Sashe 92
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 2 min read
Aina'u!" Sarah ta faɗi da ƙarfi. Wani shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da faɗin, "To ai shi kansa mijin da umarnina yake amfani. Ko baki san ni nace ya kore ki ba?" Sarah bata bata amsa ba ta cigaba da yiwa Khalil magiya. Tureta Khalil yayi tare da faɗin, "Please Sarah, don't make things worse, just do as I said." Yana gama faɗin haka ya tashi ya fita. Aina'u sai da tayi mata gwalo sannan ta fice daga ɗakin, "Sarah ki tashi kawai ki tafi kar ƴar iskan nan ta saka Khalil ya yanke igiyoyin aurenki dake kansa." Wata zuciyar ta faɗa mata haka. Da sauri ta tattare kayan ta zuba a akwati ta zuge zip tare da saka hijjab sannan ta jawo akwatin zuwa parlour ta ɗauki Sam'an ta riƙe Sauban kuma ta goya shi, sai da ta ƙarewa parlourn kallo sannan ta murɗa handle ta fita tana kuka, tana zuwan wajen gate, kamar ance ta juyo, sai ta ganshi a bayanta yana hawaye, buɗe hannunta yayi tare da saka mata Atm card ɗinsa tare da faɗin, "Current account, date of birth ɗinki ne pin ɗin. Ki kular min da kanki da yaranmu." Caraf Sarah ta rike hannun tana kuka tana girgiza masa kai, shima hawayen yake yi tare da ƙoƙarin kwatar hannunsa, da kyar ya zame hannun tare da yiwa Sam'an kiss a goshi yace, "I'm going to miss you son, ku tayani neman gafarar mummynku." Yana gama faɗin haka ya juya da sauri. Kuka sosai Sarah tayi ta rusawa kamun ta juya tare da jan akwatin suka fice daga gidan..........