Sashe 111
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 7 min read
faɗuwa ya kusa yi kuma dama gashi ba isasshen lafiya ba, nan muka tara Nuhu muna masa faɗa sosai. Wani ihu daya kwatsatsamin bani ba, hatta mahaifinsa sai da ya firgita, Nuhu babu kunya ya shiga cemin, 'Ke ba Mahaifiyata bace, baki isa ki yankewa gobena hukunci ba, don haka babu wani banzan da ya isa ya hanani auren Elizabeth Lami'. Dafe ƙirji Alyasa'a yayi tare da faɗin, har dani kake faɗawa haka Nuhu?' Nuhu sai ya riƙe ƙugu ya ɗage kai yana hura hanci. Zamewa ƙasa Alyasa'a yayi tare da kallona na buɗe baki zanji magana kenan yace, 'Bar shi Saratu, bar shi! Yaje duniya zata koya masa hankali. Ban amincewa ɗan da na haifa ya ƙara yi masa magana ba, sannan ban yarda ya ƙara zama min a cikin gida ba, sannan duk wani abu da yasan nawane, ya ajiye ya tafi!" Yana gama faɗin haka ya juya ya shige ɗaki. Ina kallon lokacin da yake share hawaye. Shi kuwa Nuhu kaɗa kai yayi ya fice yan faɗin 'To se me don an kore ni, duniya ai faɗi ce da ita.' wannan rana ita ce ranar da na saka Nuhu a idanuna na ƙarshe. Daga ƙarshe muka samu labarin wai ya musuluntar da Elizabeth har sunyi aure sun bar garin. Basu fi wata biyar da barin garin ba, Alyasa'a ya amsa kiran Ubangiji, amma kin san wani abu, tsakanin ɗa da mahaifa, kamun Alyasa'a ya cika sai da ya furta kalmar yafiya ga mahaifinki. Wannan shine labarin sanadin barin gida da mahaifinki yayi." Sosai Sarah ke kuka kamar ranta zai bar jiinta. "Nnanne ina ji a jikina Babana ba'a cikin hayyacinsa yayi maku duk abinda yayi maku ba, ke da kanki kin ce baban mamana matsafine, kuma yayi alƙawarin cikawa mamana burinta domin ya baƙantawa mahaifiyar mamana, to wallahi zai iya komai daga ciki har da juya kwakwalwar mamana. Kuma jikina ya bani, shi ya mayar da soyayyar da Babana kewa Aunty Rose Merry izuwa kan mamana domin ya samu cikar burinsa, tunda tun farko ai Aunty Rose Merry ɗin Baba ke so ba Mamana ba. Nnanne akwai alamar tambaya akan wannan batu!" Shuru Nnanne tayi na wasu daƙiƙu tare da faɗin, "To, Allah masanin gaibu Saratu. Mahaifin mamanki ne kawai zai iya warware wannan ƙullin, idan shi sanadi ko bashi bane." Da sauri Sarah ta kalleta tare da faɗin, "Yana nan a raye ne?" Jinjina kai Nnanne tayi tare da faɗin, "daga Samuel har pasto Emanuella Debora suna nan a raye!" Dafa Nnanne tayi tare da faɗin, "Nnanne idan kinyi min lamuni, zan je gidan domin na gana dashi mahaifin maman nawa." Murmushi Nnanne tayi tare da faɗin, "Bashi kaɗai ba, har ita pasto ɗin zan so ki kai mata ziyara. Idan kin nutsu zuwa gobe, zan saka a kai ki. Idan zaki tafi, zan baki kuɗi sai ƴar wajen Lukman ta raka yi." Da sauri Sarah tace, "Nnanne Ina da isassun kuɗi, Khalil ya bani ATMCARD ɗinsa domin nayi amfani da kuɗin ciki idan buƙatar haka ta taso." "To ma sha Allah!" Faɗin Nnanne. Sarah kuma tashi tayi tare da faɗin, "Nnanne zan fita na ciro kuɗin yanzu nayi sayayyar, kin ga goben sai dai kawai mu wuce." Gyaɗa mata kai Nnanne tayi. A nan gaban ƙofar gidansu ta ciri dubu hamsin. Kuma a wannan lokacin ne Khalil yaga alert ɗin kuɗi ya shigo wayarsa wanda hakan ya nuna masa inda Sarah take. Washa gari tun ƙarfe goma Sarah ta saka Suhana a gaba akan ta tashi su tafi gidan Samuel. "Wai ke baki da kunya ko? Kakanki ne kike kiran sunansa gatsau haka? Kaka Samuel zaki ce!" Harara Sarah ta maka mata tare da faɗin, "Anƙi ace kakan, kako ba kaka. Kaji wani suna wai Samuel!" Ta ƙarisa maganar tare da bushewa da dariya. "Baki da kirki maman twins!" Faɗin Suhana tana ƙarisa sakawa Sam'an takalmi. "Wai auntyn Sam'an, dasu za muje?" Faɗin Sarah. Hannun Sam'an ɗin ta kama tare da faɗin, "Kwarai kuwa! Sauban muje kaji." Ta faɗi tana riƙe hannayensu. Komai Sarah bata ce ba har suka fito parlourn, matar ba Lukman suka samu a parlour, "Aunty zamu wuce!" Faɗin Sarah. "To Sarah, Kar dai a manta ayi addu'a, sannan idan sun baku nama, kar kuci." Da "To" suka amsa sannan suka fita daga ɗakin, sai da suka ƙara zuwa wajen Nnanne suka yi mata sallama sannan suka fito. Kasancewar babu nisa, a ƙafa suka yi ta takawa har suka gangara, sun zo wajen ƙofar gidan wani makeken gida wanda gaba ɗaya wanda shi ya haska unguwar, sai Suhana ta taɓo Sarah tare da faɗin, "Sis ga gidan kakarki, pasto Emanuella Debora." Ɗaga kai Sarah tayi, babu abunda idanunta suka fara ganin sai tafkeken sunanta a jikin saman gidan, _Pasto Emanuella Debora Gabriel House_. "Lallai matarnan taji kuɗi, duk wannan uban gidan nata ne?" Gyaɗa mata kai Suhana tayi tare da faɗin, "Kuma ƴata rak kawai gareta, Mahaifiyarki!" Taɓe baki Sarah tayi suka cigaba da tafiya har zuwa wani ƙaton ginin ƙasa, rabin katangar ta zube kana iya hango mutanan dake ciki, ga manya-manyan tukwane nan a kan murhun duwatsu har huɗu, gefe kuma ƴan matane su kusan bakwai da ɗaurin ƙirji, wasu kuma ɗan siketi ni iya ƙauri sai riga da bata gama rufe cibiya ba da uban kitson attachment har baya, farcen hannu zaƙo-zaƙo da ƙumba. Wasu tsoffi kuma zagaye a akan wani banci suna wani abun da su Sarah basu sani ba don basu iya hangowa. Can gefe kuma samarine da manyansu suna shan wani abu a kofi, wasu kuma suna buɗe wannan tukunyar suna ɗeban abun ciki suna sha. "Kin ga wancen abun da suke sha a kofi, sunansa burkutu." Faɗin Suhana. "Burkutu dai!" Sarah ta faɗi tana kallon Suhana, jinjina mata kai tayi daidai lokacin da suka iso ƙofar gidan. "Gafaranku dai!" Faɗin Suhana. Gaba ɗaya mutanan gidan suka zuba masu idanu, "Lafiya?" Wata budurwa mai ɗaurin ƙirji ta faɗi. "Mun zo wajen baba Samuel ne." Faɗin Suhana. Da hannu suka yi masu nuni da ɗakin, domin idan da sabo sun saba ganin musulmai suna zuwa gidan wajen baba Samuel domin yayi masu aikin asiri kasancewarsa shahararren matsafi. Daga asabarin dake ƙofar suka yi sannan suka shiga. Ɗagowa wani tsamurarren tsoho yayi tare da kallonsu, wani murmushi ya saki sannan ya nuna masu wajen zama tare da kallon Sarah yace mata, "Jikata, ƴa ga Elizabeth! Kin zo nan ne domin son sanin mahaifinki Nuhu yana cikin hayyacinsa ya ƙi bin umarnin Mahaifansa ya auri Elizabeth ko?" Da mugun mamaki Sarah ta kalli Suhan sannan ta mayar da kallonta izuwa ga Baba Samuel. Murmushi yayi tare da nuna mata tukunyar tsafin dake gabansa, sannan yace, "Duk wanda ya iso ƙofar gidana tukunyar tsafina take faɗa min zuwansa da kuma abunda ya kawosa gare ni. Ina ƴata Elizabeth?" Shuri Sarah tayi tana kallonsa, babu ta inda ta hango kamannin mamanta a jikin wannan yamutsatstsan tsohon, sai dai tabbas taga wani baƙin halitta dake cikin kwayan idanunsa wanda akwai shi sak a idanun Lami. Dariya Baba Samuel yayi mai sauti wanda ya saka Sarah saurin kallonsa ita da Suhana. "Tabbas hasashenki gaskiya ne! Ni na juya tunanin mahaifinki, sannan ni na sanya soyayyar ƙawar mahaifiyarki ya juye na mahaifiyarki a zuciyar babanki, Elizabeth bata taɓa son Nuhu ba, haka Nuhu bai taɓa son Elizabeth ba, nayi amfani da dutse ɗaya ne na jefi tsuntsu biyu, na haɗa wannan soyayyar ne domin in wulaƙanta tsohuwar matata pasto Emanuella Debora Gabriel, na biyu kuma domin in rama abunda mahaifin Rose Merry yayi min, kuma naji daɗi sosai saboda na rama komai cikin sauƙi." Ya ƙarisa maganar yana dariyar jin daɗi. Miƙewa Sarah tayi tare da kama hannun Suhan tace, "Tashi mu tafi Suhan, tsoro tsohon nan yake bani!" "Mijinki yana hanya, yanzu haka yana cikin unguwar nan yana cigiyar gidanku, sannan nan da wasu kwanaki masu zuwa, mijinki zai sake auren wata ƴarinya kyakkyawa wacce za tayi yunƙurin kwace maki fada a cikin gidanki, baza ku taɓa jituwa da ita ba, yarinya ce mai tsananin kishi, sannan uwar mijinki bata sonki yanzu, kuma akwai wani abun mamaki da zai faru kuma zai girgiza uwar miji kuma sannan........." "Muje Suhan!" Sarah ta faɗi da ƙarfi jikinta na rawa. Da sauri Suhan ɗin tayi gaba, yayin da Baba Samuel ya ɗaga murya tare da faɗin, "Idan kina neman wani taimako, kiyi gaggawan zuwa nan, cikin ƴan daƙiƙu zan gyara maki komai."