Sashe 12
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read
kamata ki taimaka mata ta wanko jikin nata sai ku tafi asibitin." Mik'ewa Aina'u tayi don har ta zauna tare k'arisawa ta amshi kud'in sannan tace, "Ko kai fa d'an tsoho. Tsohon nan kud'i fa gare ka naga alama!" K'ala bai cewa Aina'u ba, sai ma kallon Sarah da yayi tare da fad'in, "Allah ya baki lafiya." Sannan ya juya ya shige d'akinsa. Aina'u kuwa, k'arisawa wajen Sarah tayi ta kamata ta mik'e ta kaita har gindin pamfo ta wanke mata jiki. "Aina'u taimaka min da fanta mai sanyi a shago dan Allah. Akwai naira dubu d'ari biyu, ki d'auki d'ari biyun ki sayo min." Matsawa baya kad'an tayi tare da fad'in, "To ki tabbata shima akwai kud'insa daban. Don yasin ban aikin banza." Sarah na nishi tace, "Naji ji ki sayo min. Idan muka fita zan cire kud'i a POS sai in biya ki." Ba tare da Aina'u tace komai ba ta juya ta nufi d'akinsu Saran ta d'auko d'ari biyun ta fito ta nufi waje don sayo Fantan. Sarah kuma da kyar ta iya jan jiki ta koma d'akin. Sai da ta d'an yi jimm kamun ta tura k'ofar ta shiga saboda bata son ganin abunda ta baro a cikin d'akin. Alhamdulillah Hassanar ta gama abunda take yi, kwance ma same ta tana kwasar barci. Kai tsaye wajen wardrobe ta nufa ta canza kayan jikinta ta zauna a k'asa tana nishi. Don wani irin juwa take gani. Aina'u ce ta hankad'o labulen ta shigo d'akin tare da dire mata kwalbar fanta a gabanta mai sanyi. "Nagode Aina'u!" Shine abunda Sarah ta fad'i tare da kai kwalbar bakinta ta cire kwankwalatin ta hau shan fantar. Kad'an tasha taji kamar za tayi amai sai ta mayar da kwankwalatin ta rufe ta ajiye a gefe tare da mik'ewa ta d'auki hijjab ta saka ta cewa Aina'u, "Muje Aina'u. Zamu d'an tsaya a shagon Nura zan cire kud'i, taimaka min ki d'au min jakata." Jakar ta d'aukar mata suka fita daga d'akin. "Lami mun tafi." Fad'in Aina'u. "To sai kun dawo. Ki tabbatar kin karb'i kud'inki." Wani murmushi Aina'u tayi tare da fad'in, "Kin san wannan dole ne Lami, sai dai mun dawo d'in." Ita dai Sarah bata ce komai ba ta nufi hanyar k'ofar gida. Sai da suka biya ta shagon Nura Sarah ta cire 11k ta bawa Aina'u 1k na sayo mata fanta da tayi sannan suka tsari napep suka shiga. "Ina zamu je Hajiyoyi?" Fad'in mai napep. "Ka kai mu wani asibiti mai kyau da kasan sun san aikin su sosai." "An gama Hajiya!" Fad'in mai napep d'in. Sun d'an yi tafiya mai tsayi mai napep d'in ya tsaya a bakin wani katafaren asibiti kamar ba a k'asar Nigeria ba, a saman asibitin an rubuta *_Khalilullah Specialist hospital_* "Kai! Kana hauka ne da zaka kawo mu wannan asibitin? Shin baka san tsadar asibitin bane?" Fad'in Aina'u. Ko kamun mai napep yace wani abu, Sarah ta sauko daga keken tare da zaro dubu d'aya ta mik'a masa ya cire kud'insa ya bata canji. Sai a sannan ya kalli Aina'u tare da fad'in, "Ai gani nayi kunyi kalar asibitin shiyasa na kawo ku nan d'in." Harara ta zabga masa tare da bin bayan Sarah da har ta kusa shiga cikin gate d'in. Sai da ta d'an had'a da gudu tukun ta isketa tare da fad'in, "wannan wani irin iskanci ne haka zaki wuce ki barni? Don kin samu na rakoki ko? Gobe rana ce ai!" Ba tare da Sarah ta kalleta ba tace, "Yau d'in ma kud'i nane dana Baba ya sakaki taimako na, gobe ma idan kika ga kud'in, biyo ni za kiyi." Aina'u bata kuma cewa komai ba har suka shiga reception d'in asibitin. Gaba d'aya numfashinsu ya kusa d'aukewa sabida tsabar had'uwar da asibitin yayi. Aina'u kuwa baki bud'e take bin lungu da sak'on asibitin da kallo. "Baiwar Allah dan Allah Ina zan je na bud'e file?" Fad'in Sarah bayan ta tab'o wata nurse da tazo wuce wa. Da hannu nurse d'in tayi mata nuni da wajen sannan ta wuce. Sarah kuwa k'arisawa tayi tare da yin sallama ta gaishe da saurayin da ta gani a wajen sannan tace, "File nake so a bud'e min. Ina son ganin doctor." Wani file ya d'auko tare da kallonta ya mik'a mata wani k'aramar paper tare da fad'in "Je ki biya wannan a wajen cashier sai ki dawo min da receipt d'in." Karb'a tayi tare da fad'in, "Ina ne wajen dan Allah?" Shima da hannu ya nuna mata wajen. Tana zuwa ta mik'a masu papern, matar dake wajen ta d'ago ta kalleta tare da fad'in, "Kud'in ki dubu bakwai. Don kinyi sa'a babban doctor ne zai duba ki. Bud'e file dubu biyu, sai kud'in ganin likita dubu biyar. Shuru Sarah tayi, domin idan ta bada 7k saura 2k a jikinta. Da mai zata biya kud'in scanning? Don ta san tabbas za ayi mata scanning. Aina'u ce tazo wajen ta tsaya, Sarah tayi saurin cewa, "Dan girman Allah Aina'u aramin dubu hud'un hannunki, idan mun koma gida zan baki." Ciro kud'in Aina'u tayi ta mik'a mata tare da fad'in, "Amma fa ki sani, wallahi sun haifu. Ba dubu hud'u zaki mayar min ba." Komai Sarah bata ce mata ba. Sai mik'awa cashier kud'in tayi tare da mik'a mata receipt ita kuma ta karb'a ta koma wajen wanda ke bud'a file ta mik'a masa. Sunanta ya tambaya tare da age, adresss da kuma phone number sannan ya nuna mata inda zata je tare da shaida mata ya turawa doctor file d'inta ta computer. Consultant room taga an rubuta a sama. Har zata murd'a sai kuma ta d'an tsaya jim ta juyo ta kalli Aina'u dake zaune a kan kujera ta d'aura k'afa d'aya a kan d'aya tana danna waya. Ajiyar zuciya ta sauke tana fatan ace wannan karon idan an dubata ace wani ciwo ne daban a jikinta ba ciki ba. Kwankwasa k'ofar tayi sannan ta tura ta shiga. Wani gaurayayyen sanyi Ac taji ya ratsata mai tafe da wani k'amshi mai shiga zuciya da b'argon d'an Adam. Har sai da Sarah ta lumshe idanu tana mai fatan ace ta cigaba da jin wannan k'amshi har abada saboda yanda yayi mata wani irin dad'i da salama a cikin zuciyarta. Ba tare da ya d'ago kai ba yayi mata nuni da kujerar dake gaban teburinsa. Zama tayi tana mai wasa da hannunta. Shi kuwa doctor wani rubuce-rubuce yake yi a jikin wani file. Ya d'auki mintuna uku kamun ya ajiye file d'in ya zare glasses d'in dake fuskansa sannan ya juyo da computer yayi danne-danne tare da fad'in, "Saratu Nuhu ko?" Ya fad'i hakane tare da juyowa ya kalleta dai-dai lokacin da itama ta d'ago kai idanunsu suka sark'e dana juna. A mugun firgice Sarah ta mik'e tare da tura kujeran da take kai baya gabanta na wani irin mugaba kamar yanda dak'ik'an agogo yake bugawa. Bakinta na rawa tace, "kkkk.... Kai!" Shima da matuk'ar mamaki ganinta ya furta, "Ke ce?" Da sauri ta juya ta fita daga office d'in har tana k'ok'arin kifawa tayi saurin dafe bango. Aina'u dake charting ganinta kawai tayi ta fito kamar wacce aka biyo ta tayi waje da sauri. Ita ma mik'ewar tayi tana fad'in, "Sarah! Sarah!! Lafiya?" Dai-dai lokacin ya fito shima ya bita a baya, Aina'u na ganin haka ta rufa masu baya amma suna isa wajen gate d'in suka ganta har ta hau napep, napep d'in ya wuce. Juyawa Aina'u tayi ta kallesa tare da fad'in, "Lafiya? Mai ka mata? Ko HIV kuka gano tana d'auke dashi?" Wani irin kallo Khalil yayi mata tare da fad'in, "Ni ko dubata ban yi ba. Kin santa ne?" Ya tambaya duk da kuwa yana ganin kamannin jini a fuskar Aina'un. "K'anwarta ce ni. Ni ke binta." Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in, "Ko zaki shigo mita muje in sauke ki sai in san gidan naku daga nan." Wani kallon up and down tayi masa, ganin babu k'arya sai tace, "To amma kai mai yasa kake son zuwa kaga gidan mu?" Kai tsaye ya bata amsa da, "Saboda ina son had'uwa da yayarki. Auren ta nake son yi. Na jima ina naimanta sai yau Allah ya had'a ni da ita." Wani dariya rainin hankali Aina'u ta kwashe dashi tare da fad'in, "Lallai! To ka ko san abunda ya kawota nan asibitin? To bud'e kunnuwanka da kyau in fad'a maka. Ciki ne da ita har na tsawon watanni uku, kuma zuwa tayi nan domin a zubar mata da cikin. Mu gidan mu bamu aure. Kar ka wahalar da kanka don baza ka tab'a samun Sarah matsayin mata ba. Ko da yake, ban san tsananin son da kake mata zai saka kayi auren ragowar wani ba. Ni na barka lafiya." Tana gama fad'in haka tayi gaba. Shi kuwa Khalil mutuwar tsaye yayi kansa na wani irin juyawa jin wai wacce yake matuk'ar k'auna ce take d'auke da juna biyu. Tirr ya auri mazinaciya a rayuwarsa. Idan kuma hakan ta faru, daran ranar da ya fahimci haka, a ranar zai korata gidansu. Don ya san zama da zargi babu aure, shi kuma ba zai tab'a iya auren yarinyar da zuciyarsa zai rik'a kokwanto a kanta ba. Har ya fara tafiya ya tsaya cak tare da maimaita abunda Aka Aina'u tace masa cikin zuciyarsa "Ciki wata biyu? Kai ba zai tab'a yuwuwa ba." ya fad'i a bayyane tare da bin bayan Aina'u da sauri.............