← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 112

Sashe 101

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya na gama faɗin haka ta miƙe ta fita fuuu tana sharar hawaye. Khalil kuwa mutuwar tsaye yayi a wajen yana jin wani irin matsanaicin bugun zuciya kamar zata faso ƙirjinsa ta fito, Abdul-Hakeem kallonsa yayi tare da ɗaga hannunsa yana shafa ƙirjinsa alamar he should calm down sannan ya fita ya bi bayan Hajiya. Aunty Maryam ƙarisowa tayi kusa da Khalil tare da faɗin, "Khalil ka kwantar da hankalinka, in Sha Allah Hajiya zata sauko. Maganar laifi kuma, ba laifin Sarah bane, Sarah bata da laifi akan abinda Aina'u ta aikata, ita kanta Sarah ai Aina'un ta cutar da ita, don wannan tsutsotsin da ta riƙa fitarwa warin nan ai babbar cutarwa ce! In Sha Allah hajiya zata sauko, don tabbas babu laifin Sarah a cikin abinda Aina'u ta aikata, kuma wallahi ko da ba Sarah ka aura ba, Aina'u sai ta shigo cikin gidan nan ta wata hanya daban ta cutar damu don hakan rubutacce ne a cikin ƙaddarar mu, kuma muma duk muna da namu laifin na sake da muka yi da Allah muka kama jin daɗin duniya, mun manta da azkar da karatun Alƙur'ani wanda Alai ya gina a cikin gidan nan, mun ɗauka kawai salloli biyar da azumin watan Ramadan ɗin da muka riƙe kawai sune dolen mu. Wannan izinace a gare mu dukanmu. Amma tabbas Sarah bata da laifin komai, kuma ina ji a jikina zata sauko nan kusa, yanzu dai shawarar da zan baka itace, tunda har Hajiya tayi fushi haka har ta furta waɗannan kalamai, ka kyaleta na wasu lokaci, kar ka kuskura ka tunkareta da maganar, ka bari har ta huce tukun." Gyaɗa kai Khalil yayi tare da faɗin, "Shikenan, Nagode Aunty Maryam!" Yana faɗin haka ya fita ya bar ɗakin, side ɗin Hajiya ya koma ya nufi ainahin ɗakinsa dake sashen, buɗe Ƙofar yayi ya shiga ciki, ɗakin nan kamar yanda yake, bayi ya nufa ya dunga cuɗa kansa kamar zai yage fatar dake jikinsa saboda tuna ya haɗa jiki da Aina'u. Ya jima kamun ya fito daga wanka, wajen mirror ya nufa yana ƙarewa kansa kallo ganin yanda ya koma kamar mahaukaci, gashin kansa yayi buzu-buzu babu gyara. Hawaye zafafa yaji suna biyo ƙirjinsa sakamakon tuno duk abubuwan da yayiwa Sarah, "Hajiya ki taimakeni kar ki raba ni da uwar ƴaƴata!" Ya faɗi yana mai zama a kan kujerar dake gaban mirror ɗin tare da ɗaura kai a kan drawer. Ya jima a haka kamun ya tashi ya saka don ko shafa mai bai yi ba. Fitowa yayi daga ɗakin, kiciɓis suka yi da Laure a ƙofar ɗakinsa, kanta a ƙasa don kuka take yi tace, "Ya kalif kaje inji Hajiya!" Ba tare da yace komai ba ya gittata ya wuce. Ɗakin hajiyan ya nufa, sai da ya Kwankwasa sannan ya shiga ciki, zaune ya same tana waya kamar zata taune harshe don masifa, "To shikenan sai kazo goben, don wasu abubuwan ma baza su faɗu ba har sai ka iso, ku taho kai da Ayshan." Faɗin Hajiya. Tun da tace ku taho kai da Ayshan, Khalil ya fahimci da Ya Abdullahi take magana. Ajiye wayar tayi tare da kallonsa tace, "Khalilullah, ka dai ji abunda na faɗa maka ko? Tom! Yanzu abunda nake so da kai, kayi maza ka tashi ka tafi gidansu yarinyar nan ka taho min da jikokina, sannan ka tabbatar kamun ka dawo cikin gidan nan ka tsinke igiyar dake tsakaninka da ita, sannan gobe in Sha Allah idan Marmari daga nesa ya iso yaga wannan la'ananniyar yarinyar data tarwatsamin gida, zaka nemo akori kura a kwasheta a kai ta gidan iyayenta can susan yanda za suyi da ita, mu baza mu yafe mata ba, amma kuma baza muyi mata komai ba domin Allah ya riga ya soma nuna mata iyakarta tun a nan gidan duniya! Sauran kuma sai mun je can. Don haka ka tashi maza ka bar gidan nan kayi abunda na umarce ka da kayi." Ta ƙarisa maganar tana mai nuna masa hanya. Ya kwashi kusan mintuna biyu jikinsa na rawa kamun ya miƙe ya fita daga ɗakin. Kai tsaye parking lot ya nufa ya buɗe mota ya shiga yayi reverse ya bar gidan, a hanya babu abunda yake yi sai goge zufa kuma a lokaci guda gabansa na wani irin bugawa da ƙarfin tsiya, kuma hakan ƙara faruwa ne idan ya ƙara kusa da unguwarsu Sarah. A ƙofar gidan yayi parking sannan ya fito daga cikin motar, glasses ɗinsa ya fiddo ya saka saboda yanda idanunsa suka yi jazur. Kallon layin ya riƙa yi, domin tunda ya saya masu gidan zai iya irga zuwansa unguwar. Gaban gate ɗin gidan ya tsaya tare da kai hannu ya Kwankwasa gidan sau uku, jin alamar ana cire jamlock sai ya ɗan matsa baya kaɗan yana jiran a buɗe Ƙofar. Murmushi ta sakar masa tare da faɗin, "Ah Khalil kai ne a gidan namu yau? Wallahi yanzu muka gama magana da mama (Lami, kasancewar malamar mu ta hana su kiran sunanta kai tsaye. Tace masu hakan rashin tarbiyya ne da nuna rashin ɗa'a ga mahaifiya )" Faɗin Na'ima wacce gaba ɗaya ta rame kamar ba Na'ima ƴar gayu ba. Murmushin kawai ya iya mata, "Shigo mana ka tsaya a tsaye." Ta faɗi tare da matsa masa, shigowa yayi yana mai ƙara gyara zaman glasses ɗin fuskansa, a tsakar gidan ya taras da Lami da sauraran ƴaƴanta, sai dai yaji gidan tsit ba kamar yanda ya saba jin hayaniyar yaransu ba aduk sanda ya leƙo, kasancewar yana zuwa masu da abun motsa baki, suna jin muryansa ko da basu tsakar gidan suke fitowa da gudu suna masa oyoyo. Har ƙasa Khalil ya tsuguna tare da faɗin, "Mama ina wuni, na same ku lafiya?" Sai da Lami ta ƙura masa idanu na kusan tsayin mintuna biyu kamun tace, "Lafiya Khalil? Shin kayi dogon jinya ne? Amma Saratu bata kyauta ba da bata zo ta faɗa ba, ashe shiyasa kenan babu ganta wajen zaman makoki ba!" Faɗin Lami cikin jimami. Gaban Khalil ne ya buga da wani irin ƙarfi jin abunda Lami tace, amma kuma sai yayi saurin kawar da hakan cikin ransa tare da furta, "Mama wanene ya mutu har akai zaman makoki bamu sani ba?" Nuna su Na'ima tayi tare da faɗin, "Gaba ƴaƴansu ne suka mutu sakamakon saran maciji!" Na'ima har idanunta sun cicciko da hawaye sakamakon tado mata da mikin da Lami tayi. Khalil kuma sai yanzu ya tuna abunda Aina'u tace lokacin da take confessing, cewar ta tura maciji ya sari duka ƴaƴan gidan ta bawa bokanta jininsu. "Wannan yarinyar tsinanniya ce ta ƙarshe!" Faɗin Khalil cikin zuciya. Shuru yayi na wasu lokaci kamun yace, "Mama idan babu damuwa ina son magana da dukkan ku dan Allah, amma kamun nan bari na duba Baba tukun." Jinjina kai Lami tayi, yayin da shikuma ya miƙe ya nufi ɗakin baba wanda har yau yana nan kwance kamar gawa. Sallama yayi tare da saka hannu ya cire takalmin ƙafarsa sau ciki sannan ya shiga, baba na nan kwance a kan gadon, Sai dai cikin tsafta yake don ba ƙaramin ƙoƙari su Na'ima suke yi ba wajen kula da tsaftar baban kasancewar anan yake bowali da bahaya! Har gaban gadon Khalil ya jawo kujera tare da zama sannan ya kamo hannun baba dake bacci tare da soma faɗin, "Baba kayi haƙuri duk da nasan cewar kalmar ciwo zata ƙara saka maka cikin zuciya! Tabbas ko da ban san ainahin ciwon da kake ji ba matsayin ka na uba, amma zan iya ɗan kwatanta ko da kaɗan ne. Kayi haƙuri, shine kawai abunda zan iya ce maka. Sannan in Sha Allah baba bazan taɓa bari rayuwar Sarah dana sauran ƴaƴanka ya taɓarɓare ba kamar na Aina'u, nayi maka wannan alƙawarin, zan tsaya tsayin daka a kansu, Ni ba sirikinka bane kawai, Ni ɗane a wajenka kuma yayyinsu Na'ima. Kai kuma Baba in Sha Allah zaka warke kuma ka cigaba da harkokinka kamar da. Kayi haƙuri baba!" Abunda ya matuƙar bawa Khalil mamaki jin Baba ya ɗamki hannunsa ya riƙe gam-gam kuma a lokaci guda hawaye na zirarowa daga kwarmin idanunsa har suna shiga kunnensa. Khalil ɗaura ɗayen hannunsa yayi a kan na Baba tare da riƙe hannun da ƙarfi yana kallon fuskan baban dake a rufe kuma yana zubar da hawaye. "Kayi haƙuri baba, in Sha Allah zaka samu cikakken lafiya." Baba magana yake so yayi, amma babu damar haka, a zuciyarsa kuwa cewa yake, "Dan girman Allah Ibrahim kar ka nema min lafiya, ka barni a haka, ni fatana ɗaya in koma ga Allah cikin gaggawa kuma tare da imani, don baƙin cikin dake cin zuciyata ni kaɗai na san shi. Dan Allah Khalil ka barni a haka." Da kyar Khalil ya iya zame hannun Baba a cikin nashi sannan ya fita daga ɗakin, dama kuma Na'ima na jiransa domin tayi masa jagora zuwa parlourn Lami, yana fitowa tayi gaba, shi kuma ya bita a baya har cikin ɗakin Lamin. Be zauna a kan kujera ba, a ƙasa ya zauna tare da zare glasses ɗin dake maƙale a idanunsa ya ajiye a gefe yana kallon mutanan dake ɗakin cikin dabara, amma har ya gama kallosu bai hango fuskan annurin zuciyar tasa ba a cikinsu. Kai a sunkuye ya kuma gaida Lami a karo na biyu tare da yi mata ta'aziyar jikokinta ƴan gaba da fatiha sannan ya ɗaura da faɗin, "Haƙiƙa na taho maku da labari mai girgizarwa da tashin hankali gami da baƙin ciki!" Yana kaiwa nan ya ɗan dakata na wasu daƙiƙu, yayin da Na'ima ta shiga nanata "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Kasancewar malamar su ta faɗa masu duk ɗayansu da ya faɗa cikin wata masifa to ya karantata. Lami kuwa da ƙarfi ta faɗi, "Yesu Almasihu mai ceto, ka kawo ɗauki da sassauci, ka sanyaya zuciyarmu da ruwa mai tsarki." Khalil kuwa bayan dogon ajiyar zuciya sai ya soma basu labari tiryan-tiryan, bai rage komai a cikin abubuwan da Aina'u ta aikata ba, har kwanciyar aure da yayi da ita sai da ya faɗa masu, kashe-kashen da tayi har zuwa koran da ta saka yayi wa Sarah da kuma halin da Aina'un take ciki yanzu na girban abubuwan data shuka. Kif! Lami ta faɗo daga kan kujera ta sume, yayin da su Na'ima
Chapter 101 · 0% Book details