← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 112

Sashe 104

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hajiya dan........." Ko kamu ya ƙarisa abun da yake shirin faɗa har Hajiya ta yanke wayarta. Hannu ya kai ya daki steari da ƙarfi tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Haba Hajiya!! Habaaa!!!" Ya jima kamun ya kunna motar ya sau hanya, "Wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa!" Ya faɗi bayyane, can kuma ya kuma ɗaukar wayar ya sake dailing number ɗin Sarah, " _The number you're trying to call is currently switched off, please try again later. Thank you_." Tsaki yayi tare da ajiye wayar a gefe ya nufi gida don bai san dame Ya Abdullah yazo ba. Tafiyar da zai yi ta mintuna sha biyar, amma saboda tsoro da tashin hankali cikin mintuna talatin da biyar ya iso layinsu. Tun da ya hango uban sojoji uwa saƙago sun tsatstsaya ya kuma tabbatarwa kansa ya LTG ya iso gidan. Horn yayi, mai gadi ya wangale gate shi kuma ya shiga tare da parking sannan ya fito yana tafiya sumimi-sumumi kamar an tsoma jaba a cikin koko. Tun da ya doshi ɗakin Hajiya yake jin koke-koken mata na fitowa daga ɗakin. Shahada yayi tare da ɗaga labule ya shiga. Turus ya tsaya yana kallon matan dake ɗakin tare da mamakin yaushe suka iso all the way from Maiduguri. Duƙawa yayi har ƙasa tare da soma gaishe su, yayin da kansa a ƙasa ya shiga gaida ya Abdullahi da tun shigowarsa kallo ɗaya kawai yayi masa ya kau da kai. "Wallahi, tallahi Hajiya baza mu taɓa yarda ba, sai an ɗauki mataki akan wannan abu da ƙanwar matar ya Khalil tayi masa, ta cuce mu ta raba mu da ƴar uwarmu, kema kuma tayi ƙoƙarin raba mu dake, baza mu yafe mata ba akan wannan abu da tayi mana. Hajiya ko gawan Nafeesa ban gani ba!" Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka mai ciwo. "Har da jaririyar da bata ji ba bata gani ba, yarinyar da bata jima da shaƙar iskar duniyar ba, wannan wani irin rashin imani ne haka!!" Aysha ta sake faɗi tana mai kwanciya akan cinyar Aunty Yagana, ƙanwar Hajiya. Shafa kanta Aunty Yaganar tayi tare da faɗin, "Aysha duk wacce imaninta zai bar jikinta har ta iya kwanciyar aure da mahaifinta, to wallahi babu abunda baza ta iya aikatawa ba, da a zamanin annabawa tazo, to tana ɗaya daga cikin wacce zata iya yunƙurin kashe Annabi! Wallahi Hajiya ina bayanki ɗari bisa ɗari, kar ki sake ki yarda matar Khalil ta dawo cikin gidan nan, mai za ayi da zuri'a irin tasu, zuri'ar matsafa, zuri'a karuwai ƴan dangi Arna!! Ai wallahi don dai kisa haramun ne, da ko ƴaƴan da Khalil suka haifa tare, shaƙe wuyansu kawai za ayi su mutu kowa ya huta. To sun tsotsi nonon tsiya!" Faɗin Aunty Yagana a mugun zuciye, don har ta kusan fin Hajiya ɗaukar zafi. Khalil lokacin guda yaji haushin Aunty Yagana ya rufesa jin abunda tace akan ƴaƴasa, nan da nan ya ɗaure fuska tamau. "Kayi abunda na umarce ka dashi ko kuwa???" Faɗin Hajiya tana watsawa Khalil harara. Ko kamun yayi wani yunƙurin yin magana tuni Aunty Falmata mai bin Aunty Yagana tace, "Ba magana ake yi maka ba don ubanka? Ko sai na taso ba na shaƙi wuyarka!" Ta ƙarisa da ƙarfi har sai da Khalil ya razana, "Hajiya wallahi, tallahi daga gidan nake, su kansu iyayenta basu san bata gidana ba, ashe dana koreta ba gida tayi ba, can dangin babanta ta nufa." Ya ƙarisa maganar a tausaye. "Dubi yanda yake wani rausayar da kai kamar maraya, to ubanka zaka ci, kuma dole ka rabu da yarinyar nan tun da ba tare aka haife ku ba. Yaro duk kabi ka zama wawa a kan mace!" Faɗin Aunty Yagana. "Uhm! Baku ji wata maganar banza da yake yi ba, wai ta tafi dangin mahaifinta. Ina ce nan Marmari yayi bincike lokacin auren naku, kowa cewa yake bai san asalin mahaifinta ba, su dai kawai tarewarsu suka gani a unguwar, kuma babu wanda ya taɓa ganin wani ko wata daga cikin ƴan uwansu yazo gidan, kaii Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'una, wannan fitina haka!" Hajiya ta faɗi har da buga cinya. Tun da suka fara magana ko tari ya Abdullahi bai yi ba yanzu da yayi gyaran murya tare da faɗin, "Hajiya, tun farko irin haka na guda shiyasa naƙi auren don zuciyata bai kwanta da ahalin ba, amma Hajiya kece ki kai ta tausata akan inyi haƙuri ayi auren tunda dai mutane huɗu sun bata shaida a kan ita matar Khalil ɗin, sannan kika ƙara da faɗin, laifin wani bai shafan wani. To Hajiya yanzu hakan ma haƙuri za kiyi tunda dai an riga an haɗa zuri'ar nan kuma laifi bana matar Khalil bane, na ƙanwar matarsa ce, kuma laifin ƙanwar matarsa babu yanda za ayi ya shafi matarsa, tunda ke shaida ce hatta ita kanta matar tasa ba barinta tayi ba. A bar abunda ya wuce ya wuce, sai a tari gaba kawai." Tsabar zuciyar Hajiya na tuƙuƙi, ta buɗe baki za tayi magana ta shaƙe da miyau, take ta hau wani irin mugun tari, idanunta na zubar da hawaye. Da sauri Laure ta nufi kitchen ta ɗauko bottle wata ta buɗe tare da kawowa Hajiyar, da sauri Hajiya ta karɓa ta kafa kai, sai da tasha rabi sannan ta ajiye goran tana mai da numfashin. Babu abunda kake ji a ɗakin sai "Sannu Hajiya!" Sai da ta lafa sosai sannan ta shiga faɗin, "Marmari idan har ka san ba zuwa kayi ka taimaka min muyi wannan yaƙin tare ba, to ka tashi ka koma tun yamma bata yi maka ba, don ka san wallahi, ba zan taɓa yarda Saratu ta kuma zama da Khalil ba in har nice na haifesa, idan kuma zai yi mani musu da gardama, sai in sallawa duniya shi!" "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya!" Khalil ya faɗi da ƙarfi har da dafe ƙirji yana zaro idanu. "Haba Ya Bilki, ai wannan furucin bai kamata ya fito daga bakinki ba matsayinki na uwa, idan ki kai haka ai sun ci riba. Hakan ma ba zata faru ba, Khalil ai me biyayya ne, ko ba haka ba Ibrahim, mai sunan ɗan gatan Allah!" Faɗin Aunty Yagana har da dariya. Sunkuyar da kai yayi tare da gyaɗa kan alamar eh. Aunty Falmata kuwa cewa tayi, "Yauwa Khalil, ko kai fa! Yanzu abunda za ayi, dubawa za kayi cikin dangi na nan ko na can Maiduguri, a kwai ƴan mata tsala-tsala, na san dai ba zai wuce kyal-kyal banzar matar nan taka bace kake ganin baza ka samu sama da ita ba kasancewar jajur kuma kyakkyawa, to akwai waɗanda suka fita komai a cikin dangin ubaka dana uwarka. Dangin ubanka akwai irin su, Ajaja, Gona, Am'an, yaba, yakaruu duk kyawawane duk da kuwa baƙaƙe ne, idan kuma basu yi maka ba, sai ka tafi dangin uwarka, ka san dai Shuwa ba baya ba wajen kyau, gasu Hindatu, Rakiya, Raliya dasu Aysha da Ameena, kai nayi tuya na mance da albasa, ga wannan ƴa ƴar wajen Mariya, _Habbooba_! Kai ita ma na zaɓa maka, Yarinya kamar India, yanda kasan ita tayi kanta tsabar kyau, ga gashi don san yana ɗaya daga cikin abubuwan dake tsole maku idanu ku maza." Caraf Hajiya tace, "Wallahi ni Habbooban ma tafi kwanciya min a rai, kawai ayi magana da iyayenta, idan sun amince sai ayi magana. So nake ayi komai cikin gaggawa, kuma ni wallahi na haƙura da zamansa a nan Nigeria kuma dama ni na matsa a kan ya dawo nan ɗin, to yanzu na haƙura, ana ɗaura auren sai ya tattara matarsa su koma cen _Las Vegas_ ɗinsa da zama." Da gefen idanu Ya Abdullahi ya kalli Hajiya tare da ɗan yin murmushin gefen baki tare da miƙewa yace, "Muje can side ɗin naka naga yarinyar!" Yana gama faɗin haka ya fice, da sauri gaba ɗaya mutanen ɗakin suka miƙe suka fito don suma duk abunda ake yin basu ga Aina'u ba. Jiki a sanyaye Khalil ya miƙe yabi bayan ya Abdullah zuwa side ɗinsa, shi ya saka key ya buɗe sannan ya shiga, ya Abdullahi yabi bayansa, su Hajiya kuma suka bi bayan ya Abdallah. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Kuna jin warin da nake ji kuwa a cikin ɗakin nan kamar gawa ta ruɓe?" Faɗin Nafeesa tana mai toshi hancinta. Gaba ɗaya sauran ma toshe hancinsu suka yi, "Allah yasa ba wannan shaiɗaniyar bace ta mutu a cikin gidan mu!" Hajiya ta faɗi. Cikin sauri Khalil ya nufi sama yana tsallake step bibbiyu. Ƙafa ya saka ya daki ƙofar ta bulle da ƙarfi, da wani uban sauri ya koma baya yana toshe hanci tare da zaro idanu, "Wa'innahu Sulaimanu!" Faɗin Aunty Yagana da aunty Falmata. "Ibrahim menene wannan ka ajiye a ɗakin ka." Ɗagowa Aina'u tayi cikin wa.i irin mugun azaba tare da faɗin, "Ku taimaka min, ku taimakeni Aina'u ce!" Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da faɗin, "Wallahi tallahi jama'a mu kiyaye ALLAH! Mu kiyaye ALLAH jama'a!! Yanzu wannan yarinya Aina'u ce ta koma haka?" Kallonta Nafeesa take tayi cikin tsoro, ganin da tayi mata na ƙarshe shine ranar da tazo washa garin auren su Khalil. Yanzu kam ta lalace, tsirara take a cikin ɗakin, maƙogwaronta a waje, idanunta ya zazzago, ko ina a jikinta babu inda babu rami zuƙuƙu, duk inda tsokar ta yanko ta faɗo, tsutsotsi ke cunkusuwa a wajen suna cin sauran naman dake wajen. Gaba ɗaya Aina'u ta fice daga hayyacinta, gashin kanta duk ta gama fuzgar shi, haƙoranta duk jini ta gama tattaune leɓenta. Sai wani irin miƙewa take yi tana zabura sannan sai ta fasa ihu tare da kai hannu gabanta ta kwakwulo kunamu ta watsar a tsakar ɗakin sannan ta hau burgima tana buga kanta da bango. "Hajiya a fitar da yarinyar daga gidan nan, ta koma can gidan iyayenta dan Allah!" Fadin Nafeesa jikinta na wani irin rawar tashin hankalin ganin halin da Aina'u take ciki. Ya Abdallah kuwa girgiza kai yayi tare da saurin barin waje yana mai faɗin, "Hajiya yanzu yarinyar nan zata bar gidan nan, ku fito mu fita." Gaba ɗaya suka bi bayansa, Khalil kuwa sai da ya kalli Aina'u sannan yace, "Ban taɓa jin ɗigon tausayinki ba Aina'u, domin kuwa kin cutar
Chapter 104 · 0% Book details