amma baza ki taɓa ganin kwanki ba a duniya in dai ina raye! Shegiya mayya mai ɗuwawun saurin ɗaukar ciki. To kin ɗauki ciki ma ba tare da saduwaba, inaga kuma an sadun.. Shegiya mahaifar zan yi sanadin lalacewarsa inga ƙarshen saurin ɗaukar cikin naki" duk a zuciya tayi maganar yayin da tayi kwafa a fili ta cigaba da cin indomie ɗin ta." Sarah kuwa tun tana saka ran ganin Aina'un tazo kawo mata ɗauki har ta fidda rai. Aina'u kuwa bayan gama cin indomie ɗin ko plate ɗin bata ɗauke ba ta hau kan kujera ta ɗauki remote ta kunna kallo. Sarah kuwa ƙaramar azaba tasha ba don babu komai a cikinta sai tsabar wuya da take sha. Da kyar bayan ta wanke jikinta ta dawo parlour ɗin ta dunga birgima a ƙasa tana riƙe ciki. Duk abunnan da take yi ko sau ɗaya Aina'u bata ce mata sannu ba. A hankali ciwon cikin dake damunta ya kafa, jirin da take gani shima kamar anyi ruwa an ɗauke, lokacin bacci har ya ɗauke Aina'u a kan kujeran da take kai. Kallon Aina'un tayi tana mamakin taurin zuciya irin nata ganin duk malelekuwar da take yi ko sannu bai haɗata da ita ba. Infact tama ɗan ɗago taga halin da take ciki bata yi ba, amma a hakan take cewa tazo zama da ita domin taimakonta har ta haihu. Tashi Sarah tayi ta haura sama ta shiga jacuzzii tayi wanka da ruwa mai zafi sannan ta fito ta tada sallar la'asar kasancewar ta ɗauro alwala kamun ta fito. Riga kawai ta zura da dogon hijjab ta tada sallah, bayan ta idar ta isa gaban madubi ta tantsara kwalliya kasancewar Khalil ya kusa dawowa don sau da dama a gida yake sallar magrib. Wando ta sanya pallazo kalar emerald green da shirt mai button kalar grey sai ta kama jekar shirt ɗin biyu ta ɗaure ta gaba. Gashin kanta kuma tayi parking ɗinsa in a low ponytail jelar gashin ya zuba har gadon bayanta. Turensa _Imperial Majesty kaɗai ta fesa tare da saukowa ƙasa, tun daga kan steirs Aina'u ke ƙare mata kallo ganin wari irin kyau da tayi, tayi haske sosai hips ɗinta kuma sun ƙara cika. Tana saukowa kai tsaye kitchen ta nufa tare da buɗe fridge ta ɗauko can fanta wanda yayi mugun sanyi ta dawo ta zauna kan kujera tare da ɗauka ƙafa ɗaya a kan ɗaya ta buɗe fanta ɗin ta shiga sipping a hankali tana lumshe idanun. Aina'u kuwa babu abunda take yi sai aika mata da harara ta gefen idanu. "Zuwa anjima kamun Happiness ya dawo za muje can cikin gida ki gaido Hajiya da sauran mutanen gida." Faɗin Sarah ba tare da ta kalli inda Aina'un take ba." "Ok" shine abunda Aina'u tace tana mai faɗin, "Nine ajalin farin cikinki, kiji daɗinki iya jin daɗi kamun turn ɗina ya zagayo. An kusa fara yaƙin wallahi, yaƙi ne da yafi na biafra!" Sai da tasha rabin fantan nan sannan ta mayar dashi cikin fridge tare da komawa sama ta ɗauko ƙatoton hijjab har ƙasa ta saka ta dawo parlour tare da faɗin, "Ki taso muje cikin gidan." Miƙewa tayi tabi bayan Sarah da tayi gaba tana yi mata daƙuwa a baya. Sallama suka yi, babu kowa a parlour sai TV dake ƙara, "Zauna anan ina zuwa." Sarah ta nuna mata kujera tare da wucewa tabi corridor ɗin da zai sadata da ɗakin Hajiya. Ai'n kuwa sai bin parlourn ɗakin take yi tana jinjina kai tare da mamakin dukiyar da aka kashe wajen tsara gidan gaba ɗaya, don ko ina ka kalla babu ƙarya. Tare Hajiya da Sarah suka fito daga ɗakin kamar ƙawaye, don ita Hajiya ƴaƴa ta ɗauki matan ƴaƴanta ba surukai ba. "Sannu da zuwa Aina'u, ai kin kyauta da kika zo taya ƴar uwarki jinya, Saratu na shan wuyar laulayi, don ma dai yarinya ce mai dauriya." Faɗin hajiya tana zama a kan kujera. Har ƙasa Ai'n ta zamo tare da faɗin, "Ina wuni Hajiya, mun same ku lafiya?" Cike da jin daɗi Hajiya ta amsa da "Lafiya ƙalau, ya wajensu mahaifiyarku?" Aina'u ta amsa da, "lafiya ƙalau" sosai Sarah taji daɗin yanda Aina'u ta gaida Hajiya. Sun ɗan jima a nan ɗakin Hajiya kamun suka tafi ɗakin Aunty Maryam, Kallo ɗaya Aunty Maryam tayi wa Aina'u taji sam bata kwanta mata a rai ba, sai dai ta amsheta faram-faram. Basu jima a nan ba suka komai side ɗin Sarah ganin har shida tayi. Ko mintuna biyar basu yi da dawowa ba Khalil ya dawo, yana danna doorbell Sarah ta saki wani murmushi don ta san shine ta tashi ta nufi ƙofa ta buɗe tana yi masa wani irin kallon love mai sumar da wanda ake yiwa. Hannun biyu ya saka ya kama ƙugunta tare da jawota kusa dashi yana kallon cikin idanunta tare da faɗin, "Mine, kin San fa baki da lafiya amma shine kike neman tsokalata da irin wannan kwalliyar da dressing ɗin ko?" Aina'u dake zaune kan kujera sai leƙo kai take yi tare da dogon wuya tana jin takaici na neman kasheta. Wani lunshe idanu Sarah tayi tare da kwantar da kanta a kan ƙirjinsa tace cike da shagwaɓa, "Tun ɗazu ni da babynka muke son jin ɗumin jikinka, gaskiya an kusa fara tafiya dani asibitin nan." Rungume yayi sosai tare da faɗin, "Lallai kuwa duk lokacin da na ajiye ki a office babu abunda zan iya aikatawa, don wallahi bazan iya duba ko petient ɗaya ba. Muje Wife ki kula dani kamun a kira sallah." "Uhm!" Aina'u tayi gyaran murya don ta lura har Sarah ta mance da zamanta a parlourn balle kuma Khalil da bai san tana wajen ba. A tare Khalil da Sarah suka kalli inda Aina'un take, lokaci guda fara'ar fuskansa ya ɗauke don shi tun asali bai ƙaunar Aina'u tun da ta dunga maimaita masa ya rabu da Sarah su gidansu ba'a aure yaji ya tsane ta. Kuma haka nan duk lokacin da zai yi arba da ita sai gabansa ya faɗi. Bai taɓa jin ya tsani Na'ima ko Hassana, Marfu'a da Nuratu ba, su da ya sha ganinsu a hotels daban-daban da maza kala-kala, amma Aina'un da bai taɓa kamata da kowa ba, sai yake jin muguwar tsanarta. "Ina wuni?" Faɗin Aina'u tana wani kwarkwasa. "Lafiya" kawai yace tare da ɗaukar matarsa cak suka yi sama. Da idanu Ai'n ta bisu hawaye na zubo mata, duk suka haɗa idanu da Khalil, babu abunda take hangowa sai wutar ƙiyayyarta. Yanzu hakan ma abunda ta gani kenan, yana ganinta mood ɗinsa ya canza. "Wife naga Aina'u har wannan Lokacin, bata jima da zuwa bane?" Faɗin Khalil bayan ya ajiyeta a kan gado. "Ta jima da zuwa, nan zata kwana!" Shuru Khalil yayi bai son ya fito ƙiri-ƙiri ya nuna mata bai son zaman Aina'u da su a gidan don ko yaya Sarah zata ji zafi tunda ƴar uwarta ce ciki ɗaya. "Kayi shuru Happiness!" Faɗin Sarah. Murmushi yaƙe yayi tare da faɗin, "She's welcome! Ai akwai ɗakuna da yawa a gidan, idan ma nan bai yi mata ba, ga side ɗin Hajiya." Murmushin jin daɗi Sarah tayi tare da faɗin, "Thank you love, nan ɗin ma ya ishe ta, har na saka kayanta a bedroom ɗin dake ƙasa." Miƙewa
Chapter 60 · 0% Book details