← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 112

Sashe 3

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sarah dake matsar hawaye zaune a bakin gado ta mik'e ta fito ta tsaya nan daga bakin k'ofa ba tare da ta kalli inda su Lamin suke ba. Sama kawai ta zubawa idanu tana kallon hadarin da ke k'ara had'uwa. "Oh ni inzo nan ke nan in same ki ko, shafaffa da mai!" Fad'in Lami a fusace kamar zata yo kanta. A hankali Sarah ta sauko daga kan dandamalin k'ofar d'akin ta nufi inda su Lamin suke tana kallon k'asa. "Munafuka annamimiya, makira! Sai ki rik'a yi sumumi-sumumi kamar ta kirki, ashe a bayan fage Allah kad'ai ya san abubuwan da kike shukawa. Ya kiyi magana ko sai na hamb'are ki a nan wajen?" Lami ta fad'i tana mai kai mata duka Sarah tayi saurin kaucewa. "Lami wannan yarinyar fa ba magana za tayi ba sai ki had'a mata da duka. Kin fi kowa sanin irin taurin kai da kafiyarta tun tana k'ank'anuwarta. Ke kika bamu labari idan tayi zuciya ko nono kika bata bata karb'a, idan kuma kika matsa mata ta kama, to ranar kan nonon ki kamar zai tsinke tsabar cizon da take ganna maki. Ai wannan yarinyar jaraba ce a gidan nan. Ita ta d'ebo halin tsoho kaf!" Fad'in Hassana tana hararar Sarah. Sarah kuwa wani d'agowa tayi ta watsa mata harara tare da fad'in, "Idan ni annoba ce, ke kuma wulak'antacciya tsinanniya mai zagin uban da yayi sanadiyar zuwan ki duniya! Na gwammaci inyi ta d'ebo hali da dabi'un mahaifina har k'arshen rayuwata da in d'auki irin naku halin. Ko kunya bakya ji, babu aure amma kin ajiye y'ay'a uku duk shegu. Kuma a hake kike fita kina yawo kowa ba kallon ki yana nuna ki a unguwa. Ku jawo mana abun fad'a da zai bibiyi tsatson mu har k'arshen mu. Allah ya isa tsakani na daku kun hana ni aure saboda mugayen halayen ku. Duk wanda ya fara zuwa waje na, k'ark'arinsa sati d'aya, shima kamun ya gano asalin su wanene y'an gidan mu. Yana ganowa yake blocking d'ina kuma ba zai sake dawowa ba." Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka. "Kutumar bura uba......! Lami kina jin irin maganganun da y'ar iskar yarinyar take min a cikin gidan nan ko!" Fad'in Hassana tana mai nuna Sarah da hannu tare da girgiza jiki. Kau da fuska Sarah tayi tana mai kallon gefe. Lamin kuwa d'aga hannu tayi ta wanke fuskan Sarah da mari sai da tayi taga-taga zata fad'i, sai Allah ya taimaka ta tsaya da k'afafunta tare da dafe fuskan tana kallon Lamin hawaye na zubo mata. "Dan uban ki Nuhu, ita sa'ar ki ce da zaki tsaya kina mata rashin kunya? Ta tara y'ay'an shegun dan ubanki! Ke menene wannan yanzu a cikin ki? Shegiya kema kina tare da abun gorin amma kike yiwa wata. Za kici ubanki dani a cikin gidan nan idan na kafa maki k'ahon zuk'a." Fad'in Lami tana mai nuna ta da yatsa. "Lami ke baki gano ta bane? So take ki mance da maganar da kika soma na sai ta fad'a maki uban cikin dake jikinta." Fad'in Marfu'a. "Kwarai sai yanzu na fahimci zancen Marfu'a. To ban mance ba dan ubanki. Uban wa ya yayi maki tsirara ya kwashi albarkatun roman jikin ki? Nace wani shegen ne yanzu in fita in kwankwasi gidan su?" Fad'in Lami tana mai jawo Sarah gabanta. Sarah kuwa wani kukan ta kuma fashewa dashi tare da duk'awa a wajen tana fad'in, "Ni dai Allah ya san cewa babu namijin da ya tab'a kaiwa ga jikina. Ni ban ta yaya ciki ya shiga jikina ba wallahi." Baki sake Lami da y'an uwan ta suka bita da idanu. Na'ima ce tayi k'arfin halin fad'in, "To a ruwa kika sha dab kutumar uban ki? Kuji min shegiyar yarinya zata mai damu y'an iska wanda basu san inda ke masu ciwo ba." Lami kuwa tsabar takaici bata san lokacin da ta kai k'asa inda Sarah take duk'e ta shak'o wuyarta tare da wanke fuskanta da mari hagu da dama sannan ta tura ta baya ta fad'i dab'as sai da ta dafi k'asa da duka hannayenta biyu. "Ku shiga d'aki ko waccen ku ta d'auko lafiyayyan bulalanta kuyi ta jibgar shegiya har sai ta magantu tukun zaku kyaleta. Ni anya kuwa ba canje aka yi min a asibiti ba kuwa?" Lami ta fad'i tana shurin Sarah da k'afafunta. Gab'a d'ayan su kuwa dama cike suke da ita, ko wacce ta d'auko bulalanta a hannunta tayo kan Sarah suka shiga lafta mata bulala ta ko'ina a jikinta. Tsabar zuciya irin na Sarah ko gezau, kuma gashi tana jin azaba duk sanda bulalar ta sauka a fatar jikinta. Don har rige-rige suke yi wajen aje bulalar a kan fatarta. Ita burinta d'aya, Allah yasa wajen dukan nata su zubar da cikin dake jikinta ta huta da mugun abun kunyar nan da take d'auke dashi. "Wallahi duk wacce ta k'ara kai duka jikinta sai ta bar gidan nan a cikin daren nan tunda ba gidan uwar ku bane." Fad'in mahaifin su da fitowarsa kenan daga cikin d'akinsa. Wani yamutsatstsan tsohe wanda wahalar rayuwa duk ta gama cinyesa ya fad'i hakan hannunsa rik'e da sanda yana dogarawa har ya k'ariso inda Sarah ke duk'e a k'asa. D'aga sandar yayi kamar zai makawa Na'ima da ta kuma d'aga bulalar zata zabgawa Sarah, sai tayi saurin ja baya tare da fad'in, "Kul! Wallahi kar ka kuskura ka tab'a ni da k'azamar sandan nan naka. Don kana sauke min sandar a jiki, kaji na rantse maka sai na rama." Ta fad'i hakane tana mai zaro masa idanu kamar shima zata kai masa bulalar dake hannunta. Mik'ewa Sarah tayi a zafafe tare da fad'in, "Wallahi kika tab'a jikin mahaifina sai na kashe ki a cikin gidan nan, ai nafi shekaru sha takwas a duniya, hakan na nufin na isa d'auri." Matsowa kusa da Sarah yayi yana d'ingishi tare da fad'in, "Kul, Saratu! Kar in kuma jin kin sake furta irin wannan maganar. Ke d'in yarinyar albarka ce. Ki barta, duniya ta ishi kowa riga da wando, wanda bai shigo bama jiransa take yi. Kiyi hak'uri kin ji. Koma d'aki. Idan kowa be yarda da ke va, bi na yarda dake y'ata. Ke kuma, kije Allah ya isa tsakani dake. Allah zai min sakayya Lami." Wani irin gud'a Lami ta saki tare da fad'in, "Wallahi Allah ya isar ka babu inda zata je sai dai ta koma kanka. Ai nice ma ya kamata nayi maka Allah ya isa irin wannan uk'uba da na sha a gidan ka kamun Allah ya wanke y'ay'a mata shidda ya bani. Dan ma dai gud'a d'aya a cikin su azzaluma ce mai irin halin ka wacce bata son share min hawaye. Yanzu wannan akurkin kake tutiya dashi har kake kira gida? Lallai! Bayan da ba dun taimakon su y'ay'an da kullum kake zagi da ikirarin zaka kore su sun taimaka sun d'an yi gyare-gyare a gidan ba, har zai kallu balle ma a kira sa gida. Ka dai ji kunya wallahi Nuhu. Kuma y'ay'ana babu inda zasu je. Zama a cikin gidan nan dole, idan kaji ana daram dam-dam to ni da y'ay'ana kenan a cikin gidan nan. Sai dai idan kai ne zaka fice ka bamu waje don billahil lazi naci gida! Y'ay'a bakwai na haifar maka, d'aya namiji, sai tsala-tsalan mata har shidda. Ni ai wallahi har yau tsinewa soyayya nake yi da har ta rufe min idanu ta jani da kyawuna na fuska da na jiki amma na b'uge da auren fak'iri irin ka wanda aka haifesa da bak'in fentin talauci. Nuhu ka fita harkata da ta y'ay'ana tun kan in kai ka k'ara kotu a raba tsakanin mu." Wani dogon tsaki Nuratu taja tare da fad'in, "Ni wallahi Lami ban san mai kike yi har yanzu da wannan tsohon ba da baki rabu dashi ba. Ke kan ki da zaki d'au wanka ki fara shafa mayuka masu gyare jiki kina hawa leses masu tsada da atampofi, wallahi da wani mayen mai kud'i zai yi wuff dake kema kije kici arziki ki bar arziki inda yake. Don wallahi ba wani tsufa kika yi ba, kawai wahalar wannan tsohon ne ya mai da ki haka." Ta k'arisa maganar tana hararen mahaifin nata. Shi kuwa wani irin kukan bak'in ciki ya fashe dashi tare da dogara sandar shi ya juya ya koma d'akinsa wanda ba k'aramin abu yake fitowa dashi ba, ko alwala da sallah a ciki yake yi. Yana da bahon da yake alwala a ciki, sannan kuma akwai wani bokitin penti k'arami da yake yin fitsari ko ba haya a ciki wanda Sarah ce ke d'awainiyar fitar dasu tana zubar da abunda yake ciki tare da wankewa sannan ta dawo masa dashi ta ajiye. Da sauri Sarah tabi bayansa ita ma tana kukan tana kuma bashi hak'uri. Lami kuma harara ta bisu dashi tare da fad'in, "Munafukan banza da wofi! Kin ga yarinyar nan, wallahi za'a iya had'a baki da ita a kashe mu. Kuma zan yi maganin ta." Tana gama fad'in haka taji an banko gidan da k'arfi an shigo da gudu tare da afkawa d'akin ta. Da idanu duk suka bishi a tsorace, dai-dai lokacin da wani matashi shima ya fad'o gidan ya tsaya tsakar gida hannunsa rik'e da k'atuwar adda yana huci. Gaba d'aya su Na'ima suka koma bayan Lami a tsorace. Shi ko matashin ya k'ariso har inda suke fuska babu rahama tare da karta addan a k'asa yace, "Na rantse da ubangijin Yunusa da Musa, idan ba'a fiddo min da wayar k'anwata da d'an ki ya kwata yanzu ba, duk sai na sassare ku a cikin gidan nan. Ni dashi kar ta san kar billahil lazi. Dalla malama ware ki amso min waya a hannun kafurin d'an ki ko kuma yanzu lahira tayi bak'o." Ya k'arisa maganar yana zarowa Lami idanu. Jikin Lami da y'ay'anta gaba d'aya babu inda bai rawa saboda kaf cikin gari babu wanda bai san *Naliliyo* ba. D'an daba ne sosai wanda kisan mutum a wajensa kamar take kiyashi ne. Da sauri Lami ta juya zata shiga d'akinta domin karb'o wayar, sauran y'ay'an zasu rufa mata baya ya daka masu wata uwar tsawa tare da fad'in, "Duk wata kafurar da ta motsa a cikin ku sai na kashe a
Chapter 3 · 0% Book details