Sashe 31
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin murmushi mugunta ta saki bayan ta kalli goron fantar. Bud'ewa tayi tare da jefa duka kwayoyin sannan rufe da k'arfi ta girgiza tare da saka shi cikin aljihun doguwar rigar dake jikinta ta nufi hanyar gida cike da jin dad'i. Ko da ta shiga d'akin, bata samu Sarah a ciki ba lokacin Baba yayi kiranta tana d'akinsa domin tattauna da ita game da batun aurenta da iyayen _Khalil_ suka yi. Sai ta ajiye fantar a dai-dai inda ta san Sarah na shigowa zata gani sannan ta bar d'akin ta koma d'akin Lami inda ta same su duka a d'akin suna tattauna game da zancen aure da iyayen _Khalil_ suka yi. "Kuma ke Lami sai ki yarda? Tabd'ijam! Bayan kin hana d'aya daga cikin yin soyayya mai zurfi balle har hakan ya saka mu bujire maki wata ran muce aure muke so. Ai kamar yanda muke zaune a gida har wannan lokacin, haka ita ma zata zauna babu wani zancen aure." Fad'in Aina'u wacce ta tsinci maganar daga sama kawai ta tsumbula baki. "Kuji min shegiyar yarinya! Ke da Naima wanene babba da har zaki bud'e baki kiyi wannan maganar. Ke da ko b'ari baki tab'a yi ba cikin gidan nan har kyayi wannan maganar. Wai ma Lami tana da samari ne masu fita da ita?" Fad'in Nuratu. "Ina fa!" Lami ta bada amsa a gajarce. "Har wani fad'i take kamar yanzu har yanzu bamu yi aure. Dudu-dudu fa bata wuce sha bakwai sha takwas ba amma har take wannan maganar. To Na'ima tace me ita da take da shekaru talatin da d'aya a duniya?" Dogon tsaki Na'ima taja tare da fad'in, "Bar y'ar iska. Lami dube ni nan in baki shawara idan zaki amsa. Kin ga, kar ki sake kice zaki ja game da batun auren Sarah da _Khalil_. Kin ga dai uban sojojin da suka zo gidan na d'azu, kuma da bakinki kike bamu labari Y'ay'anta gaba d'aya hukumomine, daga soja, sai d'an sandar farin kaya da kuma lauya. Kuma kin san akwai dukiya babu k'arya a wajen su. Wallahi Lami sai kin fi jin dad'i idan Sarah ta shiga gidan matsayin mata ba dadiro ba. Kuma kince mana dagaske fyad'e yayiwa Sarah ba kanta ta kai ba. Yanzu idan kika k'i amincewa, da zarar ta haihu karb'e y'ar ko d'an kawai za suyi, shikenan ku da k'ara ganinsu sai Allah. Amma idan auranta yayi, arziki har mu sai mun ture don Sarah ba marowaciya bace kowa ya sani. Maganar gaskiya idan ta fito a fad'eta ko yaya take." Shuru Lami tayi tana auna maganganun Na'ima. Aina'u kuwa wani dogon tsaki taja tare da fad'in, "Wallahi idan har tsautsayi yasa aka yi wannan auren, sai na zame wa Sarah bala'i daga ita har su dangin mijin nata." A zuciya tayi maganar. "Ke Na'ima, Saratu fa tana da mugun hali. Ina tsoron kar ta shiga gidan arziki ta manta cewar nice wacce tayi sanadiyar zuwanta duniya. Da ace zata iya shawo kanta kawai yayi ta d'ura mata ciki a waje yana kashe mata kud'i ni kuma ina kula da yaran ina kame y'an currencyn zai fi min. Amma zuwan gidan matsayin matarsa sai inga kamar akwai matsala. Don a irin kallon rainin da yaron yake min, sai inga kamar zai iya hana ni zuwa gidan ko kuma ita ya hana ta zuwa nan d'in. Kuma tsaf ubanku zai goya masa baya." Marfu'a tayi karaf tace, "Kuma wallahi Lami zai iya hakan. Don ko mu baki ga irin kallon da yake mana ba matsayin yayyin budurwarsa." Gyara zama Lami tayi tare da fad'in, "To ya kuke ganin za ayi kenan?" Karaf Aina'u tace, "Lami, zubar da cikin kawai za ayi!" Da sauri gaba d'aya suka kalleta tare da fad'in, "Baki da hankali ne Aina'u? Ai idan aka zubar da cikin kamar rabasu aka yi. Halan baki san abunda baban wansu yace ba ko?" Fad'in Hassana. Yamutsa fuska Aina'u tayi irin ban san komai d'in nan ba tare da fad'in, "Mai yace shi babban wan nasu?" "To cewa yayi idan har aka zubar da cikin to babu aure tsakaninsu." Fad'in Lami. Tsaki Aina'u tayi tare da fad'in, "To dama ba auren ake so a samu hanyar fasuwarsa ba?" "Ke dak'ik'iya ce wai? Idan har haka ta faru ai fita za suyi daga harkan mu gaba d'aya kuma su hana shi _Khalil_ d'in zuwa gidan nan. Kin ga kenan anyi two-zero babu ciki, babu auren." Murmushi Aina'u tayi tare da fad'in, "To ku saurare ni da kyau. Shin ke Lami baki lura da irin son da shi _Khalil_ d'in yake wa Sarah ba? Idan da ace ba sonta yake yi ba, babu abunda zai saka ya nemi gidansu har yazo ya samu mahaifinta suyi magana, kuma sannan ba zai tab'a d'auko iyayensa ya kawo su gidan nan ba. Sannan da baya sonta ba zai tab'a yarda shine uban cikin jikinta ba. Kar ki manta shi likitane. Da zai iya duk dabaru ya cire cikin ya kuma koreta. Idan ta nemi tona mata asiri yayi amfani da dukiyarsa ya kulle ba ita kad'ai ba har damu y'an uwanta ko kuma ya kai mu kotu yace zamu b'ata masa suna da sharri. Duk k'auna ce mai zafi ya kawo haka. Kuma wallahi kinji na rantse maki Lami, da ace _Khalil_ bai son Sarah, babu abunda zai kawo shi, shi da iyayensa gidan nan a yau. Kuma a gaban idanunsu ya dunga kwarara godiya bayan Baba da y'an uwansa sun amince ya auri Saratu." Hannu Marfu'a ta bata suka tada tare da fad'in, "Shegiya k'anwata! Ina maki kallon k'aramar yarinya ashe kwakwalwarki na ja. Na yarda da maganar Aina'u yasin Lami. Ko ya kuke gani y'an uwana?" Ta k'arisa maganar tana kallon su Nuratu. Na'ima tace, "Ni dai maganar zubar da cikin nan har yanzu bai gama kwanta min ba. Duk da kuwa zuciyata tana rawa akan wata rana Sarah zata iya juya mana baya sabida mijinta. Babu wata shawara ce sai wannan Lami?" "Gaskiya ni dai babu a waje na." Fuska kumbure Aina'u tace, "Shikenan Lami tunda ni kun d'auke k'aramar yarinya wacce shawararta bai da wani amfani. Idan komai ya kwab'e maku nan gaba, zaku tuna wannan ranar wallahi." Tana gama fad'in haka ta tashi ta fice tana mai dana sanin yin maganar zubar da cikin kasancewar basu amince da shawararta ba. Sarah zaune gaban Baba tana hawaye, "Saratu, ba zan tilasta maki ki auri _Ibrahim_ ba, sai dai a matsayina na mahaifinki, ina mai baki shawara da ki bawa zuciyarki hak'uri ki amince da wannan yaro don Shi kad'ai ne rufin asirinki. Na yaba da hankalisa da kuma karamci irin na iyayensa. Kuma ina da kyakkyawar zato akan zasu rik'e ki bisa amana tamkar y'ar cikinsu ba suruka ba." Jan majina Sarah tayi tare da fad'in, "Baba ba kukan nake yi ba sabida ban son zab'in da kayi min, kukan farin ciki nake yi sabida zab'a min kai da Allah yayi matsayin mahaifi. Wallahi ko mahaukaci ka zab'a min matsayin mijin da zan zauna dashi, zan amshe shi hannu bibbiyu in kuma yi biyayya a gare shi. Nagode sosai Baba, Allah ya k'ara maka lafiya. Sannan nayi maka alk'awarin yiwa _Khalilullah_ biyayya har k'arshen numfashina idan har Allah ya rubuta ni matarsa ce. Bazan tab'a baka kunya ba Baba." Tausayi da k'aunar Sarah ya lullub'e Baba, "Allah ya maki albarka Saratu, Allah ya saka maki da alkhairi ya kuma zab'a maki abunda yafi zama alkhairi a rayuwarki ya shirya sauran y'an uwanki. Ubangiji ya jib'anci lamuranki. Je ki kwanta ki huta. Allah ya tashe mu lafiya." Da "Ameen" Sarah ta amsa bayan ta matso masa da duk wani abunda za zai buk'ata cikin dare sannan ta fice. Sai da tayi alwala a fanfo tukun ta nufi d'aki domin yin sallar shafa'i da wuturi. Tana shiga babu abunda idanunta suka fara gani sai wannan robar fanta mai sanyi da Aina'u ta ajiye sai naso yake yi. Hakanan Sarah taji bai wani burgeta ba. Sallaya ta shimfid'a tare da tada sallah. Tun bayan shigowarta d'akin Aina'u ta shigo ya kai sau biyar amma tana ganin robar fantar a inda ta ajiye. Ji take kamar ta shak'o wuyar Sarah da bacci ya kwashe bisa darduma ta d'ura mata wannan fantar. Da k'afa ta dunga shurin Sarah har sai da ta farka, "Ga Fanta nan mai sanyi idan zaki sha. Na sayo ne d'azu domin in sha, sai kuma ya fitar min a rai. Ki shanye ba sai kin biya. Tun d'azu dama ke na ajiyewa ganin duk gidan nan kece mai son Fanta." Bacci a idanun Sarah ta mik'e zaune tare da fad'in, "Bar mi shi a wajen. Sai zuwa anjima nasha yanzu cikina a cike nake jinsa." Ba tare da Aina'u tace komai ba ta fice haushi kamar ya kashe ta na rashin shan fantar da Sarah bata yi ba yanzu. Tana fita daga d'akin wayar Sarah ta soma ringing. Kai hannu Sarah tayi tare da d'auko wayar dake kan one sitter dake d'akin. Kallo d'aya yayiwa numbern ta gane _Khalil_ ne duk da kuwa bata yi saving number d'in ba sabida 3 d'in guda shidda da ya k'are da numbers d'in. Sai da ta turo baki sannan tayi picking tare da mik'ewa ta hau kan gadon sannan tace, "Assalamu alaikum!" Ajiyar zuciya _Khalil_ ya sauke tare da fad'in, "Amin wa'alaikissalam amaryata. Har kin fara bacci ne baki jira naji yanda kuke ba?" Bata ce masa komai ba sai ma mirginawa da tayi zuwa k'arshen gadon. "Baza kiyi magana ba?" Ya fad'i yana mai gyara kwanciyarsa. "To ni mai zan ce? Bacci fa nake ji sosai." Ta fad'i tana mai lumshe idanu." "To kiyi baccin ki mana. Na hana ki ne?" _Khalil_ ya fad'i yana murmushi. "To ta yaya zan yi bacci bayan ka hana ni? Ka kashe wayar to sai in kwanta." "Wato kin manta da deal d'in mu kenan ko?" Ya fad'i har da yiwa wayar hannunsa gwalo kamar tana ganinsa. Itama hararar wayar tayi tare da fad'in, "Tab! Ai yanzu babu wani zancen deal kuma." Waro idanu yayi tare da fad'in, "Inji wa ya fad'a maki haka? To ni dai har yanzu deal d'in mu na nan." Bata san lokacin da tace, "Duk da manya sun shigo cikin zancen?" Dariya