Sashe 28
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu kad'an ke saurin d'aga mata hankali. Babu mamaki yanzu idan aka duba BP d'inta aga ya hau. Ta jima duk'e a bayin kamun ta iya cire kayan jikinta tayi wanka sannan ta sake d'auro alwala ta fito ta sauya kaya. Tuni wani zazzafan zazzab'i ya rufeta sai kakkarwa take yi a bakin gado. Dai-dai nan Laure ta shigo bakinta d'auke da sallama tana fad'in, "Hajiya a kawo maki zogalen yanzu?" Da sauri ta k'arisa shigowa d'akin tana fad'in, "Hajiya lafiya? Mai ke damun ki? Yanzu fa na barki lafiya kina amsa waya." Dakyar Hajiya tace, "Tafi ki kira min Maryamu yanzu a b'angarensu." da sauri Lauren ta juya ta bar d'akin har da had'awa da gudu ta nufi side d'in aunty Maryam tare da danna doorbell. Mijinta Yaya Abdul-Hakeem ne yazo ya bud'e k'ofar tare da fad'in, "Lafiya Laure na ganki a rud'e?" Ya fad'i don shima dawowarsa kenan daga wajen aiki. Yanzu nan kuma yake son shiga wajen Hajiyar. "Yaya Abdul Hajiya ce ba lafiya shine tace in kira mata aunty Mar....." Ko kamun ta k'arisa maganar har ya tureta ya fito da sauri ya nufi side d'in Hajiyar kamar zai tashi sama. Aunty Maryam ma da sauri ta fito don fitowarta kenan daga kitchen taji abunda Laure ke fad'awa mijin nata. Bin bayansa suka yi ita da Lauren hankali tashe. Ko da yaya Abdul ya isa d'akin Hajiya, gaba d'aya ta gama firgicewa. Jikinta yayi mugun zafi musamman ta wajen kanta. Zama yaya Abdul yayi tare da tallabo Hajiyar yana fad'in, "Inna lillahi! Hajiya mai ya same ki. Ai bamu ga ta zama ba. Mu tafi asibiti kawai." Dai-dai nan aunty Maryam d'in ta shigo ita da Laure. "Abdul-Hakeem d'au wayarka yanzu ka kira min _Khalilullah_." Hajiya ta fad'i hakan da kyar. Yaya Abdul bai kawo komai a ransa ba sanin k'anin nasa ai doctor ne. Maybe don yazo ya duba tane don Hajiya ta tsani zuwa asibiti. Wayarsa ya fiddo tare da kirar _Khalil_ d'in. Ringing yayi har ya katse ba'a d'aga ba, zai sake kira kenan sai ga shigowar kiran _Khalil_ d'in. D'agawa Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "Kana ina?" Daga can _Khalil_ yace, "I'm sorry yaya, na fito da wayar kenan zan d'auka sai katse. Gani kusa da gida." "To kayi maza ka shigo yanzu. Hajiya ba lafiya." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. _Khalil_ kuwa ji yayi gaba d'aya hankalinsa ya tashi. K'ara gudun motar yayi duk da yana gab da layin. Mintuna biyar suka k'ariso dashi gidan. Ko parking mai kyau bai yi ba ya shigo gidan ya nufi d'akin Hajiya kai tsaye. Nan ya tarar dasu sun yi curko-curko. "Hajiya mai ya same ki, taso mu tafi asibitina dan Allah." Da kyar Hajiya ta d'ago kanta ta zubawa _Khalilullah_ idanu tare da fad'in, "Abdul-Hakeem ku d'an bamu waje." Tana fad'in haka gaban _Khalil_ ya yanke ya fad'i. Don har ji yayi wani k'aramin zufa ya gangaro daga goshinsa. Abdul-Hakeem babu musu ya mik'e ya fita, aunty Maryam da Laure suka bi bayansa tare da rufo masu k'ofa. _Khalil_ shuru yayi kamar ruwa ya cinyesa, don hakanan jikinsa Hajiya ta gano abunda yake b'oyewa. " _Ibrahim_" Hajiya ta kira sunansa da muryanta da yayi rauni. Hankalin _Khalil_ ta tashe yace "Na'am Hajiya." "Wacece Saratu?" A mugun furgice duk da kuwa zuciyarsa na bashi ta gano ko kuma wani ya fad'a mata ya d'ago bakinsa na rawa yace, "Haj..... Hajiya ban gane abunda kike fad'i ba." Hannu Hajiya ta d'aga ta wanke masa fuska dashi tare da fashewa da kuka tace, " _Khalilullah_ ka b'ata wayanka. Baka kyautawa kanka ba. Dadiro _Ibrahim_? Yanzu har kayi rik'an da zaka ajiye dadiro a waje _Khalil_. Kana da kud'i, kana da wajen zama, duk wani abu da namiji zai mallaka kamun yayi aure, ka mallaka _Mu'azzam_, amma shine sabida shaid'an ya buga maka gangi, giyar kud'i na janka, shine zaka butulcewa Allah ta hanyar yin abunda ya haramceka dashi. Ka bani mamaki _Khalil_. Ashe irin tarbiyan da muka gina ku a kai ni da mahaifinku, watsar dashi kayi? _Khalil_ baka yi wa kanka da mu adalci ba. Ka b'atawa zuri'ar suna. Ashe dai da gaskiya su Ameeru da suke cewa ka ajiye dadiro. Shiyasa a kullum burinsu shine suyi maka aure sabida sun san lalatar da kake yi a waje. Baka min adalci ba _Mu'azzam_!" Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka takaici. Shima _Khalil_ d'in kukan ya soma yana fad'in, "Hajiya dan girman Allah kar kiyi mani kuka. Kukanki bala'i ne a gare ni. Ki tsaya inyi maki bayani. Duk wanda ya fad'a maki na ajiye dadiro wallahi sharri yake min kawai yana son shiga tsakanina dake ne. Wallahi tallahi ban tab'a ajiye dadiro ba a rayuwata. Kuma Hajiya ban tab'a ratsa jikin wata y'a mace ba. Ban san ta yanda zan yi maki bayani ba ki fahimceni ni." Hajiya tsagaita kukanta tayi tare da fad'in, "Kenan sharri ake maka baka san wata Saratu ba." Girgiza kai yayi tare da fad'in, "Na santa Hajiya, amma ba ta yanda kike tsammani ba. Ita ce wacce nake fad'a maki ba tsayar matsayin wacce zata zama uwar y'ay'ana." Wani ajiyar zuciya Hajiya ta saki, sai kuma tace, "To maganar ciki fa? An ce kayi mata ciki in tsammaci zuwan jika nan da wata takwas. Ya matsayin wannan maganar take?" Shuru _Khalil_ yayi yana kallon k'asa. Sai kuma ya d'ago tare da kama hannayen Hajiya duka biyun yace, "Hajiya dan girman Allah kiyi hak'uri da abunda zan fad'a maki yanzu. Amma ki saurare daga baya sai ki yanke hukuncin da kika ga ya dace. Dagaske Sarah tana d'auke da ciki, kuma nawa ne." Tass Hajiya ta sauke masa mari tare da nuna masa k'ofa tace, "Fita! Fita nace ka bar min d'aki yanzun nan!!" Ta kuma fad'i a tsawace. Da sauri ya mik'e tsaye tare da fad'in, "Haj......" "Fita _Khalil_ kar ka sa nayi abunda zan dawo ina dana sani. Fita nace kar in fad'i mummunar kalma a gare ka." Fad'in Hajiya tana matsar hawaye. Da sauri _Khalil_ ya fita tare da rufo mata k'ofar. Shi babban tashin hankalinsa, kar jininta ya hau. Yana fitowa daga d'akin ya nufi waje ya zauna tare da kama kansa har akai kiran sallar Isha sannan ya mik'e ya nufi masallaci. Hajiya kuwa kuka tayi sosai har da majina. Bayan ta idar da sallar isha'i wanda tayi sa da kyar, sannan ta lalubi wayarta ta dannawa babban wansu soja mai muk'amin *_LTG (Lieutenant general)_* dake zaune a abuja, a can yake da iyalansa gaba d'aya kasancewar aikinsa a can yake. Bugu d'aya yayi rejecting tare da karanta, "Assalamu alaikum Hajiya." "Amin wa'alaikassalam." Tun daga yanayin yanda ta amsa kiran ya tabbatar babu lafiya, mik'ewa yayi d'aga kwancen da yake ya zauna tare da fad'in, "Hajiya lafiya? Mai ke faruwa?" Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da fad'in, "Marmari daga nesa (Bata kiran sunansa kasancewarsa d'an Faari) duk abunda kake yi ka d'auki sakuis (excuse) kazo gida gobe, kuma ka kira wancen yaron na Kano shima ina son ganinsa har da k'anwarku Aisha. Duk kuzo ina neman ku gobe." Gaba d'aya tunanin _LTG Abdallah_ akan maganar gadonsu ne, don wani lokacin haka uncles suke sako mahaifiyar nasu a gaba duk akan dukiyar da mahaifin nasu ya bari. "Dan Allah Hajiya ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah gobe zan biyo jirgi ni da Aysha. Zan kira mijinta yanzu ina gama waya dake." Fad'in LTG Abdullah don Aysha d'in a nan Abuja tayi aure, kusan a hannunsa take, don shi ya aurar da ita. Ita ma soja take aure ana Abujan. Katse wayar Hajiya tayi tare kifa kanta a kan pillow tana zuciyarta na mata zafi, gaba d'aya Y'ay'anta daga maza har matan lafiya k'alau ta aurar dasu, Nafeesa ta je gidan mijinta lafiya, haka Aysha. Mazan ma gaba d'aya babu wanda ya d'auko mata abun kunya sai _Khalilullah_. Kuma duk cikin y'ay'anta shi, yana da wani special guri a zuciyarta. Don shi d'in favourite d'inta ne. Duk da kuwa ba shine auta ba. Nafeesa ce autarta. B'angaren _Khalil_ kuwa yanda yaga rana, haka yaga dare. Abun duniya duk yabi ya ishesa. Sam ba ta haka yaso hajiya taji wannan maganar ba. Yaso ya shaida mata da kansa ta hanyar da ko zata jijjiga ba kamar haka ba. Tunani ya dunga yi wanene ya san abunda ke faruwa har ya d'aga waya ya kira Hajiya, "Doctor Kamal!" Fad'in _Khalil_ a bayyane. Da sauri ya mik'e zaune yana jin wani irin matsanaicin b'acin rai da tsanar doctor d'in. "Wallahi sai na baka mamaki Kamal. Ni zaka had'a da mahaifiyata. Zaka san koni wanene. Daga kai na baza ka k'ara irin wannan munafurcin ba." Saukowa yayi ya nufi bayi yayi alwala tare da fitowa ya shimfid'a darduma ya dunga yin sallah yana rok'an Allah sauk'i da sassauci akan lamarin. Bai tashi daga kan darduma ba sai da yaji kiran sallar asubahi na shiga masallaci sannan ya mik'e ya fito. Sai da ya fara bi ta d'akin Hajiya tukun, da sand'a ya murd'a k'ofar a hankali tare da bud'ewa. Karaf suka had'a idanu da Hajiyar dake zaune a kan darduma, don kamar yanda ya kwana sallah haka ita ma. Da sauri ya jawo k'ofar ya rufe tare da barin wajen ya nufi masallaci. Sai bayan da aka idar da sallah har fito zai koma cikin gida yayansa Abdul-Hakeem ya tare sa, bayan sun gaisa yake ce masa, " _Khalil_ mai ke faruwa Hajiya tayi kiran kowa na gidan nan cikin gaggawa? Yaya Abdullah ma yana hanya zuwa anjima zai biyo jirgi shi da Aysha. Kuma nima Hajiya ta saka na kira mijin Nafeesa akan ha kawo ta gobe. Wani irin meeting kuma za ayi yau a gidan nan? Allah yasa ba dai akan rigimar gado bane. Nifa wallahi abunda Papa ya tafi ya bari bai tab'a d'ad'ani da k'asa ba, abun na tara da gumina ma ya ishe ni zaman duniya." Tun da ya fara maganar _Khalil_ jinsa kawai yake yi amma kwakwalwarsa da tunaninsa sun yi nisa tun lokacin da yace masa yaya Abdullah na hanya. Wannan masifaffan mai bak'ar zuciya kamar da taurin kai. Don shine ya d'auko Papa sak. Shi kaifi d'aya ne, idan yace yes, to ko duniya zata tashi yes d'in