Sashe 68
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read
babban murya kar ku sake ku tadawa marmari daga nesa hankali, tunda dai Allah ya ban lafiya ba sai yaji ba, ku bar shi yayi aikinsa hankali kwance, Ko Musaddiq (Barrister Muhammad Kabir) bance a faɗa masa ba." Da sauri Khalil yace, "To amma Hajiya....." "Nace bana son su sani idan har na isa! Sannan kuma maza ka amsar min takardar Sallama mu tafi gida, kuma ina so mu biya ta gidan surukanka zan roƙi alfarmar a bani wannan ƙanwar tata ta zauna damu na wasu lokaci?" Faɗin Hajiya. Da mamaki Khalil yace, "Hajiya, ba dai Aina'u ba ko?" A gadarance Hajiya tace, "Ita fa! Ko baza ka kai ni bane?" "Zan kai ki." Faɗin Khalil tare da ficewa daga ɗakin ya koma office ɗinsa, wayarsa ya fara ɗauka tare da sakawa aljihu ba tare da ya duba ba, gaba ɗaya hankalinsa ya koma gida, so kawai yake yi ya gansa kusa da Sarah don itama dole ya kawota asibiti ya duba abunsa. "Ni da kaina zan duba matata babu wani ɗan iskan da zai gane min jikin mata." Ya faɗi a bayyane tare da fitowa daga office ɗin. Kiciɓis suka yi da ya Abdul-Hakeem, "Yanzu dama wajenka zani, mummyn Moon ta kira ni tana kuka sosai wai Sarah babu lafiya tana ta aman tsuts........." Ba tare da Khalil ya gama sauraron ya Abdul-Hakeem ɗin ba ya nufi hanyar waje da bugun sauri, parking lot ya nufa tare da shiga motar yayi reverse ya bar asibitin a guje. "Ina Khalilullah ɗin? Yazo mu wuce mana!" Faɗin Hajiya wacce ke kallon yaya Abdul-Hakeem. "Hajiya akwai matsala ya wuce gida, matarsa ce babu lafiya, Maryam tace aman wasu jajayan mitsi-mitsin tsutsotsin take yi, abun dai babu daɗin ji." "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wannan wani annobace ya shigo cikin zuri'a ta? Allah gamu gare ka! Laure babu baki, ni da maƙoƙo da zazzagowar idanu, surukata kuma da aman tsutsotsi. Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Allah mun tuba." Faɗin hajiya tana mai fashewa da kuka. "Hajiya kiyi haƙuri ki bar kuka, in Sha Allah, zasu samu sauƙi, ku taso mu tafi gida, to amma wa zai kwana da Laure tunda ba'a bata sallama ba?" Share hawaye Hajiya tayi tare da faɗin, "Tare da ita zamu tafi tunda itama bayan rashin maganar babu abunda ke damunta, kuma ba gida muka yi ba kai tsaye, zamu fara biyawa ta gidansu Uwata domin taho da ƙanwarta ta ɗan zauna damu kaga ni ba ishashshen lafiya ba, Laure kuma babu baki, dole ina neman mai taimako." "Kuma Hajiya sai a rasa wacce za'a ɗauko domin taimakon ki sai ƙanwar matar Khalil, a'a gaskiya Hajiya, don ni haka nan yarinyar bata kwanta min a rai ba." Faɗin yaya Abdul-Hakeem. "To ni ta kwanta min, kuma dole ka kaini gidan na taho da ita." Faɗin Hajiya tana hararensa. Bai kuma cewa komai ba ya juya ya ɗauki akwatin kayan haihuwar Nafeesa ya fita dashi, ita kuma Nafeesa ta rungumo babynta Hajiya a bayanta suka fito. Can gidan su Sarah kuwa, Aina'u ta gama shirinta tsaf don tana ganin komai ta tsakiyar tafin hannunta. Suna parking a ƙofar gidansu ta saki wani murmushi tare da faɗin, "This is the end of you Saratouh Nuhu!" Fitowa kawai Aina'u tayi da akwati a hannu ta fito waje, kallonta Abdul-Hakeem yayi ta yi yana mamakin dama ta san da zuwansu ne ganin ba tare da an shiga da sun shiga ciki ba, kuma basu tura kowa ba har ta fito. Da kanta ta buɗe boat ta saka kayanta a ciki tare da rufewa ta zagayo ta buɗe gidan baya ta shiga tare da rufe motar tana faɗin, "Hajiya ina wuni, ya kuma ƙarfin jikin?" Ita kanta Hajiyar ba ƙaramin mamaki tayi ba jin furucin Aina'u, "Ya akai tasan bani da lafiya?" Faɗin Hajiya cikin zuciya. Amma a fili sai cewa tayi, "Jiki Alhamdulillah Aina'u." Kallon jaririyar hannun Nafeesa tayi tare da faɗin, "An samu ƙaruwa? To Allah ya raya." Ba tare da tunanin komai ba Nafeesa ta miƙa mata jariyar, hannu biyu Aina'u ta amshi jinjirar tana mai faɗin, "kyakkyawa da ita!" Daidai nan yarinyar ta tsandara wani mahaukacin ihuu sai da ya Abdul-Hakeem dake driving ya juyo da sauri yana faɗin, "Lafiya?" Babu wanda ya bashi amsa sai miƙa hannu da Nafeesa tayi tare da amsar jinjirar, sai kuma tsit kamar an ɗauke ruwan sama. Aina'u kuwa wani murmushi tayi ganin kurwar ƴar na yawo a saman motar, can kuma sai ga fuskan *_Hell Ofulafula_* ya wani irin zaro harshe tare da lashe kurwar jinjiran yana mai jinjiwa Aina'un sannan fuskar tasa wanda Aina'u kaɗai ke gani ya ɓace. Khalil kuwa yana parking da gudu ya nufi side ɗinsu yana tsatstsallake step uku-uku har ya isa ƙofar ɗakin Sarah, cikinsa ne ya bada wani irin saurin kuuuuuuuuu tsabar wani dunƙulallan wari da ya shaƙa, amma stil haka ya tura ƙofar ya faɗa ɗakin. Tsalle ɗaya yayi ya isa inda take tare da rungumota gaba ɗaya a jikinsa.............