Sashe 80
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
fi son shi juyo ga barin muguntassa, shi kuma yi rai; Ya bada iko da umurni ga masu-bautansa su furta, su fadi kuma ga mutanensa da su ke tuba da neman gafarar zunubansu. Allah ke gafartawa, yana kwancewa dukan masu-tuba da gaskiya, masu-bada gaskiya ga bisharassa mai-tsarki ba da munafunchi ba. Domin mu roke shi, shi ba mu tuba mai-gaskiya, da Ruhunsa Mai-tsarki, domin abubuwan da mu ke yi yanzu su gamshe shi; kuma sauran ranmu da ke nan gaba shiyi tsabta da tsarki, domin hakkanan a-karewa mu zo chikkin farin cikinsa na har abada, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu. Ubangiji kar kayi duba ga saɓon yarinyata, ka yafe mata a cikin yafiyarka mai girma! Ka juyo da hankali da tunaninta ta gane gaskiya a cikin addinin ka ya Yesu Almasihu! Mijina kuma ka bashi lafiya da juriya duk da ya ɓace daga gaskiya, kar kayi duba da laifinsa, ka samu a cikin aljanna gaba ɗaya, Amin._" Wani irin dariya ne ya kusa kufcewa Khalil jin yanda surukar tasa ta dage da iya ƙarfinta tana addu'arsu ta kirista, gefe guda kuma yana jimamin rashin hankali irin na ƴan uwan matan nasa. "Ubangiji ba ya kare mu da komawa addininki Lami! Duk da nasan ba kullum nake sallah ba, amma bana fatan in mutu a cikin addinin Kirista, ai na taɓa jin wani wa'azi akan duk wanda yace La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi, ba zai taɓa dauwama a wuta ba, so ina da hope ɗin zan shiga ko da kuwa wuta na fara shiga." Faɗin Marfu'a, da sauri Khalil ya juyo kuma hakan yayi daidai da wani uban burki da ya taka duk sai da suka tsorata, "Ke wacce irin jahila ce? Kina hauka ne? Kin san mecece wutar ubangiji kuwa? Ƙarya kike yi wallahi, baza ki taɓa iya jurewa azabar Allah ba, kar ki kuskura ki ƙara faɗin wannan kalmar, kiyi fatan ko hucin wuta kada Allah yasa kiji bare ki shiga ko da kuwa na daƙiƙa ɗaya ne! Wai tsaya, dukan ku kun taɓa zaman aji na islamiyya kuwa?" Girgiza kai suka yi gaba ɗaya. Dogon tsaki Khalil yaja tare da faɗin, "Akwai babban matsala!" Yana gama faɗin haka ya kunna motar tare da cigaba da tafiya ransa a ɓace. Har suka isa asibitinsa babu wanda ya ƙara ko tari, nan da nan aka shiga da baba emergency, sakamakon gwaje-gwajen da akai masa ya nuna jininsa yayi mugun hawa, wanda hakan yayi sanadin faɗuwarsa har ya samu mutuwar ɓarin jiki, ga kuma ciwon zuciya da ya kai matakin stage C. Sosai Khalil ya girgiza da ganin haka, abunda ya kawo ransa shine halin da ƴaƴansa da kuma matarsa ya kaisa wannan stage ɗin saboda tara abu a zuciya. Aina'u na shiga ɗaki ta soma jin wani irin kuuwa a kunnanta har sai da ta saka hannu biyu ta toshe kunnan tare da durƙushewa a ƙasa, can ta soma ji ana ɓarke kayan jikinta, sai da aka mata tsirara sannan aka kwara mata wani irin balaƴenƴen ruwan sayi mai ƙanƙara-ƙanƙara a jiki sannan aka shiga zubaba mata bulalan doki a jikin, yanda ƙaran dukan ke fita zaka fahimci ba wai mutum ko aljani ɗaya bane ke dukan, da wannan yace waaap, sai wannan yace shauuuu! Ba ƙaramin duka taci ba, don tun da ta shiga ciki ake dukanta har wajajan goman Safiya, ta suma yafi sau a ƙirga, gaba ɗaya jikini yayi ruɗu-ruɗu, sannan kuma aka shafe jikin da gishiri da yaji. Tsabar azaba Aina'u zawo ta dunga saki a kwance a ƙasan tiles. A can asibiti kuwa, duk wanda ya kalli yanda baba ya koma lokaci guda sai ka tausaya masa, ido ya juye, hannun da ƙafa na ɓarin dama sun shanye, harce kuma ya karye, basu Na'ima kaɗai ba, hatta Lami sai da ta fashe da kuka. Khalil jan su Na'iman gefe yayi ya shiga yi masu nasiha mai ratsa jiki, sannan ya shaida masu abubuwan da suke aikatawa ne ya jefa baba a cikin halin da yake ciki, sannan yayi masu alƙawarin idan har sun tuba sun komawa Allah duk sun daina yawace-yawacen da suke yi, shi kuma yayi masu alƙawarin akan su sai inda ƙarfinsa ya ƙare, kuma daga yau in dai kuɗi suke nema to su tambayesa, sannan ya bawa kowaccen su damar nemo sana'ar da zata riƙa yi shikuma daga nera ɗaya zuwa miliyan biyu zai bawa kowaccen su ta kama sana'a domin rufawa kai asiri, ya ƙara da faɗa masu duk wacce ta natsu a cikinsu in Sha Allah tana zaune Allah zai kawo mata mijin marainiya ya aurenta. Sannan kuma yace dukkansu sai sun koma islamiyya. Lami ma ya kirata gefe yayi ta rioƙonta akan dan girman Allah ta daina ingiza ƴaƴanta suna yin karuwanci, idan har kuɗi take buƙata tana da number ɗinsa ta kira ko nawa take da buƙata shi kuma yayi alƙawarin zai bata. Ranar dai kowa jigum-jigum ya kwana, Lami kuwa lokacin da Khalil ya kaita ɗakin da babies ɗin suke, kamar ta ɗebesu haka taji, wani irin ƙaunar yaran ya shigeta. Sarah kuwa ganin daga ƴan uwan nata har Lami duk sun koma wani silent, sai taji wani irin daɗi da natsuwa ya kamata. Babu wanda ya faɗa mata baba na asibitin har sai da ya kwana goma, Duk yanda suka ɗauka Sarah zata tashi hankalinta, sai suka ga tashin hankali yafi kwatancesu, kuka kuwa kwana tayi tana yi, yaran kuwa ƙin zuwa tayi ta basu nono saboda haushin Khalil da take ji na ɓoye mata mutuwa har biyu da kuma rashin lafiyar baban, don mutuwar Rabo ɗan wajen Na'ima da kuma Nafeesa, duk a ranar aka faɗa mata, tayi kuka kamar ranta zai bar jikinta har sai da jininta ya sake hawa. Dakyar Hajiya da Khalil suka lallasheta. Lami kuwa hankalinta gaba ɗaya ya koma wajen Aina'u ganin bata ganta a asibiti ba, rabon da ta saka Aina'un a idanunta ma har ta manta, duk a tunaninta tana wajen yawace-yawacen banzanta ne, haka nan sai taji hankalinta ya mugun tashi don ko lokacin da su Na'iman suke tashen yawon bin maza, basu wuce kwana uku ko sati a waje, sannan duk ranar duniya sai sunyi waya da ita, amma Aina'u kusan watanni uku kenan rabon da ta ganta kuma babu kiran waya, ko Lamin ta kira ta a waya bata ɗauka. Tagumi Lami ta zabga tana kallon baba da ya koma kamar wani tsumma, a hakan ma wai don yana Asibitin da ake kula dashi kenan! Ƙara kunnanta tayi zuwa bakin baba ganin magana yake yi amma bata jin abunda yake furtawa, don harcen ya riga ya karye. Sarah dake kusa dashi don kullum tana tare dashi, anan kuma take kwana duk da Lami da Na'ima suma suna nan, itama ta kawo nata kunnan amma bata fahimta ba, fita tayi ta kirawo Khalil domin yazo yaji ko shi zai gane, ko da Khalil yazo ya kara nashi kunnan, sai yaji kamar yana cewa Aliyu cikin karyewar harce, sai ya ɗago ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama Ni dai ji nayi kamar yana faɗin Aliyu, kuna da wani ne mai suna haka?" Girgiza kai tayi tare da faɗin, "Gaskiya babu, da dai ma Lukman yace, sai ince ɗansa namiji yake nema." Da mamaki Khalil ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama dama kina da ɗa namiji?" Gyaɗa kai tayi tare da share guntun hawaye tana kuma jin tsoron da kunyar faɗin Lukman ya mutu da kuma sanadin mutuwar tasa don ko ƴan uwansa basu sani ba, daga ita sai ƙawarta Aunty Rose Merry suka san komai, su Na'ima kuwa sun ɗauka yana can yawon banza da sace-sacen da ya saba. Khalil bai ƙara cewa komai ba sai juyawa da yayi ya kalli baba dake ta ƙoƙarin magana amma babu baki, kuma ba kowa yake kira ba sai Aina'u yana faɗin, "Allah ya isa tsakanina da Aina'u" su Khalil kuma Aina'un kawai suke ji shima kuma cikin karyewar harce sai kalmar yake yi masu kamar Aliyu. Bayan fitan Khalil daga ɗakin sai Lami ta juyo ta kalli Sarah tare da faɗin, "Sarah, kin san kuwa har yanzu babu wanda yasan inda Aina'u take! Yau watanni uku kenan rabon da na saka ta a idanu." Da sauri Sarah ta kalli Lami tare da faɗin, "Wai dama baku san tana gidana ba? Ai tana can wajen Hajiya, Maman Khalil." Da mamaki Lami tace, "Gidanki? Tun yaushe?" Sarah tace, "Ai ta jima, zata kai kusan watanni ukun da kwanaki, duk da nima sai in haɗa sati biyu ban ganta ba." Riƙe haɓa Lami tayi tare da faɗin, "Lallai Aina'u! Yanzu kuma ta san babanku ba lafiya amma ta rasa zuwa duba shi." Watsa hannu Sarah tayi tare da faɗin, "Ohooo! Ta damu dashi ne? Ni wallahi Lami, wani lokacin Aina'u tsoro take bani. Tana da mugun hali." Wani irin jijjiga baba ya fara yi yana watsa hannunsa na dama alamar dai magana yake yi amma babu mai gane abunda yake cewa, kuma Sarah yake kallo yana watsa hannun. Fadi yake Sarah ta kori Aina'u a gidanta, amma kuma bata gane ba sai kukan da take yi ganin yanda ya burkice, fita tayi da gudu tayi office ɗin Khalil, yana ciki yana duba wata petient ta afka tare da kamo hannunsa zuwa ɗakin baban. Allurar bacci yayi masa, nan da nan baccin ya kwashesa, sannan Khalil yace duk su fita daga ɗakin su bar shi ya huta. Aina'u kuwa kwananta goma a ɗakin Hajiya babu ci babu sha sai ƙarban azaba daga hannun _Hell Ofulafu_ take yi babu ƙaƙƙautawa. Dukan safe daban, na rana da ban, haka na dare. Kuma har wannan lokacin Hajiya bata san da dawowarta ba, ba ƙaramin alwashi da mugun nufi Aina'u take yi ba a zuciyarta duk lokacin da ta samu sassauci da yafiyar Hell, wani irin tsanar Sarah ta kuma ji ya ninku a zuciyarta. Watan su Sarah ɗaya a asibiti aka sallame su, idan kaga twins baza ka taɓa cewa bakwaini bane, sun yi ƙiba abunsu, haka ma Sarah ta ƙara cika tayi kyau, baba ma an sallame shi duk da jikin na nan dai jiya i yau, sai dai Khalil yace zai riƙa zuwa har gida yana yi masa gashi wanda in Sha Allah zai taimakawa jikin nasa. Satin na zagayo da