← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 112

Sashe 108

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 5 min read

da matar. Saki a matsayin zaɓi na ƙarshe: Ko da yake an halasta saki a Musulunci alama ce ta sassauci da aiki da tsarin shari'ar Musulunci, kiyaye haɗin kai na iyali yana ɗaukar fifiko don kare yara. Saboda wannan dalili, saki a koda yaushe zabin karshe ne, bayan gajiyar dukkan hanyoyin sulhu. Misali, Allah yana magana da maza yana tambayar su da su yi ƙoƙari don kiyaye auren, koda sun ƙi matansu: Ku zauna da su bisa tushen kyautatawa da adalci. To, idan kun ƙi su, akwai tsammãnin ku, ku ƙi wani abu, kuma Allah ya sanya albarka a cikinta. Surah 4 Aya 19 Haka nan ayar nan tana magana ne ga mata suna tambayarsu irin wannan: Idan mace ta ji tsoron zalunta ko tawaya daga bangaren mijinta, Bãbu laifi a kansu idan suka yi sulhu a tsakãninsu, Surah 4 Aya 128, wannan ayar tana magana ne ga dangi ko kuma al'umma don wannan manufa ta kubutar da wannan alaka, wanda Allah bai sauwake wa karya ba: Idan kun ji tsõron sãɓa a tsakãninsu, (biyu) masu sasantawa, daya daga danginsa, da sauran daga nata; idan suna fatan zaman lafiya, Allah zai daidaita su: Kuma Allah Masani ne, kuma Masani ne ga dukkan komai. Surah 4 Aya 35, Amma, idan bayan gajiyar dukkan hanyoyin sulhu, Ƙiyayyar da ke tsakanin miji da mata har yanzu ta fi haƙuri, sannan saki ya zama babu makawa. Ga kuma hazakar shari’ar Musulunci, wanda ke da amfani, maimakon hanyoyin da ba su dace ba, zuwa ga haƙiƙanin yanayi. Maƙasudin aure, da kuma duk wani ɓangare na rayuwar dan Adam, su ne don cimma farin ciki da nagarta. Don haka, lokacin da aka hana mutane hakkinsu na kashe auren da ba a yi daɗi ba, waɗannan biyun an keta su sosai. Wannan shine, kamar yadda ma'aurata za su rayu cikin wahala, wanda zai iya kai su ga rashin imani a aure. Don haka saki a cikin wannan yanayin - idan an auna har zuwa bala'in rarrabuwar iyali – zai zama ƙasa da bala'i. Maza suna da hakkin saki. Idan mutum baya son kiyaye aurensa saboda wani dalili, sai ya saki matarsa ​​kuma ya biya mata kudi ta hanyar biyan ta abin da ake ce wa mut’a. Wannan kari ne akan abin da ake yi mata na kudi akai-akai, idan har tana da hakkin 'ya'yansu. Saki ya fara aiki da zarar miji ya furta ko ya rubuta duk wata ka'idojin saki na shari'a kamar: ‘Na sake ki’ ko ‘kin sakeki’...da sauransu. Miji na iya yin wadannan ko dai da kansa ko kuma ta hanyar manzo (Ɗan aike).Idan har sha'awar mace ce ta yanke auren, lamarin ya zama daban. Dalilinta na iya zama cewa ta sami rashin lafiya, miji baya iya ciyar da ita kudi ko kuma ba ya da karfin jima'i. Za ta iya tabbatar da wadannan aibu a gaban alkali, sai alkali ya ba ta saki tare da samun cikakkiyar damar samun dukkan hakkokinta na kudi. Hakanan, idan mijin ya kyautata mata amma ba ta son ci gaba saboda wani dalili na zuci, sai ta tambaya me ake ce masa khul’. Wannan yana nufin a ba da saki amma ba tare da samun dama ga haƙƙin kuɗi ba, da kuma biyawa mijin sadakin da ya riga ya biya akan aurenta. Hajiya, duk na kori maki wannan jawaban ne saboda kisan cewa shi fa kalmar saki ba abun da za ayi wasa dashi bane, A wasu lokuta, furta kalmar saki ya zama mara amfani. Daga cikin wadannan har da lokacin da miji yake:1.) Buguwa. 2.) Wani ya tilasta musu furta su. 3.) Cikin tsananin bacin rai har bai san abinda yake fada ba. 4.) A cikin yanayi mara kyau na hankali, kamar hauka na wucin gadi, farfadiya ko a cikin suma. A irin wadannan lokuta, saki banza ne. Kin ga kuma Khalil na ƙaunar matarsa, kece kawai kike son tilasta masa ya sake ta. Hajiya bari nayi maki wani tambaya dan Allah, shin a zaman da kika yi da matar Khalil na kimanin shekaru biyu da ɗoriya, shin kin taɓa ganin wani mummunar hali da take dashi? Shin ta taɓa zaginki? Ta taɓa dukanki? Ta taɓa hana ɗanki zuwa gareki ko kuma yi maki wani alkhairin? Bin bata girmamaki da yi maki biyayya?" Shuru Hajiya tayi, can kuma ta girgiza kai tare da faɗin, "Ko ɗaya, Saratu bata taɓa yi min ɗaya daga cikin abubuwan daka lissafo ba." "To kin gani Hajiya! Hakan na nufin baiwar Allahn nan bata yi maki komai ba, kawai laifin ƴar uwarta ne yake son shafarta. Hajiya dan girman ubangijin halitta, ki sassautawa zuciyarki ki bar maganar Khalil ya saki matarsa, wallahi Allah zai yi fushi dake idan har kika tilasta masa rabuwa da matarsa, don wallahi zaki iya haddasa ɓanna a bayan ƙasa, zata iya yuwuwa, ki tsinke igiyar dake tsakaninsu, amma kuma suje suna bibiyar juna a waje bayan babu aure tsakanin su, kuma kin ga idan har haka ta faru, wallahi kina da babban kamasho! Hajiya ina roƙon wannan Alfarmar, ki sassautawa Ibrahim kar ki raba shi da matarsa dan Allah!" Ya Abdallah ya ƙarisa maganar a tausashe. "Uhm! Naji bayanka Marmari, kuma na gamsu, sai dai nima ina da nawa sharuɗɗan." Gyara zama Ya Abdullahi yayi, Khalil wani sanyin rahama ne ya shiga ziyartar lungu da saƙon jikinsa jin Hajiya ta janye ƙudurin saki, he is willing to accept all her sharuɗɗa in har zata amince ya cigaba da zama da his light. "Na farko dai dole ne ya auri Habbooba, na biyu, kar ya kuskura ya wulaƙanta min ƴa saboda matarsa kuma kar ya bawa matarsa fuskan da zata wulaƙantamin ƴa saboda tana taƙamar ita ce matar so, na uku, yayi takakkiya har Maiduguri yaje ya nemo soyayyar Habbooba, don ita ba _matar shige_ bace, idan har ya cika duk wannan, na amince ya cigaba da zama da matarsa, zan yi azumi uku na rantsuwar da nayi." Faɗin Hajiya, "To kai kaji Khalil, shin ka amince na abunda Hajiya tace." Gabansa na bugun tara-tara ya ɗago ya kalli ya Abdallah, sannan ya kalli Hajiya tare da sunkuyar da kai ya furta, "Na amince da duk abunda kika ce Hajiya. Zan je Nassarawa na dawo da Sarah, bayan na dawo sai in tafi Maidugurin!"
Chapter 108 · 0% Book details