Sashe 77
Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 4 min read
sai abunda yayi gaba wajen kyaran Khalil, shi kuwa ko afuska bai taɓa nuna ɓarin rai ko ƙosawa da ita ba, sai ma wani irin nunkular kulawa da ya ƙara bata don duk tunaninsa depression ke damunta. Kamar daga sama sai ga Muneeba a gidan Sarah, sosai Khalil yayi murnar ganinta, har bedroom ɗin Sarah ya kaita, kuma a gaban idanun Muneeban ta yiwa Khalil ɗin koran kare, bayan fitarsa Muneeba ta hau Sarah da faɗa kamar ta ari baki, sai kawai Sarah ta fashe da kuka tare da faɗin, "To ni ya zanyi Muneeba, ina zan saka kaina! Ciwo duk yabi ya dame ni, tsutsotsi a gabana, wari da ƙarni gami da hamami a ɗakina. Mijina kuma duk lokacin da ya kusanto ni, wani irin ƙarni da hamami yake min!" Da idanu kawai Muneeba take bin Sarah, can kuma sai tace, "Sarah! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Wani irin abu nake ji haka? Shin baba da Lami sun san wannan zancen kuwa? Ai wannan ba cutar da za ayi shuru da baki bane, dole iyaye suji don cutarki bai yi kala da cutar asibiti ba. Bari ki gani ina zuwa.." Tana gama faɗin haka ta mike tare da ɗaukar jakarta domin zuwa gida ta faɗawa mahaifiyarta abunda ake ciki domin tayiwa babanta magana ayi mata treatment na Islamic. Sai dai miƙewarta yayi dai-dai da miƙewar Aina'u da sauri tare da fitowa ta tsaya bakin gate, Muneeba na fito ta soma tafiya da sauri, sai kawai ji tayi an juyo da ita da auri tare da taɓa goshinta, "Ki kalli gabas kiyi ta tafiya kar ki ƙara waiwayar nan gidan!" Gyaɗa kai Muneeba tayi tare da kallon gabas ta hau tafiya ba tare da sanin inda ta nufa ba. Wani irin dariya Aina'u ta sheƙe dashi tare da faɗin, "Babu mai ja dani ya zauna lafiya, Khalil nawa ne ni ɗaya, don ni aka halicce shi, duk wacce tayi ƙoƙarin rabani dashi sai na ɗanɗana mata azaba, haka duk wacce tayi ƙoƙarin ceton Sarah sai na wulaƙanta rayuwarta!" Tana gama faɗin haka ta juyo ta dawo cikin gida. Cikin Sarah ya shiga na wata bakwai, still babu abunda ya canza, haka kuma Khalil shima bai taɓa canza mata ba. Aina'u ta kai maƙurar ɓacin rai ganin babu wani canji daga Khalil, sai kawai ta hau shirin tafiya Abia domin samun _Hell Ofulafu_ gaba da gaba domin tayi mai kankat.. Ranar wata asabar ta tafi, wannan karan ma Ugo ne yayi mata jagora bayan sun gama watsewarsu. Ba ƙaramin tsafi Hell yayi mata ba wannan karan, sannan sai da tayi masa alƙawarin jinin mutane goma, biyar jarirai, biyar kuma waɗanda suka soma tadawa ƴan shekaru uku zuwa goma. Sannan ya bata wani kwaɗo ƙarami yace ta haɗiye, idan har ta haɗiye duk wanda ta kalla tace yayi wani abu babu musu sai yayi, sannan kuma idan har tana son asirin da za ayiwa Khalil ya kama shi, sai ta kwanta da mahaifinta. "Idan har buƙatata zata biya ko Sarkin maka kace na kwanta dashi zan kwanta dashi." Shine abunda Aina'u tace. Kwananta uku a Abia ta juyo ta dawo Kaduna, bata sauka a ko ina ba sai gida lokacin ƙarfe biyu na dare. Banƙare ƙofar gidan tayi sannan ta shiga, ɗakin baba ta nufa kai tsaye tare da tura ƙofar ta shiga don shi bai saka sakata a ɗaki. A Zaune ta samu baban don tun lokacin da ta tura ƙofar gida ya farka, hannu ta kai ta kunna switch ɗin ɗakin tare da yin wani irin tsayuwan karuwai tana mitsi-mitsin da idanu, shi kuwa baba sai yaga gama ɗaya suffarta ta koma ta Lami sak lokacin da take amarya. Wani irin mugun sha'awa ce ta shiga fuzgar baba har bai san lokacin da ya miƙa mata hannu tare da faɗin, " _Elizabeth_" ba. Aina'u kuwa wani murmushi ta saki tare da kashe wutan ta nufe shi gadan-gadan. Cike da rashin imani Aina'u ta bari mahaifin da yayi sanadin kawota duniya ya kusanceta. Sai bayan komai ya nutsa baba ya sauko daga kan gadon a gigice ya kunna wuta, arba yayi da fuskar ƴarsa kuma autarsu tana saka brezia, hannu ya kai ya dafe saitin ƙirjinsa tare da soma nunata da hannu yana son yin magana amma bakinsa ya karkace. Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa rabin jikinsa gaba ɗaya ya mutu. Aina'u kuwa tana gama saka kaya ta tsallakesa ta bar ɗakin ta koma ɗakinsu. Da sassafe kamun kowa ya tashi ta bar gidan ta nufi gidansu Khalil. Sarah kuwa tun asuba ta soma jin wani irin mahaukacin ciwon mara wanda bai misaltuwa don naƙuda ta soma yi gadan-gadan duk da kuwa lokacin haihuwarta bai yi ba don cikin watansa bakwai, itace har safiya tana abu ɗaya, idan ta kai hannu gabanta tana jin gashi, amma haihuwa taƙi zuwa sai nuƙurƙusan azaba take yi. Aina'u na fitowa daga gida ta shafa tafin hannunta sai ga Sarah ta bayyana cikin halin naƙuda. Wani irin nishine ya taho mata, cikin sauri Aina'u ta haɗe yatsanta biyu ta kame gam, sai Sarah taji kamar an saka igiya an shaƙe wuyarta ga kuma kan ɗa daya soma turowa............