Sashe 40
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
babba, key na controlling gidanka yana hannunka, Sarah kamar motarka ce, duk inda ka nufa da ita, nan zata bi. Saboda haka, dan girman Allah, kar inji Sarah tayi kuka da kai." Sosai _Khalil_ yaji Munee ta kwanta masa a rai. Murmushi yayi tare da fad'in, "An gama aunty Muneeba. Hud'ubarki ta shiga sosai." Juyawa tayi ta kalli Sarah tare da fad'in, "K'awata na dawo kanki, kin ga, wallahi kiyi masa biyayya domin aljannarki na k'ark'ashin k'afarsa. Idan ya take, sunanki sorry, don haka kema kar inji yayi kuka dake. Irin tarairayan duk ki rik'a masa. Kamar irinsu, Gwandi, zaka sha gwanda, honey zaka sha Honey, Sweety zaka sha swee....." Kamun ta k'arisa cewa sweet d'in daga _Khalil_ har Sarah suka fashe da dariya. Ita kanta Muneebar dariyar take yi. "Gaskiya k'awar mu naji dad'in wannan hud'uba naki. Mun gode Allah ya saka da alkhairi kuma mun d'auka." Murmushi a fuskanta tana mai taya k'awarta farin cikin samun miji kamar _Khalil_ tace, "To ma Sha Allah. Haka nake so ai." Gyara tsayuwa _Khalil_ yayi tare da fad'in, "To yanzu wani shirye-shirye kuka tsara ta wajenku?" Kallon Sarah Munee tayi sai kuma ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Gaskiya ta wajen mu, walima kawai za muyi da k'awayen mu na makaranta da kuma mutanan anguwa. Ko ya kika ce k'awata?" Ta k'arisa maganar tana kallon Sarah. Gyad'a mata kai Sarah tayi tare da fad'in, "Eh hakane." "To ustazai. Ni dai abokaina sun had'a min dinner. Don haka bayan an d'aura aure akwai dinner sai ku kasance cikin shiri. Allah yasa k'awar tamu tana da account?" Ya k'arisa maganar yana kallon Munee. "Eh ina da shi." Fad'in Munee. Fiddo wayarsa yayi tare da fad'in, "Fad'a min account number d'in." Bayan ta fad'a masa da sunan bank d'in, a take yayi mata transfer d'in 500k. Waro idanu Munee tayi lokacin da tayi arba da kud'in da ya turo don har sai da ta murza idanu. Tun da take kud'i dubu ashirin ma basu tab'a zama cikin account d'inta ba ko da mistake, sai ga dubu d'ari biyar sun shigo yau. "Wad'annan kud'in fa? Wallahi sun yi yawa. Duk na minene haka." "Duk na walimar ce." Ya fad'a kai tsaye. "Dan Allah sunyi yawa wallahi." With serious face yace, "Basu yi ba. Kuma kar ki sake magana. Kuje kuyi duk wani hidimar da za kuyi dasu. And in Sha Allah two days before the wedding za'a kawo maku raguna guda uku da drinks. Yanzu haka ma idan kun koma gida kuyi list d'in duk wani abubuwan da zaku buk'ata sai ku turo min." Gaba d'aya Muneeba is speechless. Sai gyad'a kai kawai take yi. B'ata tab'a yin y'an matan amare ba, amma ta sha gani da ji, wani lokacin ma da fad'a ake k'arewa da abokan angon domin wasu dakyar suke fitar goma zuwa sha biyar. "Bari na baku waje, sai kin shigo k'awata." Fad'in Muneeba. "To k'awarmu, mun gode sai ta shigo tunda ni baza amin sallamar ba." Dariya Muneeba tayi tare da fad'in, "Sai da safe asha soyayya lafiya." Tana gama fad'in haka ta shige gida tana dariya. Sun jima a waje suna hirar su ta soyayya, sai da zai wuce yake fad'a mata ta fad'a a gida gobe za'a kawo akwati. Tana shigowa gida ta nufi d'akin Baba kai tsaye ta fad'a masa sak'on _Khalil_ shi kuma ya cire dubu hamsin a cikin kud'in da _Khalil_ ke basa idan yazo gaishe sa yace taje gidan su Muneeba ta kaiwa mahaifiyarta ayi y'an soye-soyen fulawa da kuma kaji. Sannan ya ware wasu kud'i ya ajiye wanda idan y'an kawo kaya sunzo a basu tukwuici. Da Muneeba zata wuce gida tare suka tafi wajen mahaifiyarta tayi mata bayanin sak'on da Baba ya turo ta ta fad'i. Hannu biyu Mama ta karb'a har ta bada sautu saboda a sayo komai da wuri kasancewar gobe bak'in za suzo. Anan ne kuma Sarah da Muneeba suka fad'a mata yanda suka yi da _Khalil_ game da walimar da za suyi da kuma kud'in da ya turo. Ita kanta mama tayi mamakin kud'in, amma da taji anan mahaifin _Khalil_, sai mamakin ya sake ta don ta san irin kud'in da suke dashi. Mama tambayar Sarah tayi shin akwai wani gyara ne da ake mata na jiki a gida, sai Sarah ta fad'a mata babu abunda ake mata. A take mama ta kira waya aka turo mata number d'in wata kwararriyar mai gyaran jiki da yake tana home service. Cikin awa d'aya ta iso da duka kayan gyaran jiki. A cikin kud'in _Khalil_ da ya turo aka tura mata 200k domin soma fara yiwa Sarah gyaran jiki daga yau da daddare. Ai kuwa na dare d'aya tal sai da Sarah ta tabbatar an soma gyara jikinta. Baba da kansa yaje har d'akin Lami ya shaida mata y'an kawo akwati za su zo, sai da tayi masa kallon sama da k'asa tukun sannan tace, "To wata uwar zan yi masu da kazo ka tsaya min a kai?" Murmushi kawai baba yayi tare da juyawa ya koma d'aki don dama yaji a jikinsa babu wani abu da Lami za tayi shi yasa ma ya tura Sarah can gidan su Muneeba. Na'ima ce ta kalli Lami tare da fad'in, "Gaskiya Lami ba haka ake yi ba. Idan fa za'a kawo akwati, dangin amaryar sha tara na arziki suke yiwa dangin ango kamar irin su soye-soyen kaji, su meatpie, samosa, spring rolls da sauraransu har da tukwuicin kud'i. Kuma ni ina ji a jikina ba k'aramin kaya za'a kawo wa Sarah ba." Harara Aina'u ta makawa Na'ima tare da fad'in, "Munafuki annamimiya!" A cikin zuciyarta. Amma a zahiri sai cewa tayi, "Wallahi Lami kar kiyi komai. Kin san halin masu kud'in nan da shegen raini da d'aga kai kamar dan su Allah yayi duniyar." Da sauri Na'ima tace "Ke dai Aina'u annamimiya ce. Idan baza ki kashe wuta ba, to kar ma ki soma hurawa. Shegiya gwara dai ki fito da naki nashinshinin bar yiwa wata hassada. Ko sau d'aya bam tab'a jin wani yazo yana sallama dake ba." A fusace Lami tace, "Wannan wani irin maganar banza ce haka Na'ima? Ban so! Kar ki kuma yi mata irin wannan maganar. Ni kaf y'ay'ana babu wanda bai da farin jini. Farin jini a nono na kuka tsotsa." A fusace Aina'u tace, "Ni ko mai zan yiwa Hassana a jikin wannan banzan da zata aure! Allah ya kiyaye in auri wanda zan zama baiwarsa. Ai duk wata shegiyar da tayi aure ta san inda ta kai kanta. Daga wanke min kayana, dafa min abinci sai goge min takalmi. Sannan idan dare yayi ya kwashi romon albarkan jikin banza a banza ya tashi ya kakkab'e jikinsa kuma ba shi zai hana gobe yayi maki muzurai ba. Watak'ila ma naira d'ari biyu sai kinyi kamar za kiyi kuka ka mun ya cire ya baki. Allah ya sawake nayi aure! Ita ma da kuka ga ina nuna kamar ina jin haushi, sabida y'ar uwata ce ina hango mata wahala musamman da zata shiga gidan masu arziki. Kun ga sun samu y'ar aiki a sama wacce bata da salary." "Nace ba, da kike wannan hak'ik'icewar, ina naki tsayayyan kwarton?" Fad'in Na'ima tana harararta. Aina'u za tayi magana kenan Luckyboy ya fad'o d'akin tare da fad'in, "Ke Aina'u, gasu can a waje suna jiranki." Kwafa Aina'u tayi tare da mik'ewa babu ko gyale ta fice daga d'akin. "Kina ji ko Lami, dan Allah kar kibi shawarar Aina'u, kiyi amfani da kud'inki kiyi masu sha tara ta arziki, sannan gayya fa ake yi. Dole sai kin kira k'awayenki domin su zasu karb'i kayan ba ke ba." Fad'in Na'ima. "Wai maganar me kuke yi haka? Ni sallame ni kawai Lami in ware. Kuma eh, naga anyi eh ya ne a cikin gidan nan, amma ba'a bani rabona ba. Ke nan ni ba d'an gidan bane?" "Ungo wannan, tafi ni ka ishe ni." Fad'in Lami tare da mik'a masa dubu talatin. Da idanu Na'ima tabi kud'in sannan ta juyo ta kalli Lami bayan fitar Luckyboy tare da fad'in, "Lallai ma Lami! Dama duk uban kud'in da muke baki, da wanda _Khalil_ yake baki Lucky kike tattarawa kike ba yana tafiya shi da abokai suna shaye-shaye." Lami ko taro bata yi ba sai zurawa plasma TV tayi tana kallon arewa kamar bata san mai Na'imar ke cewa ba. Washa gari wajajen k'arfe biyu sai ga dirar motoci masu kawo lefe sun zo. Dama kuma Munee na gidan, da sauri ta fiddo waya ta kira mahaifiyarta ta shaida mata sun zo don ita ce tace su fad'a mata a waya idan sun k'ariso. Cikin k'ank'anin lokaci sai ga mama da tawagarta su k'ariso gidan hannunsu nik'i-nik'i da manyan kuloli. A nan tsakar gidan aka shimfid'a masu k'atoton tabarma. Su suka yi insisting sabida d'akin ba d'aukar su zai yi musamman da irin kayan da suka zo dashi. Aunty Maryam, aunty Khairat, kanwar Hajiya, matan uncles da matar ya Abdullah ne suka kawo kayan. Su suka fara shigowa, sai da suka gama gaisawa da mahaifiyar Munee da mutananta da ta gayyato. Na'ima kuwa hana Lami fitowa tayi don cewa tayi sai tayiwa Baba da mahaifiyar Munee tujara akan abunda suka yi mata. Sai zage-zage take tana fad'in akwai wani banzan alak'a tsakanin Baba da mahaifiyar Munee. Allah yaso babu wanda yaji abunda take fad'i sai Na'ima da take ta faman bata baki a d'aki. Kuma ta kulle d'akin ta ciki duk da kuwa tana so ita ma taje taga kayan da ta hanga ta window driver na wucewa dasu yana ajiyewa a nan tsakar gidan. Sai da ya kawo duka sannan aka soma bubbud'ewa. Babu abunda ke tashi sai kabbara da gud'an mata. Tun mata na irge har suka hak'ura don b'ata lissafi suke yi. Mata sai uban santi suke yi da gud'a. Gaba d'aya gidan ya cika da mutanen dake ganin kayan Sarah. Aina'u kuwa zawonta uku a cikin wando ganin mahaukatan kayan da aka zubawa Saran. Bayan an gama gani, mama ta ware na Baba, Lami da kuma wanda aka ce na k'annai da yayyin amarya ne ta ajiye a gefe, sauran kuma aka bar su nan tsakar gida. Dubu d'ari uku Baba ya bada matsayin tukwuicin duk da kuwa bai san adadin