← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 112

Sashe 24

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya isa k'ofar gidan sannan ya d'auko wayarsa dake gefensa ya lalubo number Sarah da yayi saving da *_My endless bliss_* yayi dialing, ringing uku ya amsa kiran tare da fad'in, "Hello, Assalamu alaikum." Tab'e baki yayi kamar tana kallonsa tare da amsawa da, "Hi, wa'alaikissalam." Da sauri Sarah ta cire wayar daga kunne tana k'arewa special number d'insa kallo wanda ya k'are da 3 guda shidda a k'arshe. Turo baki tayi don sarai ta gane muryansa, gashi kuma tana tsoran yanke kiran don bata manta da deal d'in su na d'azu ba. "Wake magana!" "Bugun zuciyarki!" Kai tsaye ya bata amsa yana mai sakin murmushi. Sarah kuwa yana fad'in hakan zuciyar nata ta soma bugawa. Shuru tayi bata k'ara cewa komai ba. Sun d'au lokaci har na tsawon mintuna biyar babu wanda ya sake yin magana. _Khalil_ ya ciro wayar daga kunne, kamar yanda itama Sarah ta fiddo nata domin ganin is he still their. Sai taga yana reading kamar yanda shima ya gani daga can, mayar da wayar yayi kan kunnansa tare da fad'in, "Tun ba'a je ko ina ba, har kin fara karya dokar ko?" K'ara turo baki Sarah tayi daga can tare da fad'in, "To ni ai kai ne baka yi magana ba, kuma ni ban san mai zan ce ba." Gyara zama yayi cikin motar tare da fad'in, "Ki fito ina waje." Waro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Waje kuma? Ni dai......." Sai kuma tayi shuru bata k'arisa ba. "K'arisa maganarki mana, ke dai baza ki fito ba ko?" Kwanciya tayi rigingine tare da fad'in, "Ni dai Allahna yana sama yana kallo ba haka nayi niyyar cewa ba." D'age gira yayi kamar tana kallonsa tare da fad'in, "Au Allah d'in naki ne ke d'aya mai son kai. To idan ba tsoro ba ki fad'i abunda kika yi niyyar fad'i daga farko mana." Sai da ta juya idanuta sannan tace, "Ni dai so nake in ce maka, ni dai gaskiya.... Gaskiya, ummm-ummm...." Dariya ya saki tare da fad'in, "Kin ga k'aryar ma ta kasa fitowa. To bari na juya kawai kin ga kenan deal d'in mu ya rushe." Waro idanu Sarah tayi tare da mik'ewa da sauri tana fad'in, "Wallahi a'a, wallahi ni dai a'a ba haka nake nufi ba. Gani nan zuwa yanzu." Sosai ya saki dariyarsa tare da fad'in, "Matsoraciya, ana so ana kaiwa kasuwa." "To mai ake so d'in." Ta tambaya tana hararar wayar. " _Khalilullah_ mana." "Khalilo." Ta fad'i cikin zuciya har da Allah ya kiyaye. Bata san cewar a zahiri tayi maganar ba sai da taji yace, "Ni ne _Khalilo_ d'in?" "Na shiga uku na!" Ta fad'i jin ashe a bayyane tayi maganar. "Ki fito maman twins kar ki b'ata min lokacina." "Mene? Ni wallahi ba maman Twins bane. D'aya kawai zan haifa maka. Shima don babu yarda zanyi ne. Ai don dai zubar da ciki haramun ne, kuma tamkar kisan kai mutun yayi, da zubarwa zanyi wallahi." Fad'in Sarah. "Don Allah ki gwada! Da na baki tsan-tsan mamaki don kin san Allah sai na kuma yi maki real ciki kin haihu." Kuka Sarah ta saka tare da fad'in, "Kuma ba zan fito d'in ba. Mugu kawai!" "Dan Allah ban rok'eki ba, kar ki fito d'in cikin mintuna biyu rak." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. "Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wannan wani irin jaraba ce haka? Ga duka ga tsinke jaka." Fad'in Sarah tare da share guntun hawayen da suka zubo mata ta nufi wardrobe ta d'auki Vail madaidaici ta yafa a kan riga da skirt d'in jikinta wanda ya amshi k'irar jikinta cif-cif. Babu ko hoda a fuska sai wani d'aure fuska take yi tare da fita waje ba tare da ta kalli y'an uwanta dake tsakar gidan ba. Babu mai shigar arziki a cikinsu. Marfu'a ma shayar da y'arta Fadwa take yi y'ar shekara d'aya da wata biyu. Ko kasheta za ayi baza ta iya nuna uban y'ar ba saboda yawan samarinta. Ga y'ar fara tas kyakkyawa kamar mahaifiyarta. Don duka Y'ay'an Lami kyawawa ne, duk da Lamin ita ma ba laifi tana da kyau, Sai dai ita bak'a ce, hasken Baba suka yo da kamannin fuskansa shiyasa gaba d'aya suke kama da juna sai dai wancen tafi wancen dogon hanci, ko kuma k'irar jiki. Wata kuma dimple gareta, wata kuma wushirya. Masu dimple d'in sune, Sarah, Na'ima da Hassana, masu wushirya kuma, Aina'u, Nuratu da Marfu'a, Lukman ne kawai ya d'auko Lami kaf, kamanni da hasken fata. Sai Aina'u da itama ba fara bace sosai kamar sauran y'an uwanta. Kuma ita tana da d'an jiki irin na mahaifiyarsu. Da kallo suka bi Sarah dukkan su, kuma babu wanda ya tambayeta ina zata je. Tura k'ofar gida tayi tare da fita ta coge a k'ofar gidan tana k'arewa motar da yake ciki kallo ta gefen ido tana mamaki shi motoci har nawa gare shi haka. Shima kuwa ta cikin tinted glass window d'in yake k'are ma halittar jikinta kallo yana mai jin wani irin matsanaicin kishi na taso mata. Domin gyalen dai bai da maraba da babu don babu abunda ya b'oye a jikinta. Ga shape d'inta da ya fito kamar zanata aka yi. Hannu ya kai ya d'auki glasses d'insa ya mak'ala a idanunsa tare da bud'e motar ya fito, luckily sai ga wasu almajirai su biyar zasu wuce, da hannu ya yafito tare da bud'e boat ya nuna masu abunda zasu kwashe su kai gidansu Sarah. Sarah na ganin uban kayan da ake fitowa dasu a cikin boat, back seat da kuma front seat ta bud'e ido tana mamaki don kamar za'a bud'e shago. Sai da aka gama kwashe kayan tsaf ya sallamesu sannan ya nufi wajenta don tuni ta bawa almajiran nan waje ta koma gefe. Fuskan nan b'utu-b'utu ya kalleta tare da zare glasses d'in fuskansa. Lokacin da Sarah ta d'ago ta saka idanunta cikin nasa, sai da gabanta ya fad'i ganin yanda launin idanunsa suka canza, duk lokacin da ta kalli idanunsa a wannan yanayin, tuno mata da ranar da aka samu cikin jikinta yake yi. "Ke har yanzu baki yi hankali ba ko Sarah!" Duk lokacin da ya furta sunanta, sai taji duk duniya babu wanda ya iya kira kamarsa. "To ni kuma mai nayi yanzu?" Ta fad'i tana mai turo baki. Ko kamun yayi wata magana, Lami ta turo k'ofar gidan tare da fad'in, "Sannu-sannu! Sannu da k'ok'ari yaron arziki! Wannan irin uban kaya haka? Kai an gode sosai. Ai irin ku ake so masu hannu a bud'e. Allah yayi maka albarka." Fad'in Lami tana washe baki. Sarah kuwa ji tayi kamar ta kwalla ihu tsabar takaici. Don Lami ta riga ta gama zubar mata da mutunci. Shi kuwa _Khalilullah_ ko kallonta bai yi, sai cewa kawai yayi, "Ameen." Yana kallon fuskan Sarah da ta gama b'ata masa rai. Juyawa Lami tayi ta koma ciki. Sarah kuwa sunkuyar da kai tayi tana jin hawaye na taruwa a idanunta. "Kar ki yarda wannan hawayen su zubo _Mine_, kar ki yarda su zubo don idan suka zubo nayi maki alk'awari sai na lashe su tsaf kuma a titin nan." Da kyar Sarah ta iya maida hawayenta suka koma, don ta san tabbas duk abunda _Khalil_ ya fad'a zai iya yin fiye da haka tun da dai yanzu haka cikinsa ne a jikinta. "Dan Allah kayi hak'uri da halin mahaifiyata." Mai makon yayi sharhi akan maganar da tayi, sai cewa yayi, "Sarah idan kina son zaman lafiya dani, kuma kina gudun abunda zai je ya dawo, to kar in kuma ganinki da irin d'an iskan gyalen nan. Wai ke baki san ba irinku bane suke saka gyale ba? Wallahi yawancin mata ku kuke ja ana yi maku fyad'e. Kin san cewa Allah yayi ku ma Sha Allah ta yanda ba kowani namiji zai iya had'iye miyansa akan ku ba, amma sai ku rik'a fitar da surar jikinku. Wasun ku ma har k'ari suke yi don kawai su burge samarin. To ni wallahi ban so, kuma ban so na sake ganin irin haka. Ki kiyaye ni _Mine_. "Wai wani _Mine_ sabida kinibibi. Ko ta ina na zama na shi oho!" Fad'in Sarah amma a zahiri sai cewa tayi, "Zan kiyaye daga yau in Sha Allah!" Politely ta fad'i maganar. Shi kuma _Khalil_ yace, "That's very good. Allah ya baki iko. Yanzu menene kike buk'ata?" "Turaren jikinka." Ta fad'i a cikin zuciya saboda yanda k'amshin yake fizgarta, don na yau ma yafi mata dad'i akan wanda ya saba sakawa. Amma a zahiri sai cewa tayi, "Babu komai. Ni babu abunda nake buk'ata. Abunda ka kawo yau ma yayi yawa." Harararta yayi tare da fad'in, "To ke na kawo mawa? Ni su Baba da mama da y'an uwanki da kuma babyna dake cikinki na kawo mawa. Akwai chocolate, wannan duka naki ne, au na baby na. D'an kai hannu cikinki ki fad'awa babyna daddynsa na gaishe sa." Ko kallonsa bata yi ba, balle tayi abunda yace, kuma dama shima ya san ba yi za tayi ba. Yana kallonta sosai, bini-bini zata shak'i iska ta lumshe idanu, ya karanci psychology, hakan ya fahimtar dashi abunda Sarah take shak'a. Murmushi yayi tare da fad'in, " _Mine_ akwai abunda kike so amma jik'imarki ta hana ki bud'e baki ki fad'a min ko?" Bud'e idanunta tayi a kansa tare da fad'in, "Ni babu abunda nake so. Kawai zuciyarka ce ta fad'a maka gaibu." Kallonta yayi na second hud'u sannan yace, "Ki rantse da girman Allah turaren jikina baya fizgar hankalinki har yake saka ki lumshe idanu." Mamaki ne ya kashe Sarah ganin ya d'ago jirginta. Sai ta diririce ta rasa mai zata ce sai kawai tayi shuru tana kallon k'asa. Komawa mota yayi, mintuna biyu sai gashi ya dawo da kwalin turaren *_Imperial Majesty_*, bakinsa kuma yana taunar masoyin nasa _Mastika gum_. "Wai kai baka gajiya da cin chewing gum ne?" Fad'in Sarah wacce bata ma san lokacin da tayi masa wannan tambayar ba. "Kin tuna wancen ranar haka kika ce min mai d'abi'u _KARUWAAA_?" Sai da ya,ja waa d'in yana dariya. Rufe fuska da hannunta Sarah tayi tare da fad'in, "To ai kai d'in ne ka cika cin chewing gum." "Shikenan kuma duk mai cin chewing gum ya zama karuwa ko? To ai gashi kin
Chapter 24 · 0% Book details