← Book details Kanwar Matata Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 112

Sashe 41

Kanwar Matata Complete Hausa Novel · about 2 min read

kayan da zasu kawo ba. Y'an kawo akwati sun mik'e zasu wuce kenan sai ga tawagar matan zumunta sun shigo gidan da wani irin mahaukacin gud'a suna tafi tare da yin wak'ok'in coci. Gaba d'aya sai kallo ya koma sama. "Elizabeth kina ina? Ashe aurar da yarinyarki za kiyi amma shine baza ki gayyaci mutanan coch ba. Baki kyauta ba sam. Pasto William yayi fushi dake kuma yace idan baki kai Sera (Sarah) ya saka mata albarka ba, auren ba zai yi albarka ba. Yace ya baki kwana biyu ki kaita ayi mata wankan zunubi kamun ta shiga gidan miji. Da k'arfi aunty Rose Merry take maganar duk da kuwa bata ga Lami a tsakar gidan ba. Aunty Maryam da aunty Khairat da kanwar Hajiya, sai wannan ta kalli wancen, sai wancen ta kalli wannan. Da suka ga abun ba na k'arewa bane, sai suka yi salama suka tafi domin sosai dai aunty Rose Merry da tawagarta suka baje suna wak'ok'in suna kiran sunan yesu almasihu. Idan suka buga wani ihu har hanjin mutum sai ya kad'a. Baba dake d'aki kuka kawai ya fashe dashi. Don bai tab'a kawowa Lami zata iya yin wannan iskancin ba. Lami dake d'aki ita ma mamaki ne ya kamata don ko da wasa bata tab'a fad'awa mutanen coch d'insu zata aurar da y'a ba. Ko aunty Rose Merry da take k'awarta bata fad'a mata ba. "Na'ima wallahi bani na gayyace su ba, kuma ban san wanda ya kira su ba." Na'ima kuwa kallon mahaifiyarta take yi cike da tuhuma tare da fad'in, "Lami dama kina zuwa coch? Wa za ayiwa wankan zunubin?" Lami bata ba ta amsa ba, sai wucewa da tayi ta bud'e k'ofar ta fita ta samu ce aunty Rose Merry dake ta kwasar ihu da kiran yesu suna d'ad'd'aga kayan akwatin Sarah. "Hajiya kina bacci ne aka kwaso maki dangin arna matsayin surukarki?"
Chapter 41 · 0% Book details